11
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Ministan Tsaro na Nijeriya , Mohammed Badaru Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sheƙa daga jam'iyyarsa ta APC mai mulkin ƙasar zuwa jam'iyyar hamayya ta ADC. A wata sanarwa da tsohon ministan ya sanya wa hannu da kansa, ya ce wannan zancen, labarin ƙanzon kurege ne, kuma wani yunƙuri ne kawai na ɓata masa suna, da kuma kassara harkar siyasarsa. A tattaunawarsa da BBC wani hadimin tsohon ministan, Kwamared Abba Malami, ya ce su wannan labari ya zo musu ne ma da mamaki: ''Na farko dai babu ƙanshin gaskiya…
