ukarofi

12593 Posts
Gwamnatin APC ke kunna wutar rikici a jam’iyyun adawa – ADC

Gwamnatin APC ke kunna wutar rikici a jam’iyyun adawa – ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam'iyyar hamayya ta ADC a Nijeriya ta yi watsi da matakin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na cire sunan Sanata Daɓid Mark da sauran 'yan kwamitin zartarwar ta daga shafinta na yanar gizo. A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, INEC ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato Daɓid Mark da na Nafi'u Gombe. A wani hukunci da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 12…
Read More
Yadda Gwamna Bala ya bayyana yiwuwar sauya sheƙa zuwa ADC 

Yadda Gwamna Bala ya bayyana yiwuwar sauya sheƙa zuwa ADC 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana yiwuwar sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ta ADC, yana mai danganta hakan da rikicin da yake ci gaba da addabar jam’iyyar tasa ta yanzu. Gwamna Bala Mohammed, wanda kuma shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin tawagar jam’iyyar ADC a ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi. Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri, gwamnan ya ce yiwuwar sauya shekar tasa na da nasaba…
Read More
Gargaɗin EFCC ga ƙungiyoyi kan tallafa wa ta’addanci a ɓoye

Gargaɗin EFCC ga ƙungiyoyi kan tallafa wa ta’addanci a ɓoye

A wani mataki na ƙara ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon ƙasa da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya gargaɗi ƙungiyoyin sa-kai (NPOs) da su yi taka-tsantsan da yiwuwar shigar ‘yan ta’adda cikin harkokinsu domin amfani da su wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci. An bayyana wannan gargaɗi ne a yayin ƙaddamar da rahoton tantance haɗarin samar da kuɗaɗen ta’addanci a tsakanin ƙungiyoyin sa-kai (NTFRA) da aka gudanar a Abuja. Shugaban hukumar ya jaddada muhimmiyar rawar da waɗannan ƙungiyoyi ke takawa wajen tallafa wa jama’a, musamman a fannoni kamar…
Read More
Yadda sabon rikicin Jos ya dawo ɗanye

Yadda sabon rikicin Jos ya dawo ɗanye

*IGP Disu ya ziyarci Filato  *'Yan majalisun tarayya daga Filato sun kai ziyarar jaje Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, a Jos  Al'ummar garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato, sun sake shiga wani sabon ruɗani da firgici sakamakon ɓarkewar wani sabon rikici, wanda ya samo asali daga harin ’yan bindiga da aka kai wani yanki na unguwar Rukuba da ake kira Gari Ya Waye, inda ake cin kasuwar dare da mashaya. An kai wannan hari ne ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026, da daddare da misalin ƙarfe 8:00 na dare, yayin da yankin ke tsaka da hada-hada, kamar yadda aka saba. Wannan…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnatin Jihar kan aikin wutar lantarki a Charanchi

Majalisar Dokokin Katsina ta yi kira ga gwamnatin Jihar kan aikin wutar lantarki a Charanchi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kiran ya biyo bayan sake kai ƙuduri akan neman gwamnati ta cigaba da aikin wutar lantarki a mazaɓar Dan Makwaro 'A' da Dan Makwaro 'B', Tsakatsa da kuma Rugar Wake, da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Charanchi Hon. Lawal Isah Kuraye, a karo na biyu a gaban majalisar. A inda ya bayyana cewa, wannan aiki ya kai kimanin shekar 9 ana wannan aiki sai an fara sai a tsaya don haka yake sake kira ga gwamnati da ta dubi wannan al'umma na wannan mazaɓu don a cigaba da wannan aiki. Saboda muhimmacin wannan ƙuduri…
Read More
Akwai yiwuwar ɗan tsohon shugaban ƙasa Buhari ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya

Akwai yiwuwar ɗan tsohon shugaban ƙasa Buhari ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya

