ukarofi

12592 Posts
NELFUND ta musanta jita-jitar ƙarin alawus ga ɗalibai

NELFUND ta musanta jita-jitar ƙarin alawus ga ɗalibai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Asusun Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND) ya bayyana cewa har yanzu alawus na kulawa da rayuwa da ake bai wa ɗalibai masu cin gajiyar shirin yana nan a kan Naira 20,000 a kowane wata, yana mai ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an ƙara shi zuwa N25,000. A cikin wata sanarwa da aka fitar a daren ranar Litinin, wadda Daraktar Sadarwa ta Tsare-tsare ta asusun, Oseyemi Oluwatuyi, ta sanya wa hannu, NELFUND ya gargaɗi ɗalibai da su yi watsi da duk wani bayani da ya saɓa da wannan, tare da…
Read More
Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da asusun tsaro na Naira biliyan ɗaya a kowane wata

Gwamnonin Arewa sun ƙaddamar da asusun tsaro na Naira biliyan ɗaya a kowane wata

* Sun sake kira ga ‘yan sandan jihohi Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun sake jaddada bukatar yin garambawul cikin harkar tsaro, ƙarfafa haɗin gwiwar yankin, da kuma zuba jari mai ɗorewa domin ci gaba. A wani taro da suka gudanar a Abuja ƙarƙashin ƙungiyar Northern States Goɓernors’ Forum (NSGF), shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa an samu “ingantaccen ci gaba” a harkar tsaro tun bayan taron da suka yi a watan Disambar 2025. Sai dai ya gargaɗi cewa wannan ci gaba bai kamata ya sa a yi sakaci ba.…
Read More
Nijeriya ta fitar da hanyoyin dogaro da kanta a fannin lafiya, inji Minista

Nijeriya ta fitar da hanyoyin dogaro da kanta a fannin lafiya, inji Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin tarayya ta ce ta ɗauki matakai domin rage dogaro da tallafin kuɗin da ake samu daga ƙasashen waje da ƙarfafa samar da kuɗi a cikin gida da ci gaba da mutunta abokan hulɗa na ƙasashen waje. Muhammed Pate, ministan lafiya da walwalar jama’a, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja a wurin wani taron tattaunawa na lafiya da ƙasar Sin kan yadda za a shirya wa tunƙarar ɓarkewar annoba. A yayin da yake duba kan irin ƙoƙarin daƙile cutattuka a duniya, Pate ya ce, duk da cewa tallafin ƙasashen waje ya…
Read More
Kotu ta tsare direban matar Sarki Sanusi II kan satar gwala-gwalai na miliyan N60

Kotu ta tsare direban matar Sarki Sanusi II kan satar gwala-gwalai na miliyan N60

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata Kotun Majistare da ke Nomansland a ƙaramar Hukumar Fagge, Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu kan zargin satar gwala-gwalai da kuɗi da kuma wayar salula.   Masu laifin da ake tuhuma su ne Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini. An gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumar haɗin baki, sata da kuma karɓar kayan sata. Lauyan masu gabatar da ƙara, Barista Abubakar Ibrahim, ya shaida wa kotu cewa Sulaiman Yakubu, wanda shi ne direban matar Sarki…
Read More
Majalisa ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan shida 

Majalisa ta amince Tinubu ya ciyo bashin Dala biliyan shida 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Malalisar Dattawa ta amince wa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ciyo basin Dala biliyan shida domin rage bashin da ake bin Nijeriya da kuma gyaran tashoshin jiragen ruwa da ke Jihar Legas. Wannan rance zai ƙara yawan bashin da ake bin Nijeriya daga dala biliyan 110.3 zuwa Dala biliyan 115.3. Sauran amfanin da za a yi da kuɗaɗen sun haɗa da ayyukan gine-gine, da kuma cike gibin da aka samu a kasafin kuɗin ƙasar. A ranar Talata Majalisar ta amince da buƙatar ƙasar bayan karanta wasiƙu biyu daban-daban da Shugaban ƙasa ya aika…
Read More
Majalisar Dattawa ta amince da kasafin 2026 ba tare da bincike kan ƙarin buƙatar Tinubu ba

