ukarofi

12593 Posts
Sarkin Katsina zai bikin naɗa ɗan Gwamna Raɗɗa da hakimai biyu sarautu

Sarkin Katsina zai bikin naɗa ɗan Gwamna Raɗɗa da hakimai biyu sarautu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya amince da naɗin sabbin hakimai uku a masarautar. Waɗannan mutane uku duk ‘ya’yan asalin zuriyar Sarki Muhammadu Dikko ne, iyali da suka shahara da kyakkyawar al’ada ta nagarta, hidima da jagoranci a Katsina da ma Nijeriya baki ɗaya. A wata takardar buƙatar haka daga Majalisar Masarautar Katsina wacce Alhaji Isah Ali Kankia, Sakataren Majalisar Masarautar ya sanya wa hannu, an aikawa mai bai wa gwamna shawara kan harkokin masarautu. Hakimai uku da za a naɗa sun haɗa da Alhaji Ahmad Abdulmumini Kabir Usman – Hakimin Dankama…
Read More

Duk Ramadan muna tafiya hutun labarai don ibada – Zainab Abdullahi

“Yadda ayyukan marubuta a cikin Ramadan ke kasancewa” Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A kowacce shekara a lokaci irin wannan na Ramadan, al’ummar Musulmi a ko'ina a cikin duniya suna shagaltuwa da ayyukan ibada da neman kusanci da Allah (SWT). Marubuta adabin Hausa su ma sukan jingine ayyukan rubuce-rubuce na nishaɗi da faɗakarwa da suke yi, zuwa ga tilawar Alƙur'ani, da faɗakarwa kan al'amuran addini, da koyar da girke-girke ga mata. A irin wannan lokaci mambobin ƙungiyar marubuta ta Jajirtattu Writers Association suna ware tsawon watan Ramadan don gudanar da shirye-shirye da suka shafi tambayoyin Musulunci da karatun Alƙur'ani. Wannan wani…
Read More
‘Yan wasa bakwai na Katsina Academy sun isa ƙasar Portugal domin shiga gasar “Iber Estoril Lisbon 2026”

‘Yan wasa bakwai na Katsina Academy sun isa ƙasar Portugal domin shiga gasar “Iber Estoril Lisbon 2026”

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina ’Yan wasan ƙwallon ƙafa bakwai daga Kwalejin Ƙwallon Kafa ta Jihar Katsina (Katsina Football Academy) sun bar Najeriya zuwa ƙasar Portugal domin halartar babbar gasar neman ƙwarewa ta IBER Estoril Lisbon 2026. ’Yan wasan da suka tafi sun haɗa da Muhammad Hussain, Mannir Abdullahi, Ibrahim Abdu Haro, Nura S. Nura, Muhammad Muktar Katuka, Isah Usman Ali, da Abubakar Anas. Sun tashi ne daga filin jirgin sama na Murtala Muhammed zuwa birnin Lisbon da fatan samun damar zama ƙwararrun ’yan wasa a ƙasashen waje. Hakan ya biyo bayan haɗin gwiwar da Kwalejin ,ta ƙulla da Moonluck…
Read More
MLGEA ta sa ido kan rarraba magunguna a ƙananan hukumomin Katsina

MLGEA ta sa ido kan rarraba magunguna a ƙananan hukumomin Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da masarautu ta Jihar Katsina (MLGEA) ta gudanar da sa ido kan yadda aka rarraba magungunan da aka samar domin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) a faɗin jihar. An gudanar da wannan aiki ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar, Hon. Bishir Tanimu Dutsinma, tare da mai ba gwamna shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, da sauran manyan jami’an ma’aikatar, domin duba yadda aka miƙa magungunan, hanyoyin rabawa, yanayin ajiyarsu da kuma yadda aka rubuta bayanansu a ƙananan hukumomi. Masu sa ido a yankunan Katsina, Funtua da Daura…
Read More
Daular Borno da asalin Kanuri

Daular Borno da asalin Kanuri

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Da farko dai, Jaridar Manhaja ta yi iya bakin ƙoƙari wajen ganin ta kawo wa mai karatu abin da ya inganta daga abin da za mu rubuta ta hanyar tattaro bayanai daga wurare daban-daban da kuma zurfafa bincike; wato cil-da-cil, ganin Annabin tsohuwa. Muna fatan wannan rubutu ya zama fitilar da za ta haskaka zuciyar masu neman sanin haƙiƙanin tarihin ƙabilar Kanurai. A sha karatu lafiya. Daular Borno dai tsohuwar Daula ce a Afirika da aka kafa tun kafin ƙarni na 10 wacce ta haɗa da yankunan da yanzu ke cikin Nijeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da…
Read More
Tasirin abokai da ƙawaye

