03
Apr
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani ɗan hidimar ƙasa, wato NYSC, Abba Musa, ya samu ’yancinsa bayan shafe watanni uku yana tsare a hannun ’yan bindiga, lamarin da ya kawo ƙarshen damuwa da fargabar da ta dabaibaye iyalansa da al’umma baki ɗaya. Rahotanni sun nuna cewa an sako Musa ne a ranar Laraba bayan dogon tattaunawa da matsin lamba daga ’yan Nijeriya da dama da suka bi diddigin lamarin tun daga ranar da aka sace shi. Fitowarsa daga hannun masu garkuwa da mutane ta jawo farin ciki ga waɗanda suka daɗe suna addu’ar ganin ya dawo lafiya. A cikin wani bidiyo…
