ukarofi

12662 Posts
Maraici da mutuwar aurena ne suka buɗe tunanina kan kafa gidauniya  – Mariya Durumin Iya 

Maraici da mutuwar aurena ne suka buɗe tunanina kan kafa gidauniya  – Mariya Durumin Iya 

"Mace na rayuwa ne ƙarƙashin kulawar wasu har ƙarshen rayuwarta" Daga AISHA ASAS  Rayuwar aure rai ne da ita tamkar dai yadda aka san ɗan adam da ruhinsa, yayin da mai shar'antawa Ya yi kira, ruhinsa ba zai ƙara ko sa'a ɗaya a jikin ba, zai fice yana mai amsa kiran mahallici. Idan kuwa ba shi ya yi kiran nasa ba, ko duniya za ta taru don ganin ta tsayar da numfashinsa ba za ta iya tsayar da shi ba. Haka ita ma rabuwar aure, daga auren har ranar ƙarewar sa rubatacce ne, idan ranar rabuwa ta zo, ko da…
Read More
Cibiyar horar da matasa sana’o’i ta gyara motocin gwamnatin Katsina guda tara

Cibiyar horar da matasa sana’o’i ta gyara motocin gwamnatin Katsina guda tara

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sashen gyaran motoci, watau Central Mechanical Workshop da ke cibiyar KYCV mallakan gwamnatin jihar Katsina ta kammala gyara da sabunta motocin gwamnati guda tara, wanda hakan na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da kadarorin gwamnati da rage asarar kuɗi. Shugaban cibiyar, Injiniya Kabir Abdullahi Ƙofar Soro, ya bayyana ga manema labarai ya ce nasarar aikin ta ƙara tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na inganta amfani da kadarorin gwamnati cikin tsari mai inganci da tanadin kudi. Injiniya Ƙofar Soro ya bayyana cewa motocin Toyota Hilux guda biyu, an yi musu cikakken gyara da sabuntawa tare…
Read More
Yaƙi da raguwar haihuwa: Chana ta kakaɓa haraji kan kondon da magungunan hana ɗaukar ciki 

Yaƙi da raguwar haihuwa: Chana ta kakaɓa haraji kan kondon da magungunan hana ɗaukar ciki 

A wani sabon mataki da ya ɗauki hankulan duniya, gwamnatin ƙasar Chana ta kakaɓa harajin kashi 13 cikin 100 kan kayayyakin hana ɗaukar ciki kamar kondon da kwayoyin hana ɗaukar ciki, a wani yunƙuri na daƙile raguwar haihuwa da ke ƙara tsananta a ƙasar. Sabon tsarin, wanda ya fara aiki tun 1 ga Janairu, ya kawo ƙarshen rangwamen haraji da aka shafe kusan shekaru 30 ana amfani da shi, tun daga shekarar 1994, lokacin da Chana ke tsaurara manufofinta na rage yawan jama’a ta hanyar tsarin haihuwa ɗaya. Yanzu haka, duk wani magani ko wata hanya ta hana ɗaukar ciki…
Read More
Kama Shugaban Venezuela: Rasha da Iran sun yi Allah-wadai, EU Ta nemi a mutunta dokokin ƙasa da ƙasa

Kama Shugaban Venezuela: Rasha da Iran sun yi Allah-wadai, EU Ta nemi a mutunta dokokin ƙasa da ƙasa

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta kama Shugaban Venezuela, Nicolás Maduro, a wani mataki da ya ƙara tayar da ƙura a siyasar duniya, musamman a yankin Latin Amurka. Hukumomin Amurka sun ce an kai Maduro New York domin fuskantar shari’a a kotun tarayya bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi da ta’addanci. Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da kama Maduro, inda ya ce an gudanar da aikin ne cikin tsari mai tsauri, ba tare da asarar rayuka ba. A cewarsa, jami’an tsaro sun fuskanci ƙalubale masu yawa kafin samun nasarar kama shugaban. A cewar Ma’aikatar Shari’ar Amurka, tuhumar da ake yi…
Read More
Duk da Allah-wadai, Chana na kallon harin Amurka a Venezuela a matsayin dama a rikicin ta da Taiwan 

Duk da Allah-wadai, Chana na kallon harin Amurka a Venezuela a matsayin dama a rikicin ta da Taiwan 

Masana harkokin tsaro da siyasar duniya sun bayyana cewa matakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na kai farmaki a Venezuela tare da kama Shugaba Nicolás Maduro na iya zama babban darasi kuma wata dama ga ƙasar Chana, duk da cewa Beijing ta yi kakkausar suka kan harin. A cewar masana, irin wannan mataki da Amurka ta ɗauka zai iya ƙarfafa Chana ta sake duba dabarunta na tsoma baki ta ƙarfi a yankinta, musamman game da Taiwan da kuma Tekun Kudancin Chana, inda ake ta fama da rikice-rikicen ikon mallaka. Rahotanni sun nuna cewa duk da furucin Chana a…
Read More
 Travis Pastrana: Mutumin da ya mayar da jikinsa gidan ƙarfe

