31
Mar
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya amince da ɗaukar sabbin malaman makaranta 2,158 domin cike guraben da ake da su a makarantun gwamnati a faɗin jihar. Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta bayyana cewa, daga cikin adadin da za a ɗauka, malamai 1,500 za a tura su makarantun firamare, yayin da 658 za su koyar a makarantun sakandare. Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta harkar ilimi a jihar, musamman wajen rage giɓin adadin malamai da ɗalibai da kuma ƙarfafa ingancin koyarwa a matakin firamare da sakandare. Kwamitin da gwamnati…
