ukarofi

12594 Posts
Duk da saɓanin siyasa, NSA ya yi wa El-Rufai ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Duk da saɓanin siyasa, NSA ya yi wa El-Rufai ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa

Daga USMAN KAROFI Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Ribadu ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai kulawa, inda ya ce yana da kyawawan abubuwan tunawa da suka haɗa shi da ita. Ribadu ya bayyana hakan ne a cikin saƙon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, inda ya jajanta wa iyalan El-Rufai tare da tuna lokutan da suka yi tare da marigayiyar. “Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Na yi matuƙar baƙin ciki da…
Read More
Ƙungiyar Iran ta kutsa imel ɗin Daraktan FBI

Ƙungiyar Iran ta kutsa imel ɗin Daraktan FBI

Daga USMAN KAROFI Wata ƙungiyar masu satar bayanai da ake danganta da Iran ta samu damar shiga asusun imel na Daraktan FBI, Kash Patel, sannan ta wallafa hotuna na sirri da wasu bayanai a yanar gizo, rahoton kafofin watsa labarai na Amurka ya bayyana ranar Juma’a. Ƙungiyar Handala Hack Team ta ce Patel “za ya ga sunansa a cikin jerin waɗanda aka samu nasarar satar bayanansu”. Rahoton CNN ya bayyana cewa imel ɗin da aka sace sun haɗa da na sirri, harkokin kasuwanci da na tafiye-tafiye, wanda suka shafi shekaru 2011 zuwa 2022, kafin Patel a nada shi Daraktan FBI…
Read More
A karon farko Soludo ya naɗa mace a matsayin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Anambra

A karon farko Soludo ya naɗa mace a matsayin Sakatariyar Gwamnatin Jihar Anambra

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya amince da naɗin Misis Chiamaka Nnake a matsayin sabuwar Sakatariyar Gwamnatin Jiha (SSG), lamarin da ya sa ta zama mace ta farko da ta riƙe wannan muƙami a tarihin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Christian Aburime, ya fitar a ranar Litinin, ya ce naɗin ya fara aiki nan take, inda ta maye gurbin Farfesa Solo Chukwulobelu wanda ya fita daga muƙaminsa bayan rusa majalisar zartarwar jihar. Nnake mai shekaru 39, ‘yar asalin Nawfia ce da ke ƙaramar hukumar Njikoka a jihar Anambra.…
Read More
Tsare-tsaren da muka gabatar wa jam’iyyun siyasa – INEC

Tsare-tsaren da muka gabatar wa jam’iyyun siyasa – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Zaɓe ta Nijeriya (INEC) ta gabatarwa jam'iyyun siyasar ƙasar sabbin tanade-tanaden da ta yi domin shirya babban zaɓen 2027 da ke tafe. Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin bai wa jam'iyyun siyasar damar bayar da gudunmuwa ta fannin shawarwari da jan hankali kan yadda za a gudanar da zaɓe mai inganci a 2027. Shugaban Hukumar Farfesa Joash Amupitan, wanda ya jagoranci wani taron tattaunawa da shugabannin jam'iyyun Nijeriya  a Abuja babban birnin ƙasar ya ce sabbin tanade-tanaden sun tafi daidai da dokar zaɓe ta 2026, kuma za su taimaka wajen…
Read More
Muna fama da ƙarancin jami’ai mata a Kano — NDLEA

Muna fama da ƙarancin jami’ai mata a Kano — NDLEA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kwamandan Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) a Jihar Kano, CN D.Y. Lawal ya nuna damuwa kan ƙarancin jami’ai mata a rundunar a jihar, lamarin da ya bayyana a matsayin babban ƙalubale da ke kawo masu cikas kan ayyukansu. Lawal ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar don murna da Ranar Mata ta Duniya a Kano a ranar Talata. Taron wanda CDC Kano, wani shiri na musamman da aka shirya ƙarƙashin Cibiyar Isa Wali Shugaban ya ce ƙarancin mata a hukumar na kawo cikas wajen…
Read More
Kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a da jagorantar alƙiblar ƙasa

Kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a da jagorantar alƙiblar ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce kafafen yaɗa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, ƙarfafa ɗaukar nauyin abin da ka aikata, da kuma jagorantar alƙiblar ƙasa. Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a lokacin wani taron wayar da kai ga kafafen yaɗa labarai kan yaƙi da halatta kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci (AML/CFT). Babban Sakataren Hukumar Kula da Ayyukan Jarida ta Nijeriya, Dakta Dili Ezughah, shi ne ya wakilci ministan. A jawabinsa, Ministan ce: “Kafafen yaɗa labarai ba…
Read More
KANSIEC ta miƙa takardar shaidar lashe zaɓe ga Hon. Hardworker bisa umarnin kotu a Kumbutso

KANSIEC ta miƙa takardar shaidar lashe zaɓe ga Hon. Hardworker bisa umarnin kotu a Kumbutso

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta miƙa takardar shaidar cin zaɓe ga Hon. Ali Musa “Hardworker,” inda ta tabbatar da shi a matsayin halastaccen Shugaban ƙaramar Hukumar Kumbotso, biyo bayan umarnin kotu. Yayin miƙa takardar, Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi, ya bayyana cewa hukumar na aiki ne bisa tanadin doka wajen gudanar da zaɓe da kuma bayyana waɗanda suka yi nasara a matakai daban-daban. Ya ce matakin da aka ɗauka ya biyo bayan hukuncin kotu ne wanda ya tabbatar da Hon. Ali Musa Hardworker a matsayin wanda ya lashe zaɓen,…
Read More
Mataimakin gwamnan Jihar Kano ya yi murabus

Mataimakin gwamnan Jihar Kano ya yi murabus

Daga USMAN KAROFI Mataimakin gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya yi murabus daga muƙaminsa, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana a ranar Juma’a. Kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Habibu Sale Mohammed, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an sanar da jama’a matakin da aka ɗauka. Kafin wannan mataki, majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin gwamnan daga muƙaminsa, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasar jihar. Haka kuma, wata kotun tarayya da ke Kano ta ƙi amincewa da buƙatar da Abdussalam ya gabatar na dakatar da shirin tsige shi. Sanarwar ta bayyana cewa murabus ɗin…
Read More
Sheik Khalifa Sani yana raye – Rahoto na musamman

Sheik Khalifa Sani yana raye – Rahoto na musamman

Daga USMAN KAROFI Wani rahoto na musamman da jaridar PRNigeria ta wallafa ya bayyana cewa malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheikh Khalifa Sani Abdulkadir, wanda aka sanar da ɓacewarsa a makonnin baya, yana raye kuma yana hannun jami’an tsaro na tarayya a matsayin “kariya ta musamman.” Rahoton ya nuna cewa ana tsare da shi ne yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu zarge-zarge da suka shafi tsaro. Majiyoyi daga ɓangaren tsaro sun ce ana gudanar da bincike kan malamin ne tare da haɗin gwiwar sojojin Najeriya da kuma hukumar DSS, bisa zargin alaƙa da wani…
Read More
Iran na tattara dakaru miliyan ɗaya don tunkarar rundunar Amurka da ke shirin kutse

Iran na tattara dakaru miliyan ɗaya don tunkarar rundunar Amurka da ke shirin kutse

Daga USMAN KAROFI Rahotanni daga ƙasashen duniya sun bayyana cewa ƙasar Iran ta fara shirye-shiryen tsaro inda ake zargin ta tattara sama da sojoji miliyan ɗaya domin fuskantar yiwuwar harin ƙasa daga Amurka. Wannan mataki ya biyo bayan ƙarin tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu, inda ake zargin Amurka na nazarin hanyoyin matsa lamba domin tilasta Iran amincewa da wasu sharuɗɗan sulhu. Majiyoyin cikin gida a Iran sun bayyana cewa matasa da dama na ci gaba da tururuwa domin shiga rundunar kare juyin juya halin ƙasar (IRGC) da kuma ƙungiyar Basij, domin kare ƙasar daga duk wani hari. Sun kuma nuna…
Read More