Hujjar INEC ta cire shugabannin ADC ƙarƙashin David Mark daga shafinta na yanar gizo 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cewa, ta daina amincewa da kowanne daga cikin ɓangarorin jam’iyyar ADC biyu da suke rikici da juna a kotu; wanda Daɓid Mark ke jagoranta da kuma tsagin Nafiu Bala, bayan nazarin hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da aka yanke a ranar 12 ga Maris, 2026.

A wata sanarwa da Shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kai na INEC, Mohammed Kudu, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce daga yanzu ba za ta ƙara karɓar kowanne irin wasiƙa daga kowanne ɓangare ba.

Haka kuma, INEC ta bayyana cewa ba za ta yi hulɗa da kowanne bangare ba, kuma ba za ta sa ido kan taruka, zaɓukan cikin gida (congresses), ko manyan tarukan jam’iyyar (conventions) na ɓangarorin biyu ba, har sai kotu ta yanke hukunci kan rikicin.

Bugu da ƙari, hukumar ta sanar da cewa za ta cire sunan Daɓid Mark daga kundin bayananta na yanar gizo.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan Rafiu Bala, wanda a baya ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar ADC kafin kwamitin riko ƙarƙashin jagorancin David Mark ya karɓi ragamar jam’iyyar, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar sahihancin shugabancin sabon kwamitin.

By ukarofi