28
Mar
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke wani soja mai mukamin Staff Sergeant, Amoke Simon, bisa zargin aikata damfara ta kimanin Naira miliyan 114 da kuma yin ikirarin karya cewa ya taka rawa wajen kashe fitaccen shugaban masu garkuwa da mutane, Obioma Nwankwo wanda aka fi sani da “Osisikankwu.” Majiyoyin soja sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a filin jirgin sama na Fatakwal yayin da yake ƙoƙarin tserewa zuwa Abuja, bayan binciken da ake yi kan zarge-zarge da dama da suka haɗa da damfara. An ce haɗin gwiwar dakarun Brigade ta 14 da…