Tasirin abokai da ƙawaye

Tare da BILKISU YUSUF ALI Idan aka ambaci kalmar "aboki" ga namiji,  abin da yake fara zuwa a tunanin mutane shine, wani tsayayyen masoyi wanda kanwarku ke jiƙo wuri guda da shi. Wanda kuma bayan so da yake maka, yana sahun gaba na masu burin ci gabanka da kuma son ganin ka zauna lafiy      a, a gida da waje. Kamar haka kuma yake idan ka ambaci "ƙawa" ga mace. Ko wace rawa abokai da ƙawaye suke takawa a cikin zaman aurenmu? A cikin kowane motsi da dukkan harkokin da mutum zai yi, bayan ya zama baligi, za ka…
Read More
Mene ne sakamakon gwaje-gwajen da masana suka yi kan waken soya?

Mene ne sakamakon gwaje-gwajen da masana suka yi kan waken soya?

(Ci gana daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  Sallama dai masu karatu. Muna godiya da bibiyarmu da ku ke yi. Allah Ya amsa addu'o'in mu. Ya sa mun dace da daren Lailatul ƙadar. Barkanmu da Sallah. Allah Ya maimaita. Binciken mako 24: A wani bincike na makonni 24, mata 23 sun sha furotin soya mai ɗauke da isoflavones, yayin da wasu suka sha wani furotin daban. Sakamakon ya nuna: Raguwar tsananin layukan fuska da kashi 7 cikin 100. Rage duhun fata da kashi 2 cikin 100. ƙaruwa a danshin fata har kashi 68 cikin 100 a wani ɓangare na fuska.…
Read More
Soyayya kafin aure: Gari ya waye, amma hankali na barci

Soyayya kafin aure: Gari ya waye, amma hankali na barci

Daga AISHA ASAS  'Soyayya kafin aure, tamkar cin abinci ne a kasuwa, ba a san lafiya ko cutar sa ba' Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon shafin zai yi dubiya ne kan yadda soyayyar yara kafin aure ke wanzuwa, me ke janyo ta, wane irin lahani take haifarwa, da kuma yadda za a magance ta cikin hikima. Kafin komai zan faro da kai hanakalin mai karatu ga hanyar da rubutun nawa ya karkata. Soyayyar da take rubuce a wasu littafai musamman na Turawa a matsayin wayewa, soyayyar da ke ƙawata…
Read More
Hisbah ta Katsina ta buƙaci ɗan Kasuwa ya janye zargin da ya yi wa hukumar na sata

Hisbah ta Katsina ta buƙaci ɗan Kasuwa ya janye zargin da ya yi wa hukumar na sata

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta buƙaci wani Alhaji Jibrin Tanimu da ya janye zargin da ta bayyana a matsayin na ƙarya da kuma ɓata suna ga hukumar cikin kwana bakwai. A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 29 ga Maris, 2026, wacce aka aika wa Tanimu a Modoji, ƙaramar hukumar Katsina, hukumar ta zarge shi da yin ikirarin cewa jami'anta sun sace masa Naira miliyan 221. A cewar wasiƙar, an yi zargin ne a ranar ko kuma kusan 10 ga Maris, 2026, bayan da hukumar ta kama shi a gidansa. Hukumar ta kuma yi…
Read More
Majalisar dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnati ta ɗauki mataki kan matsalar ƙauraye

Majalisar dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnati ta ɗauki mataki kan matsalar ƙauraye

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan Majalissa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba shi ne ya gabatar da ƙudurin, inda yace matsalar ƙauranci na addabar al’ummar garin Katsina, inda ya bada misalai na irin mummunan aika aika da ƙauraye su keyi, wanda yake jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Majalisar ta bawa kwamitin tsaro na majalissar sati ɗaya, da yaje yayi bincike, ya kawo rahoto akan hanyoyin da ya kamata abi na doka domin a magance matsalar. Kwamitin zai haɗa kai tare da jami’an tsaro na jihar Katsina, domin samo hanyar da za’a magance matsalar. Ka zalika…
Read More