04
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Sufuri Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, ya ajiye muƙaminsa domin fitowa takarar Gwamnan Jihar Gombe. Da haka ya shiga jerin jami’an Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu da suka ajiye mukamansu domin neman takara a zaben shekarar 2027. Ya ajiye mukamin nasa ne sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da shugaban kasa ya ba wa jami’an gwamnatinsa da ke da muradin tsayawa takara su ajiye mukaminsu. Sauran ministocin da suka ajiye mukamansu sun hada da Ministan Harkokin Waje, Ahmed Tuggar, wanda ke neman fitowa takarar Gwamnan Jihar Bauchi da kuma Karamin Minista, Sununu da ke son…
