ukarofi

12662 Posts
’Yan Nijeriya miliyan 141 za su faɗa ƙangin talauci a bana – Rahoto

’Yan Nijeriya miliyan 141 za su faɗa ƙangin talauci a bana – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 141 ne ake hasashen za su kasance cikin talauci a bana, a cewar wani rahoto da ya yi nazarin tattalin arzikin kasar a 2026. Rahoton, wanda cibiyar tattalin arziki ta PwC ta fitar mai taken: “Juya daidaiton tattalin arziki zuwa ci gaba mai dorewa” ya yi hasashen cewa matakin talauci zai kai kusan kaso 62 cikin 100 na al’umma a shekarar da ke dab da ta zaben 2027. Rahoton ya nuna cewa duk da sabbin manufofi da aka ɗauka don daidaita tattalin arziki, ƙarancin haɓakar kuɗin shiga na hakika da…
Read More
Za mu yi tankaɗe da rairaya a shugabanci domin gyara KASSOSA a zaɓe mai zuwa — Walin Gafasa

Za mu yi tankaɗe da rairaya a shugabanci domin gyara KASSOSA a zaɓe mai zuwa — Walin Gafasa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Daya daga cikin matasan ƙungiyar Kano State Science Schools Old Students Association (KASSOSA), Kwamared Awaisu Nasir Walin Gafasa, ya bayyana cewa akwai buƙatar sake fasalin shugabancin ƙungiyar domin tabbatar da ingantaccen shugabanci a zaɓe mai zuwa. Walin Gafasa ya yaba wa shugabancin ƙungiyar ƙarƙashin Alhaji Balarabe Nuhu Jallah bisa irin ci gaban da suka samar wa KASSOSA a matakin ƙasa, yana mai cewa mafi yawan masu muƙami a ƙungiyar sun nuna nagarta da kyakkyawar mu’amala. Sai dai ya ce akwai wasu kaɗan da ba su tafiya da tsarin shugabanci na gaskiya da adalci, abin da…
Read More
‘Kashe-kashe da garkuwa da mutane sun dawo a Katsina’

‘Kashe-kashe da garkuwa da mutane sun dawo a Katsina’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan bindiga a daren Litinin sun kai hari a kan wasu al’ummomi na ƙaramar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.  A cewar mazauna yankin, maharan sun kutsa Unguwar Alhaji Barau, Gidan Dan Mai-gizo da Gidan Hazo a gundumar Na’alma a ƙaramar hukumar, inda suka yi ta ɓarna tsawon sa’o’i. Shaidu sun ce ’yan bindigar sun kuma toshe hanyar Dayi-Na-Alma, inda suka ƙwace babura tare da karɓe wayoyi da kuɗin jama’a. Mazauna yankin sun bayyana cewa mutum uku aka…
Read More
Yara 469 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Kano

Yara 469 sun mutu saboda rashin abinci mai gina jiki a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aƙalla yara 469 ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki tsakanin watan Janairu zuwa Yuli, 2025, a Jihar Kano, yayin da kashi 51.9 cikin 100 na yara ke fama da rahsin na girma yadda ya kamata. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Farfesa Ruƙayya Aliyu Yusuf na Sashen Nazarin Harkokin Watsa Labarai, Jami’ar Bayero Kano (BUK), a lokacin da take gabatar da takarda mai taken: “Understanding the Basics of Behaɓioural Change: Towards Improɓing Malnutrition in Kano State” a wani taron horaswa ga ’yan jarida. Farfesa Ruƙayya ta ce rashin abinci mai…
Read More
Taimakon raunana ita ce aƙidar Kwankwaso — Dakta Nisa’i Gwadabe

Taimakon raunana ita ce aƙidar Kwankwaso — Dakta Nisa’i Gwadabe

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Tsohon Shugaban Sashen Kula da Tarihi kuma mataimakin darakta a Sashen Cigaban Karatu na Jami’ar Northwest, Dakta Nisa’i Muhammad Gwadabe, ya bayyana cewa taimakon raunana da marasa galihu ita ce ginshiƙin aƙidar Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Dakta Nisa’i, wanda kuma shi ne sakataren tsare-tsare, manufofi da dabarun tafiyar ƙungiyar Kwankwasiyya Scholars, ya bayyana hakan ne yayin taron ƙungiyar na ƙasa karo na farko da aka gudanar a Kano a makon da ya gabata. Ya ce taron ya ƙaddamar da masana 318 masu digiri na biyu da na uku, har da farfesoshi, tare da…
Read More
Matsalar Tsaro: Za a sake buɗe wasu makarantu a Neja

