Gwamnatin Katsina ta raba wa jami’an tsaron gandun daji guda 70 babura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ma’aikatar muhalli ta Jihar Katsina ta gudanar da rabon baburan da kayan aiki ga jami’an tsaron daji guda 70,tare da gargaɗi da su guji sayar da baburan.

A jawabinsa daraktan Kula da gandun daji, Alhaji Saminu Soli Jibia ya bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa jami’an tsaron daji kan ayyukansu na kare dazuzzuka da hana sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba.

Sakatare na dindindin na ma’aikatar muhalli, Alhaji Lawal Suleiman Abdullahi, ya jaddada muhimmancin jajircewa da gaskiya a bakin aiki, tare da kira ga jami’an da su yi amfani da damar da aka ba su yadda ya dace.

A nasa jawabin, Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, Hon. Hamza Suleiman Faskari, ya ja hankalin jami’an tsaron dajin da su yi amfani da babura da sauran kayan aikin da aka basu domin aikin gwamnati kaɗai. Ya yi gargadi mai ƙarfi cewa duk wanda aka samu yana amfani da kayan aikin ba bisa ƙa’ida ba ko sakaci da su, za a ɗauki matakin ladabtarwa a kansa bisa tanadin doka.

Ƙauran Katsina, Hakimin Rimi Alhaji Aminu Abdulkadir, ya yi takaitaccen jawabi inda ya yaba da wannan shiri, tare da ƙarfafa gwiwar jami’an da su kasance masu tsoron Allah da riƙon amana a duk inda aka tura su aiki.

Da yake magana a madadin jami’an tsaron, Muhammad Nuradeen, yayi godiya ga gwamnatin jihar Katsina da Ma’aikatar Muhalli bisa wannan tallafi da aka bai wa jami’an tsaron daji, yana mai tabbatar da cewa za su yi aikin su bisa gaskiya da amana.

By ukarofi