ukarofi

12593 Posts
A Amurka Iran za ta buga Gasar Kofin Duniya duk da rikicin Gabas ta Tsakiya – Infantino

A Amurka Iran za ta buga Gasar Kofin Duniya duk da rikicin Gabas ta Tsakiya – Infantino

Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya tabbatar da cewa, tawagar ƙasar Iran za ta halarci Gasar Kofin Duniya ta 2026 a ƙasar Amurka kamar yadda aka tsara tun farko, duk kuwa da ƙalubalen siyasa da tsaro da ke ƙara ta’azzara a duniya. A wata hira da ya yi da tashar N+ Univision, wadda kamfanin dillancin labarai na Jamus (dpa) ya rawaito, Infantino ya ce babu wani shiri na madadin da FIFA ke da shi dangane da tsarin gasar, yana mai jaddada cewa shirin farko kaɗai ake da shi. “Mu na rayuwa a cikin gaskiya, kuma mun…
Read More
Tsaron gida ya fi kai hari muhimmanci — Ancelotti ya bayyana sirrin lashe Kofin Duniya

Tsaron gida ya fi kai hari muhimmanci — Ancelotti ya bayyana sirrin lashe Kofin Duniya

Kocin ƙasar Brazil, Carlo Ancelotti, ya tayar da muhawara a fagen dabarun ƙwallon ƙafa bayan ya jaddada cewa tsaron gida mai ƙarfi ne ginshiƙin nasarar lashe Gasar Kofin Duniya na FIFA, ba yawan cin ƙwallaye ba. Ancelotti ya bayyana haka ne yayin wata ganawar manema labarai da aka gudanar kafin wasan sada zumunci tsakanin Brazil da Croatia a Orlando, inda ya ce tarihin gasar ya nuna cewa ƙungiyar da ke rage yawan ƙwallayen da ake zura mata ita ce mafi yawan lashe kofin. A cewarsa, duk da cewa kai hari yana buƙatar ƙwarewa da basira, tsaron gida yana buƙatar tsari…
Read More
Hujjar INEC ta cire shugabannin ADC ƙarƙashin David Mark daga shafinta na yanar gizo 

Hujjar INEC ta cire shugabannin ADC ƙarƙashin David Mark daga shafinta na yanar gizo 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cewa, ta daina amincewa da kowanne daga cikin ɓangarorin jam’iyyar ADC biyu da suke rikici da juna a kotu; wanda Daɓid Mark ke jagoranta da kuma tsagin Nafiu Bala, bayan nazarin hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da aka yanke a ranar 12 ga Maris, 2026. A wata sanarwa da Shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kai na INEC, Mohammed Kudu, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce daga yanzu ba za ta ƙara karɓar kowanne irin wasiƙa daga kowanne ɓangare ba. Haka kuma,…
Read More
Kotu ta soke umarnin kama Turaki, shugaban tsagin PDP

Kotu ta soke umarnin kama Turaki, shugaban tsagin PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata Babbar Kotun Abuja a ranar Laraba ta soke umarnin kamawa da ta bayar a ranar 26 ga Maris domin cafke shugaban jam’iyyar PDP na wani ɓangare, Kabiru Turaki. Mai shari’a Peter Kekemeke ya soke umarnin kama ne yayin da yake yanke hukunci kan roƙon baki da lauyan Turaki, Chris Uche SAN ya gabatar, bayan bayyanar Turaki a kotu. Da aka kira shari’ar, Uche ya nemi afuwar kotu kan rashin halartarsa a ranar da ta gabata. Mista Uche, wanda ya ce yana waje ne a ƙasar, ya bayyana cewa ya dawo ne da safiyar…
Read More
Akpabio ya ayyana kujerun sanatoci uku a matsayin babu kowa

Akpabio ya ayyana kujerun sanatoci uku a matsayin babu kowa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talata ya ayyana kujerun Sanata uku a matsayin babu kowa biyo bayan rasuwar mambobin Majalisar Dattawa ta 10. Mazaɓun da abin ya shafa sun haɗa da Enugu ta Arewa, Nasarawa ta Arewa, da Ribas ta Kudu maso Gabas. Mista Akpabio ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisa, inda ya ce guraben sun samu ne sakamakon rasuwar sanatocin da ke wakiltar waɗannan yankuna, bisa tanadin kundin tsarin mulki. “Saboda waɗannan abubuwan bakin ciki da suka faru ga Majalisar Dattawa ta 10, an samar da gurabe domin gudanar da…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu, sun sace 11 a Sakkwato

‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu, sun sace 11 a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da sace wasu mutum 11, sannan sun raunata mutum biyu a garin Malamawar Yari da ke ƙaramar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato. ‘Yan bindigar sun kai wa garin hari ne da misalin ƙarfe 11:40 na ranar Talata, inda suka sace mata takwas, da maza uku, da ƙaramin yaro. Mazauna garin sun bayyana cewa mutum bakwai daga ciki ‘yan gida ɗaya ne, sai kuma mata bibbiyu daga gidaje guda biyu. “Sun shigo ƙauyenmu ta hanyar da ta haɗa mu da ƙaramar hukumar Rabah. Suna shigowa suka hau harbi…
Read More
PRP za ta gyara Nijeriya idan aka zaɓe ta — Baba-Ahmed

PRP za ta gyara Nijeriya idan aka zaɓe ta — Baba-Ahmed

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sabon Shugaban Jam’iyyar PRP na ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa jam’iyyar ce kaɗai za ta iya magance matsalolin da ke addabar Nijeriya idan har ta samu nasara a zaɓen shekarar 2027. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Abuja. Baba-Ahmed, ya jaddada cewa PRP jam’iyya ce mai haɗin kai wadda ba ta fama da rikici. Ya ƙara da cewa har yanzu jam’iyyar tana da yaƙinin cewa Nijeriya za ta gyaru, kuma ta shirya samar da mafita ga dukkanin ƙalubalen da ƙasar…
Read More
An yaba wa Sarkin Biu bisa kyakkyawan jagorancinsa na bunƙasa masarautar 

An yaba wa Sarkin Biu bisa kyakkyawan jagorancinsa na bunƙasa masarautar 

Daga GAMBO ISA a Abuja  Shugaban ƙungiyar Al’ummar Borno a Arewa maso Gabas (BOCN), Alhaji Bulama Hassan, ya yaba wa Sarkin Biu, Alhaji Dakta Mustapha Umar Mustapha na II, bisa kyakkyawan jagorancinsa da kuma rawar da yake takawa irin ta uba wajen bunƙasa ci gaban masarautar Biu a Jihar Borno. A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma aka rabawa jaridar Blueprint a Abuja, Bulama Hassan ya bayyana hakan ne yayin bikin naɗa rawani ga ɗiyar masarautar, Hajiya Larai Umar Mustapha, wadda ita ce Babbar Sakatariya ta ƙaramar hukumar Kwaya Kusar. An naɗa ta da sarautar “Majira ta…
Read More
El-Rufai zai ci gaba da zama a tsare har zuwa 14 ga Afrilu

El-Rufai zai ci gaba da zama a tsare har zuwa 14 ga Afrilu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kaduna, ta ɗage sauraron buƙatar bayar da belin da tsohon Gwamnan Jihar, Nasir Ahmad El-Rufai, ya shigar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu. Alƙalin kotun, Rilwanu Aikawa, ya sanya ranar ne bayan ya saurari hujjoji daga lauyoyin El-Rufai da kuma masu gabatar da ƙara a ranar Laraba. Hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 10, ciki har da zargin karkatar da kadarorin gwamnati da kuma almundahanar kuɗaɗe. Ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa. Kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da…
Read More
Shugaban APC ya gana da Bala Mohammed kan jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa ADC

Shugaban APC ya gana da Bala Mohammed kan jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kasa da sa’o’i 24 da ziyarar da wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC suka kai wa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, kan yiwuwar komawa jam’iyyarsu, tawagar jam’iyyar APC, ta yi dirar mikiya a jihar. Tawagar ta haɗa da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. Sun tafi kai-tsaye ofishin Gwamnan a Gidan Gwamnatin Bauchi, inda suka yi ganawar sirri da shi. Da akwai wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka kasance a ganawar, ciki har da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Y. Suleiman, Sakataren Gwamnatin Jihar, Aminu…
Read More