29
Mar
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, wato Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa, Nijeriya ba ta da hannu kai tsaye a rikicin Gabas ta Tsakiya, amma duk da haka za ta fuskanci tasirinsa sakamakon yadda tattalin arzikin duniya ya dunƙule wuri guda, don haka hana tashin farashin mai ya fi ƙarfin hamshaƙimin attajirin. Dangote ya yi wannan bayani ne bayan wata ziyara ta girmamawa da kuma gaisuwar Sallah ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Legas a ranar Litinin, 23 ga Maris, 2026. A cewarsa, duniya ta zama tamkar ƙauye ɗaya, don haka duk wani tashin hankali…
