11
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa, Tarayyar Nijeriya tana bin ƙasashen Nijar, Togo da Benin bashin Naira biliyan 25 na hasken lantarki da aka samar musu a ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen. A cikin rahotonta na kwata na uku na 2025, wanda Blueprint Manhaja ta samu, Hukumar NERC ta bayyana cewa abokan hulɗa uku na ƙasashen waje sun karɓi jimillar kuɗin wutar lantarki na dala miliyan 18.69 daga hannun mai kula da kasuwar don samar da wutar lantarki a lokacin, amma sun biya dala miliyan 7.125 kacal, wanda ya…