Majalisar Dattawa ta amince da kasafin 2026 ba tare da bincike kan ƙarin buƙatar Tinubu ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kuɗin shekarar 2026 a ranar Talata, bayan ƙara Naira tiriliyan 9.3 da Bola Tinubu ya nema, wanda ya kai jimillar kasafin zuwa N68.323 tiriliyan. Baya ga amincewa da buƙatar shugaban ƙasar, majalisar ta ƙara Naira biliyan 623 a kan adadin da aka gabatar, inda aka ɗaga kasafin daga N67.7 tiriliyan zuwa N68.323 tiriliyan. An amince da kasafin ne ta hanyar jefa ƙuri’a ta murya (ɓoice ɓote), inda yawancin sanatoci suka nuna goyon bayansu. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da amincewar kasafin bayan kammala ƙuri’ar.…
Read More
Jama’a sun kashe ɓarawon waya a Kano

Jama’a sun kashe ɓarawon waya a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dubun wasu matasa biyu da ake zargi da satar waya ta cika, bayan da taron jama’a ya afka musu a kusa da makarantar Fatima Special Primary School, da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, a gaban ƙofar Asibitin Koyarwa na Aminu Kano. Shaidu sun ce wata da farko matasan sun far wa wata budurwa da wuka, inda saboda tsoron kada su kai mata hari, ta mika musu wayar salim-alim. Bayan haka, sai suka kai wa wani mutum da ke wucewa hari suka kwace wayarsa. Wannan ne ya jawo hankalin masu wucewa, suka yi ƙarfin hali suka fuskance…
Read More
Gwamnatin Tarayya na shirin tallafa wa gidaje miliyan 15 ta hanyar HoPE-CT – Idris

Gwamnatin Tarayya na shirin tallafa wa gidaje miliyan 15 ta hanyar HoPE-CT – Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kai tallafi ga gidaje masu rauni miliyan 15 a faɗin ƙasar nan ta hanyar Shirin Tallafin Kuɗi na Inganta Rayuwar Iyali (HoPE-CT). Idris, wanda Daraktan Hulɗa da Jama’a a ma’aikatar, Dakta Suleiman Haruna, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin taron bayani kan aiwatar da shirin da kuma ganawa da manema labarai. Ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen tallafin jama’a mafi tasiri, yana mai cewa ya riga ya kai…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutane 13, sun yi awon gaba da masu ɗaurin aure a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutane 13, sun yi awon gaba da masu ɗaurin aure a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ibtila’in ayyukan ‘yan bindiga ya samu al’ummar ƙauyen Kahir da ke ƙaramar Hukumar Kagarko a jihar Kaduna, inda wasu ‘yan bindiga a ranar Lahadi suka dirar wa ƙauyen ana bikin ɗaurin aure tare da kashe mutane 13 da aka gayyata da sace wasu da dama. Mazauna ƙauyen sun ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 11:47 na rana wanda ya haifar da tsoro a faɗin ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar tare da tilasta wa wasu da dama guduwa su bar gidajensu. Maharan sun zo ne da yawansu tare da manyan makamai inda suka…
Read More
Ministan Sufuri ya yi murabus don fitowa takarar Gwamnan Gombe

Ministan Sufuri ya yi murabus don fitowa takarar Gwamnan Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Sufuri Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, ya ajiye muƙaminsa domin fitowa takarar Gwamnan Jihar Gombe. Da haka ya shiga jerin jami’an Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu da suka ajiye mukamansu domin neman takara a zaben shekarar 2027. Ya ajiye mukamin nasa ne sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da shugaban kasa ya ba wa jami’an gwamnatinsa da ke da muradin tsayawa takara su ajiye mukaminsu. Sauran ministocin da suka ajiye mukamansu sun hada da Ministan Harkokin Waje, Ahmed Tuggar, wanda ke neman fitowa takarar Gwamnan Jihar Bauchi da kuma Karamin Minista, Sununu da ke son…
Read More