ukarofi

12593 Posts
Yaƙin Iran: Da yiwar Turkiyya ko Pakistan ta karɓi baƙuncin tattaunawar tsagaita wuta

Yaƙin Iran: Da yiwar Turkiyya ko Pakistan ta karɓi baƙuncin tattaunawar tsagaita wuta

Wani babban jami’in Iran ya bayyana cewa ƙasar Pakistan ta isar da wata muhimmiyar shawara daga Amurka zuwa Iran, inda ake duba yiwuwar gudanar da tattaunawa a ƙasar Pakistan ko kuma Turkiyya domin rage zafin rikicin da ke ci gaba da addabar yankin Tekun Gulf. Jami’in, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa wannan mataki na daga cikin alamun farko da ke nuna yiwuwar Iran ta fara la’akari da hanyoyin diflomasiyya, duk da cewa a fili gwamnatin Tehran tana ci gaba da musanta cewa akwai wata tattaunawa da ke gudana da Amurka. Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta…
Read More
Ɗaliban Katsina sun lashe gasar I-FEST² da ta gudana a ƙasar Tunisiya

Ɗaliban Katsina sun lashe gasar I-FEST² da ta gudana a ƙasar Tunisiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗaliban sun haɗa da Abdullahi da Sani Matori da Abubakar Abdullahi sai malamin su Yazid Ahmed,sun samu matsayi na biyu a gaba ɗaya inda suka fafata da ɗalibai daga ƙasashen duniya. GwamnanJihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya taya waɗannan haziƙan ɗalibai biyu na Government College Funtua murna bisa gagarumar nasarar da suka samu a Gasar I-FEST² ta ayyukan bincike ta shekarar 2026, wadda Association for the Future of Sciences and Technology ta shirya a ƙasar Tunisiya. Gwamnan ya bayyana farin cikinsa ganin yadda ɗaliban Jihar Katsina ke fafatawa tare da samun nasara a matakin duniya. Ya…
Read More
KASSAROTA ta fara ɗaukar matakai kan toshe hanyoyi a Katsina

KASSAROTA ta fara ɗaukar matakai kan toshe hanyoyi a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar kula da tsaro da harkokin sufuri ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta fara daukar tsauraran matakai kan mutanen da ke zubar da yashi, ƙasa, tsakuwa, kayan gini ko wasu kayayyaki a kan hanyoyi a faɗin Jihar Katsina. Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in hulɗa da Jama’a na hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri, ya fitar a madadin babban shugaban hukumar, Manjo Garba Yahaya Rimi mai ritaya. Sanarwar ta bayyana cewa, yadda ake zubar da irin waɗannan kayayyaki ba tare da tsari ba a kan hanyoyin jama’a, ya zama ɗaya daga cikin manyan…
Read More
Ya hallaka mahaifiyarsa saboda ya ƙi yi masa wanka

Ya hallaka mahaifiyarsa saboda ya ƙi yi masa wanka

Al’ummar ƙauyen Ohatekwe Ukawu da ke ƙaramar Hukumar Onicha a Jihar Ebonyi sun kori wani matashi mai shekaru 20, mai suna Damian Oforbuike, bayan da ake zarginsa da kashe mahaifiyarsa. Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya kai wa mahaifiyarsa, Onyemaechi, hari da adda, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami da alhini. An ce wannan mummunan lamari ya faru ne a ƙarshen mako, inda bayan aikata laifin ya tsere zuwa cikin wani daji da ke kusa da ƙauyen. Sai dai matasan yankin sun haɗa kai, inda suka bi sahunsa har cikin dajin, suka kama shi a wurin da yake ɓoye.…
Read More
Algaita Tv ta kalli halin da Kannywood ke ciki ne ta taimake ta – Darakta Mu’azzam Yari 

Algaita Tv ta kalli halin da Kannywood ke ciki ne ta taimake ta – Darakta Mu’azzam Yari 

Daga MUKHTAR YAKUBU  A daidai lokacin da aka samu sauyin shugabanci a tashar talabijin ta ALGAITA TV wadda take haska finafinan Hausa na masana'antar Kannywood bayan saukar shugaban ta na farko Umar Sani Kofar Mazugal inda aka maye gurbin sa da sabon shugaba Mu'azzam Idi Yari. A yanzu haka an samu wasu canje-canje da kuma ci gaban tashar domin tafiyar da ita daidai da bukatar al'umma. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da sabon shugaban Mu'azzam Idi Yari domin bayyanawa masu karatu inda alkiblar ALGAITA TV ta sa a gaba, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar…
Read More
Jami’ar Dan Fodiyo za ta karɓi baƙuncin taron Tarihi da Waƙoƙin Muhammadu Bawa Dan’anace

