Kungiyar KAPAG ta ziyarci shugaban ƙaramar hukumar Tarauni

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kungiyar KAPAG ƙarƙashin jagorancin Hajiya Balaraba Ibrahim ta kai ziyarar girmamawa ga shugaban ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Sekure, a sakatariyar ƙaramar hukumar a ranar Litinin.

Hajiya Balaraba ta bayyana cewa dawowar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, jam’iyyar APC wani muhimmin al’amari ne a tarihin siyasar jihar, tana mai cewa siyasa tafiya ce ta haɗin kai duk da sauye-sauyen jam’iyyu da ake samu lokaci zuwa lokaci.

Ta ce, a matsayinsu na ƙungiya da ta dade tana aiki tun daga tushe sama da shekaru 25, sun ga dacewar su mara wa duk wanda ya dawo APC baya, musamman ma gwamnan jihar a wannan lokaci.

A cewarta, ƙungiyar KAPAG ta ginu ne daga jama’a na ƙasa, kuma manufarta ita ce hada kan al’umma domin ci gaban jihar Kano.

Hajiya Balaraba ta ce ziyarar da suka kai wa shugaban ƙaramar hukumar Tarauni wata hanya ce ta jaddada goyon bayansu gare shi, tana mai cewa babu wani bambanci a tsakaninsu duk da sauye-sauyen siyasa da aka samu a baya.

Ta yi kira ga ’yan jam’iyya da shugabanni a matakin ƙasa da na ƙaramar hukuma, musamman a Tarauni, da su guji rikice-rikicen cikin gida marasa amfani, tana mai jaddada cewa neman muƙami bai kamata ya haddasa gaba a tsakanin ’yan siyasa ba.

Ta ce Allah ne kadai ke bayar da mulki, don haka haɗin kai da taimakon al’umma ya kamata su fi zama gaba.

Ta ƙara da cewa, ƙungiyar KAPAG za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar APC goyon baya dari bisa dari, domin yawancin mambobinta sun daɗe tare a tafiyar siyasa tsawon shekaru.

A cewarta, bambancin ra’ayi abu ne na ɗabi’a a dimokuradiyya, amma bai kamata ya rusa zumunci da mutunta juna ba.

Hajiya Balaraba ta bayyana cewa duk da bambancin siyasa da kan taso, sukan ajiye siyasa a gefe idan ana mu’amala ta zamantakewa, suna halartar bukukuwa da lokutan jaje ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.

Ta kuma yabawa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa rawar da ya taka wajen ganin an samu sulhu da dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf jam’iyyar APC. Ta yi masa fatan alheri tare da addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

A ƙarshe, ta ce ziyarar Tarauni ita ce ta farko a jerin ziyarce-ziyarce da ƙungiyar za ta kai ƙananan hukumomi 44 na jihar, domin haɗa kan ’yan jam’iyya da ƙarfafa goyon baya gabanin zaɓuɓɓukan 2027, inda take da yaƙinin samun nasara da yardar Allah.

By ukarofi