 Travis Pastrana: Mutumin da ya mayar da jikinsa gidan ƙarfe

Idan aka ce mutum ya karya ƙasusuwan jikinsa har guda 90, kai ya bugu fiye da sau 25, sannan kusan kashi 30 cikin 100 na ƙasusuwansa aka maye gurbinsu da ƙarfe da ƙusoshi, da yawa za su ɗauka almara ce ko labarin fim. Amma wannan ba labarin wasan kwaikwayo ba ne. Wannan shi ne ainihin labarin rayuwar Travis Pastrana, hatsabibin ɗan kasada ɗan Amurka wanda ya shahara wajen sayar da ransa domin burge duniya. Hoton ɗ-ray ɗinsa da ke yawo a kafafen sada zumunta ya gigita mutane. Jiki da ya kamata ya kasance ƙashi da nama, ya koma haɗin ƙarfe…
Read More
An rufe rassan bankuna 229 sakamakon yawan masu PoS – CBN

An rufe rassan bankuna 229 sakamakon yawan masu PoS – CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bangaren bankuna a Nijeriya na fuskantar gagarumin sauyi a tsarinsa, yayin da ƙaruwar amfani na’urorin PoS ke ci gaba da rage muhimmancin bankuna.  Sabbin bayanai daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa rassan bankuna 229 sun rufe a faɗin ƙasar nan cikin shekara guda, lamarin da ke nuna sauyin ɗabi’ar jama’a zuwa hanyoyin biyan kuɗi ta lantarki domin mu’amalolinsu na yau da kullum. Bisa bayanan da CBN ya fitar a cikin Financial Sector Statistical Bulletin na shekarar 2024, yawan rassan bankunan ajiya da cibiyoyin kuɗi ya ragu daga 5,373 a 2023 zuwa 5,144 a 2024.…
Read More
Fiye da kashi 93 na tsabar kuɗi suna hannun jama’a – CBN

Fiye da kashi 93 na tsabar kuɗi suna hannun jama’a – CBN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sabbin alƙaluman kuɗi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya ci gaba da tafiya ne bisa dogaro da tsabar kuɗi a duk tsawon shekarar 2025, inda mafi yawan kuɗin da ke yawo a ƙasar ke ci gaba da kasancewa a waje da tsarin bankuna. Bincike kan bayanan ya nuna cewa zuwa watan Nuwamba 2025, kuɗin da ke waje da bankuna ya kai naira tiriliyan 4.91 daga cikin jimillar naira tiriliyan 5.26 da ke yawo a ƙasar. Wannan na nufin kusan kashi 93.35 cikin 100 na dukkan kuɗin tsabar da…
Read More
CBN ya ja kunnen bankunan kan takura kwastomomi sakamakon sabon sharaɗin jari

CBN ya ja kunnen bankunan kan takura kwastomomi sakamakon sabon sharaɗin jari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gargaɗin cewa tsarin ƙara jarin bankuna da ake aiwatarwa a halin yanzu na iya jawo cunkoson masu zuba jari a kasuwar hannun jari, lamarin da ka iya kashe jikin masu saka jari tare da rage damar samun kuɗaɗe ga kamfanonin da ba na banki ba. Wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin rahoton Hasashen Tattalin Arziki na 2026 da Babban Bankin ya fitar, a daidai lokacin da bankunan Nijeriya ke hanzarta neman cika sabon sharuɗɗan mafi ƙarancin jarin aiki kafin wa’adin watan Maris na shekarar 2026. A cewar CBN, wa’adin…
Read More
Kamfanonin lantarki sun karɓi biliyan N570.25 daga bashin biliyan N706.6 a ƙarshen 2025 – NERC

Kamfanonin lantarki sun karɓi biliyan N570.25 daga bashin biliyan N706.6 a ƙarshen 2025 – NERC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun samu kuɗin shiga na Naira biliyan N570.25 daga cikin biliyan N706.61 da suka caji kwastomomi a ƙarshen shekarar 2025. Wannan, a cewar rahoton hukumar, na nuna ingancin tara kuɗi kashi 80.70 cikin 100, lamarin da ke nuna ƙarin kashi 4.63 idan aka kwatanta da tsakiyar shekarar, wanda ya tsaya a kashi 76.07 cikin 100. Rahoton ƙarshen shekarar 2025 da NERC ta fitar a ranar Talata ya nuna cewa duk da samun wannan kuɗin shiga, DisCos sun biya kuɗi biliyan…
Read More