Jami’ar Dan Fodiyo za ta karɓi baƙuncin taron Tarihi da Waƙoƙin Muhammadu Bawa Dan’anace

Daga MUHAMMAD HABIB ALHASSAN Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sokoto ta yi shirin gagarumin taron ƙasa kan tarihi da waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace 'Yartsakkuwa, a Waiwayen Shekaru Arba’in masu Tarin Abubuwan Tunawa a Kansu.  Yanzu haka waɗari ke gudana babu kama hannun yaro a shirye-shiryen amsa kiran Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sokoto zuwa wajen gagarumin taron ƙasa a kan Tarihi da Waƙoƙin Muhammadu Bawa ɗan’anace ‘Yartsakkuwa a Waiwayen Shekaru Arba’in Masu Tarin Abubuwan Tunawa a Kansu.  Wata sanarwa daga Malam Adamu Yunusa Ibrahim, Sakataren kwamitin Shirya taron ta nuna…
Read More
Yadda Legas ta mamaye rabon kuɗaɗen tarayya da gagarumin kaso

Yadda Legas ta mamaye rabon kuɗaɗen tarayya da gagarumin kaso

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jihar Legas ta yi fintinkau, inda ta zama a kan gaba cikin jerin jihohin da suka fi karɓar kaso mai tsoka na kuɗaɗen shiga na tarayya da aka raba a watan Janairu 2026, bisa kuɗaɗen da aka tara a watan Disambar 2025. Rahoton da aka fitar ya nuna cewa Legas ta samu jimillar Naira biliyan 55.83, wanda ya kai kashi 7.9 cikin zari na Naira biliyan 706.47 da Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) ya raba wa jihohi 36 na ƙasar. Babban abin da ya ƙara wa Legas wannan kaso shi ne yawan kuɗaɗen harajin ƙarin darajar…
Read More
Tashin farashin mai a duniya yana barazana ga tattalin arzikin Nijeriya

Tashin farashin mai a duniya yana barazana ga tattalin arzikin Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabi a ƙarshen cinikayyar ranar 20 ga Maris, 2026, inda farashin ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 8.22 cikin ɗari zuwa Dala 112 a kowacce ganga a duniya. Wannan lamari ya ƙara tsananta matsin lamba a kasuwar makamashi tare da jefa damuwa kan makomar tattalin arzikin Nijeriya. Rahotanni sun nuna cewa wannan tashin farashi ya kai sama da kashi 53 cikin ɗari cikin watan Maris kaɗai, sannan ya haura kashi 83 cikin ɗari tun farkon shekarar nan. Babban abin da ya haifar da wannan…
Read More
Bankunan Nijeriya 34 sun cika sabbin sharuɗɗan ƙarfafa jari kafin wa’adin CBN

Bankunan Nijeriya 34 sun cika sabbin sharuɗɗan ƙarfafa jari kafin wa’adin CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwanaki kaɗan kafin cikar wa’adin ranar 31 ga Maris, 2026, ɓangaren bankunan Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba bayan da bankuna 34 suka samu nasarar cika sabbin sharuɗɗan ƙarfafa jari da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gindaya. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mafi yawan bankunan ƙasar, musamman manyan bankuna masu lasisin ƙasa da ƙasa da kuma wasu na ƙasa baki ɗaya, sun tsallake ƙalubalen ƙara jari, abin da ke nuna ɗaya daga cikin manyan nasarori a tarihin harkar kuɗi a Nijeriya. Ana sa ran Babban Bankin zai fitar da cikakken rahoto nan ba da…
Read More
Peter Obi ya sha alwashin farfaɗo da masana’antu da ‘Bankin raya Arewa’ a Kano

Peter Obi ya sha alwashin farfaɗo da masana’antu da ‘Bankin raya Arewa’ a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a shekarar 2023, ya yi alƙawarin farfaɗo da masana’antun da ke Kano da dawo da bankin Arewa da aka fi sani da ‘Bank of the North’. Obi ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Lahadi a lokacin da ya kai ziyara gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, a wani bikin sallah da Kwankwaso ya shirya wanda ya samu halartar ɗaruruwan mutane. Obi ya halarci taron ne tare da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson. A yayin da yake…
Read More