ukarofi

12594 Posts
Peter Obi ya sha alwashin farfaɗo da masana’antu da ‘Bankin raya Arewa’ a Kano

Peter Obi ya sha alwashin farfaɗo da masana’antu da ‘Bankin raya Arewa’ a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a shekarar 2023, ya yi alƙawarin farfaɗo da masana’antun da ke Kano da dawo da bankin Arewa da aka fi sani da ‘Bank of the North’. Obi ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Lahadi a lokacin da ya kai ziyara gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, a wani bikin sallah da Kwankwaso ya shirya wanda ya samu halartar ɗaruruwan mutane. Obi ya halarci taron ne tare da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson. A yayin da yake…
Read More
2027: Komai tsananin adawa Tinubu sai ya sake lashe zaɓe – Uzodimma

2027: Komai tsananin adawa Tinubu sai ya sake lashe zaɓe – Uzodimma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, zai sake lashe zaɓen 2027 duk da ƙalubalen adawa. Uzodimma ya faɗi haka ne a taron yankin Kudu maso Kudu na ƙungiyar masu goyon bayan shirin “Renewed Hope” da aka gudanar a Asaba, inda ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke yi sun fara gyara tattalin arzikin ƙasa, duk da cewa jama’a na fuskantar wasu ƙalubale a halin yanzu. Ya jaddada cewa wahalhalun da ake fuskanta na ɗan lokaci ne, yana mai kira ga mambobin ƙungiyar da su wayar da…
Read More
Dokar Zaɓe ta 2026 na iya kawo cikas ga zaɓen 2027 — IPAC

Dokar Zaɓe ta 2026 na iya kawo cikas ga zaɓen 2027 — IPAC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Jam’iyyun Siyasa ta ƙasa, wato Inter-Party Adɓisory Council (IPAC), ta bayyana damuwa mai tsanani kan wasu matsaloli da ke cikin Dokar Zaɓe ta shekarar 2026, inda ta ce idan ba a gyara su cikin gaggawa ba, za su iya kawo cikas ga sahihanci da ingancin zaɓen shekarar 2027. Shugaban ƙungiyar, Dakta Mamman Yusuf Dantalle, ya bayyana hakan ne yayin wani zama da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), inda aka tattauna kan dokoki da ƙa’idojin gudanar da jam’iyyun siyasa. Ya jaddada cewa IPAC na da alhakin jan hankalin cikin gida da na ƙasashen…
Read More
Rashin tsaro barazana ce ga tattalin arzikin Arewa — NYEEF

Rashin tsaro barazana ce ga tattalin arzikin Arewa — NYEEF

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar ƙarfafa Matasan Arewa da Wayar Musu da Kai, wato Northern Youth Empowerment & Enlightenment Forum (NYEEF), ta fitar da wata muhimmiyar sanarwar manufofi bayan kammala Taron Tattaunawa na Shekara karo na uku da ta gudanar a watan Janairun 2026 a jihar Kaduna. Taron, wanda aka shirya domin karrama marigayi Alhaji Suleiman Abubakar Uban Doman Gudu, tsohon Daraktan Harkokin Sarauta na ƙungiyar, ya haɗa manyan malamai, shugabannin addini, kwararrun harkokin tsaro, masu tsara manufofi, shugabannin matasa da kuma ‘yan jarida domin nazarin manyan matsalolin da ke addabar Arewacin Nijeriya da ma kasa baki ɗaya. A sanarwar…
Read More
Kungiyar Tsangaya ta naɗa Gwani Ibrahim a matsayin shugabanta na ƙasa

Kungiyar Tsangaya ta naɗa Gwani Ibrahim a matsayin shugabanta na ƙasa

Daga WAKILINMU Kungiyar Tsangaya da ke fafutukar samar da ci gaba ga malaman tsangaya da almajirai a faɗin Nijeriy, ta naɗa Gwani Ibrahim Mai Bindiga Hadejia a matsayin sabon Shugabanta na ƙasa. An gudanar da bikin naɗin ne a yau Talata, 27 ga watan Janairu, a dakin taro na Naicon Luɗury Hotel da ke Abuja. Taron ya samu halartar manyan shaihunnai da gwanayen Alƙur’ani mai girma daga sassa daban-daban na ƙasar nan. Mahalarta taron sun bayyana naɗin a matsayin wani babban cigaba ga harkokin kungiyar Tsangaya, suna mai cewa shugabancin Gwani Ibrahim Mai Bindiga zai samar wa almajirai dama da…
Read More
Kungiyar KAPAG ta ziyarci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni

Kungiyar KAPAG ta ziyarci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kungiyar KAPAG ƙarƙashin jagorancin Hajiya Balaraba Ibrahim ta kai ziyarar girmamawa ga shugaban ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Sekure, a sakatariyar ƙaramar hukumar a ranar Litinin. Hajiya Balaraba ta bayyana cewa dawowar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, jam’iyyar APC wani muhimmin al’amari ne a tarihin siyasar jihar, tana mai cewa siyasa tafiya ce ta haɗin kai duk da sauye-sauyen jam’iyyu da ake samu lokaci zuwa lokaci. Ta ce, a matsayinsu na ƙungiya da ta dade tana aiki tun daga tushe sama da shekaru 25, sun ga dacewar su mara wa duk wanda ya dawo…
Read More
Yadda Dangote ke gina gadon kasuwancin Dala biliyan 100 ta hannun ’ya’yansa mata

Yadda Dangote ke gina gadon kasuwancin Dala biliyan 100 ta hannun ’ya’yansa mata

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar 16 ga Fabrairu, 2026, kamfanin Dangote ya ɗauki wani muhimmin mataki da zai iya sauya fasalin makomar kasuwancin da ya fi girma a Afirka. Wannan mataki, wanda aka tsara cikin shirin ‘Vision 2030’ na kai darajar kamfanin zuwa Dala biliyan 100, ya zarce sauyin tsarin shugabanci kawai, domin yana ɗauke da wani tsari na barin gado mai tarin yawa. A zahiri, wannan sauyi alama ce ta yadda attajirin Afirka, Dangote, ke ƙoƙarin shimfiɗa gadon da zai tabbatar da ɗorewar daular kasuwancinsa bayan zamaninsa. Naɗa ’ya’yansa mata uku a manyan muƙaman zartarwa ya jawo muhawara…
Read More
Tuggar da Pate: Za a gwada ƙwanji tsakanin ministoci Tinubu kan takarar gwamnan Bauchi

Tuggar da Pate: Za a gwada ƙwanji tsakanin ministoci Tinubu kan takarar gwamnan Bauchi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A cikin wani zurfin nazari da shafin News Point Nigeria ya fitar, an bayyana yadda yanayin siyasar Nijeriya ke fuskantar sauyi, sakamakon umarnin da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar ga masu riƙe da muƙaman siyasar gwamnati da ke son tsaya wa takara. Wannan mataki, wanda aka ɗauka ba wai kawai na bin doka ba ne, ya fara sauya tsarin haɗin kai da burin ’yan siyasa, tare da sake fasalta tafiyar siyasar zuwa zaɓen 2027. Umarnin, wanda ya fito ta hannun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin George Akume, ya dace da tanade-tanaden dokar zaɓe…
Read More
Kano ta gaza yayin da jihohi 10 kacal ke fitar da cikakken rahoton kasafin ƙananan hukumomi – BudgIT

Kano ta gaza yayin da jihohi 10 kacal ke fitar da cikakken rahoton kasafin ƙananan hukumomi – BudgIT

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani sabon rahoto da ƙungiyar BudgIT ta fitar ya jefa Jihar Kano cikin zazzafar muhawara a faɗin ƙasa kan batun gaskiya da riƙon amana, bayan ya nuna cewa jihar na wallafa bayanan kasafin kuɗin ƙananan hukumomi ne ba cikakku ba, kuma wasu ma tsofaffi ne. Wannan lamari ya ƙara tayar da hankali kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen jama’a a matakin da ya fi kusa da talakawa. Rahoton mai taken “Matakin da ya ɓace: Tantance Gaskiya da Buɗaɗɗen Kasafin Kuɗin ƙananan Hukumomi a Nijeriya” ya bayyana cewa akwai babban giɓi a tsarin bayyana gaskiya a harkar…
Read More
Shugaban kamfanin Apple ya gargaɗi jama’a kan shagaltuwa da wayoyin hannu

Shugaban kamfanin Apple ya gargaɗi jama’a kan shagaltuwa da wayoyin hannu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Kamfanin Apple, Tim Cook, ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane ke amfani da wayoyin hannu, inda ya jaddada muhimmancin rage yawan kallon allon waya, wato screen, da kuma mayar da hankali kan mu’amala ta zahiri tsakanin jama’a. Cook ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin talabijin na Good Morning America, inda ya yi gargaɗi kan illolin da ke tattare da yawan shagala da wayar hannu. A cewarsa, bai kamata mutane su riƙa kallon wayoyinsu fiye da yadda suke kallon juna ido-da-ido ba, yana mai nuni da cewa mu’amalar…
Read More