Daga UMAR GARBA a Katsina Rahotanni sun bayyanawa cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya amince da Yusuf Buhari ɗan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar APC takarar ɗan majalisar tarayya a mazaɓar Daura, Mai 'adua da Sandamu. Bayanin haka na ƙunshe cikin wani taro na masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Sandamu ta jihar Katsina, 'yan jam'iyyar sun nuna muhimmancin ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar APC kafin zaɓen 2027, saboda haka ne suka goyi bayan Yusuf Buhari, ɗan tsohon shugaban Najeriya Muhammad Buhari, a matsayin wanda aka fi so…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya taya FRCN murnar cika shekaru 75 da kafuwa

Gwamna Raɗɗa ya taya FRCN murnar cika shekaru 75 da kafuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya gidan rediyon Nijeriya murnar cika shekaru 75 da kafuwa. Gwamnan ya yaba wa shugabanni da ma’aikatan kafar yaɗa labaran bisa shekaru 75 na sadaukar da kai wajen yi wa ƙasa hidima. “Gidan Rediyon tarayya (FRCN) ta kasance ginshiƙi wajen yaɗa bayanai da kuma ci gaban ƙasa tsawon shekaru 75. Kun ilmantar da miliyoyin jama’a, kun sanar da miliyoyi, kuma kun nishaɗantar da miliyoyi,” in ji Gwamna Raɗɗa. Gwamnan ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da rediyo ke takawa wajen isa ga ‘yan Najeriya a faɗin ƙasa, inda…
Read More
SPRING ta shirya taron ƙara wa juna sani kan yaƙi da cin zarafin mata da yara

SPRING ta shirya taron ƙara wa juna sani kan yaƙi da cin zarafin mata da yara

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wata cibiyar ƙarfafa zaman lafiya da samar da mafita kan cin zarafin mata (SPRING) da ƙasar UK ke ɗaukar nauyi,ta shirya taron ƙarawa juna sani mai taken 'mata ,zaman lafiya, tsaro da yaƙi da cin zarafin mata 'a Katsina. Wannan shiri na SPRING da UK ta ɗsuki nauyi ,shiri ne na tsawon shekaru huɗu da ke gudana a Arewacin ƙasar. A wata hira da manema labarai,manajan shirin na wannan yankin Alhaji Abdulkadir Sambo ya ce an shirya taron ƙarawa juna sani domin ƙarfafa kuzari na masu ruwa da tsaki kan wannan yaƙi da cin zarafin…
Read More
DSS sun kama wata matashiya mai kai wa ‘yan bindiga alburusai a Katsina

DSS sun kama wata matashiya mai kai wa ‘yan bindiga alburusai a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Jami'an tsaron DSS sun kama wata matashiya mai suna Nafisa Usman mai shekaru 25 da alburusai na bindiga za ta kai wa ɓarayin daji. An kama Nafisa a tashar mota na unguwa uku dake birnin Kano bayan an kawo mata harsashin daga garin Lafia na jihar Nasarawa, ita kuma za ta kai garin ƙanqara na Jihar Katsina. Nafisa ta ce asalinta 'yar garin ƙauyen Zango ce da ke ƙaramar hukumar Ƙanqara a jihar Katsina, kuma a yanzu ta shiga wata na huɗu kenan a wannan baƙar sana'a na safaran makamai zuwa ga ɓarayin daji. A…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta aurar da Mata 1,000

Gwamnatin Katsina za ta aurar da Mata 1,000

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina‎‎Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da wasu kwamitoci na musamman domin tsara yadda za a gudanar da shirin auren gata ga mata 1,000 tare da wayar da kan su kan muhimmancin zaman aure a musulunci.‎‎Da yake ƙaddamarwar da kwamitocin, Kwamishinan ma'aikatan addini, Hon. Ishaq Shehu Dabai,‎ ya ce shirin na da muhimmanci wajen rage matsalolin zamantakewa da kuma tallafa wa matasa da mata su samu ingantacciyar rayuwar aure, inda ya gode wa gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda, bisa goyon bayan da ya bayar kan lamarin.‎‎Shi ma Shugaban Hukumar Hizbah, Dr. Usman (Malam Abu Ammar), ya…
Read More