28
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon muƙaddashin Akanta-Janar na Tarayya, Chukwunyere Nwabuoku, hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari ba tare da zaɓin tara ba, bayan samunsa da laifin badaƙalar kuɗaɗe har naira miliyan 868. Da yake yanke hukuncin a ranar Litinin, alƙalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa, ta tabbatar da tuhume-tuhumen almundahanar kuɗaɗe har guda tara da ake yi masa ba tare da wata shakka ba. Kotun ta same shi da laifi a dukkan…
