27
Mar
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci gwamnonin jihohi goma tare da shugabannin jam’iyya wajen tarbar Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zuwa jam’iyyar APC. An gudanar da wannan gagarumin taro ne a ranar Talata a filin kasuwanci na Trade Fair da ke Gusau, inda dubban magoya baya, ’yan Majalisar Dokoki, da mambobin Majalisar Zartarwa suka halarta domin shaida wannan lamari mai muhimmanci a siyasar jihar. Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa Mataimakin Shugaban ƙasar ya isa sabon filin jirgin saman Gusau na ƙasa da ƙasa, wanda…