Matsalar Tsaro: Za a sake buɗe wasu makarantu a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa za ta sake buɗe makarantu ne a wasu ƙananan hukumomi huɗu kacal daga cikin ƙananan hukumomi 25 da ke faɗin jihar da aka rufe a dalilin matsalar tsaro. ƙananan hukumomin da aka amince za a buɗe makarantu a cikinsu sun haɗa da Bida, Suleja, Chanchaga, da kuma wasu sassan Bosso. Kwamishiniyar Ilimi ta Firamare a Jihar Neja, Dokta Hadiza Asabe Mohammed, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki gabanin buɗe makarantun. Ta ce daga cikin makarantun kwana 45 da ke…
Read More
‘Yan sanda sun ɗauke makeken bom ɗin da aka gani a jihar Neja

‘Yan sanda sun ɗauke makeken bom ɗin da aka gani a jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar 'yan sandan Nijeriya a jihar Neja ta kwance tare da ɗauke wani makeken bom da aka gani a dajin Zugurma da ke ƙaramar hukumar Mashegu. A wata tattaunawa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Mashegu, Umar Igade ya ce bayan samun kiran waya daga ƙauyen Zugurma, cewa an ga wani abu kamar bam a ƙasa "na kira DPO na wannan yanki, inda ya tura jami'an tsaro domin su duba gaskiyar al'amarin. "Bayan da suka isa wurin sun tabbatar da cewa bom ne. Bom ne mai girma, guda ɗaya." A baya-bayan nan an samu rahotanni…
Read More
Za a gudanar da maulidin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 40 a Katsina

Za a gudanar da maulidin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 40 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban babban kwamitin shirya maulidin Sheikh Hadi Balarabe ya tabbatar da haka ga manema labarai a babban ofishin ƙungiyar Munazzamatul Fitiyanul Islam a Katsina. Sheikh Hadi Balarabe ya bayyana cewa shine karo na uku da jihar Katsina ke karɓar wannan babban taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass. Sheikh Hadi Balarabe ya cigaba da cewa a bana za a fara gudanar da taron masana da ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa, wanda za a kwashe tsawon kwanaki biyar ana yin sa, wanda masana daga ƙasashen duniya za su samu halarta domin gabatar da maƙaloli da…
Read More
Gwamnatin Katsina ta raba wa jami’an tsaron gandun daji guda 70 babura

Gwamnatin Katsina ta raba wa jami’an tsaron gandun daji guda 70 babura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ma’aikatar muhalli ta Jihar Katsina ta gudanar da rabon baburan da kayan aiki ga jami’an tsaron daji guda 70,tare da gargaɗi da su guji sayar da baburan. A jawabinsa daraktan Kula da gandun daji, Alhaji Saminu Soli Jibia ya bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa jami’an tsaron daji kan ayyukansu na kare dazuzzuka da hana sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba. Sakatare na dindindin na ma’aikatar muhalli, Alhaji Lawal Suleiman Abdullahi, ya jaddada muhimmancin jajircewa da gaskiya a bakin aiki, tare da kira ga jami’an da su yi amfani da damar…
Read More
Joshua na tunanin bankwana da dambe bayan mummunan hatsari a Nijeriya

Joshua na tunanin bankwana da dambe bayan mummunan hatsari a Nijeriya

Fitaccen zakaran dambe na duniya, Anthony Joshua, na tunanin ja gefe daga harkar damben ƙwararru bayan tsira daga wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyyar rasuwar wasu muhimman mutane biyu a tawagarsa, inji iyalansa. Kawun Joshua, Adedamola Joshua, ya bayyana wa manema labarai cewa ɗan damben mai shekaru 36 ya riga ya sanar da iyalinsa a sirrance game da shawarar da yake tunanin ɗauka, biyo bayan hatsarin da ya auku makon jiya a Nijeriya. “Abu mafi muhimmanci shi ne ya ce ya bar dambe,” inji kawun nasa yayin wata ziyara da aka kai gidan iyali a Sagamu, jihar Ogun.…
Read More