ukarofi

12663 Posts
Naira ta ƙara farfaɗo a kasuwar canji

Naira ta ƙara farfaɗo a kasuwar canji

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD Darajar Naira ta rufe mako cikin ƙarfi a ranar Juma’a, bayan ta samu ƙarin Naira 1.65 kan dalar Amurka a kasuwar canji ta hukuma, inda aka sayar da ita kan N1,454.41. Bayanan da Babban Bankin Nijeriya ya fitar ta shafinsa na hukuma sun nuna cewa wannan sauyin ya wakilci ƙarin kashi 0.11 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar Alhamis, lokacin da Naira ta tsaya a kan N1,456.06 a kowace dala. A farkon makon cinikayyar, Naira ta fuskanci ɗan raguwar daraja, inda aka samu asara kaɗan-kazan a tsawon makon. A ranar Laraba, an sayar da kuɗin…
Read More
CBN ya soke lasisin bankunan Aso da Union Homes

CBN ya soke lasisin bankunan Aso da Union Homes

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sanar da gaggauta soke lasin gudanar da hada-hadar bayar da rancen gina gidaje da jingina na 'Aso Saɓings and Loans Plc' da kuma 'Union Homes Saɓings and Loans Plc'. Wannan mataki dai wani yunƙuri ne na ƙarfafa sashen Bankunan Gidaje da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin banki. Kamar yadda wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta CBN mai riƙo, Hajiya Hakama Ali, ta wallafa a shafin ɗ na bankin a ranar Talata, CBN ya bayyana cewa bankunan sun karya wasu tanade-tanade na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA)…
Read More
Gobara ta ƙone shaguna 48 a kasuwar Elegushi ta Legas

Gobara ta ƙone shaguna 48 a kasuwar Elegushi ta Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata gobara da ta tashi da asubahin wayewar gari ta lalata aƙalla shaguna 48 a kasuwar Elegushi da ke Lekki, a jihar Legas. Babban Sakataren na Hukumar Agajin Gaghawa ta Jihar Legas (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa misalin ƙarfe biyu na dare, inda nan take ta tura jami’anta zuwa wurin da wutar ta riga ta kama kasuwar baki ɗaya. A cewarsa, jami’an agajin gaggawa sun yi aiki cikin sauri tare da haɗa kai da sauran…
Read More
EFCC ta kama bokaye da dalar jabu ta miliyan 3.4

EFCC ta kama bokaye da dalar jabu ta miliyan 3.4

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC) ta sanar da kama wasu mutane biyar da ake zargi ‘bokaye’ ne, tare da kwato manyan kuɗaɗen waje na jabu da suka kai dalar Amurka 3,430,000 da kuma Yuro 280,000, a jihohin Osun da Legas. A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, an ce jami’an sashen Ibadan na EFCC sun kama mutanen ne a ranakun 7 da 8 ga Disamba, 2025, bayan bin diddigi da tattara bayanan sirri kan ayyukansu. Binciken farko ya nuna…
Read More
Sarki ya kwana a motarsa bayan ambaliya ta lalata masa fada

Sarki ya kwana a motarsa bayan ambaliya ta lalata masa fada

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya Wani basaaraken gargajiya mai suna Amos Poubinafa wato sarkin wani gari da ake kira Tungbbo da ke ƙaramar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa a yanzu haka yana kwanciya ne a cikin motarsa sakamakon kora da wata mummunar ambaliya ta yi masa daga fadar sa. Wakilin mu da ya ziyarci sarkin a cikin sabuwar fadar na sa dake cikin motarsa, ya samu ganawa da shi akan bala'in da ya rutsa da shi inda ya bayyana alhininsa cewa "Ka ga kamar yadda kake gani, yau kimanin makonni biyu kenan da nake kwanciya da sauran harkokin rayuwata…
Read More
Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya nemi ƙarin ɗorewar haɗin kai a Legas

Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya nemi ƙarin ɗorewar haɗin kai a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban ƙungiyar ’Yan Arewa na ƙaramar Hukumar Epe a Jihar Legas, Alhaji Ummaru Gwamna Epe, ya shawarci shugabanni da mambobin kungiyar a faɗin jihar da su ƙara haɗa kai da zaman tafiya a tsari ɗaya domin ƙarfafa martabar al’ummar Arewa a Legas. Alhaji Gwamna Epe ya yi wannan kira ne a garin Epe yayin wani taron tattaunawa da ya gudanar tare da wasu jiga-jigan ƙungiyar, wanda yake kanana shugabanci ke gudanarwa a ƙarshen kowane mako domin nazari kan matsaloli da kuma ɗaukar matakan magance su. Ya bayyana cewa, hadin kai da kyakkyawar fahimta ita ce…
Read More
Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta nemi a riƙa mutunta shari’a a Nijeriya

Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta nemi a riƙa mutunta shari’a a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Kare Haƙƙin Bil'adama ta Duniya (IHRC-RFT) a Nijeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun ƙaruwar amfani da umarnin kotu wajen ƙauce wa shari’a bayan aikata laifuka ko tauye haƙƙin mutane inda take neman a riƙa mutunta shari'a a ƙasar. ƙungiyar ta lura cewa amfani da umarnin kotu a Nijeriya wajen ba bisa ƙa'ida ba na neman ya zama ruwan dare wanda ke hana jami’an tsaro daga kama ko binciken masu aikata laifi. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan ƙasa ta ƙungiyar Amb. Abdullahi Bakoji Adamu ya fitar. Sanarwar ta ce,…
Read More
NRG ta ziyarci JNI da CAN a ƙoƙarin ƙarfafa fahimtar juna a Arewa

NRG ta ziyarci JNI da CAN a ƙoƙarin ƙarfafa fahimtar juna a Arewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu manyan shugabanni daga Arewa, ciki har da tsohon kakakin NEF, Dr Hakeem Baba Ahmed, sun kai ziyara hedikwatar ƙungiyar Kiristocin Nijeriya ta jihohi 19 na Arewa da kuma Jama’atu Nasril Islam. Ziyarar ta kasance ƙarƙashin wata sabuwar ƙungiya da aka kafa mai suna ƙungiyar Haɗin Kan Arewa 'Northern Reconciliation Group', wacce ta ƙunshi ‘yan Arewa Musulmi da Kiristoci da ke da manufa ɗaya ta ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai. Manufar ziyarar, a cewar jagororin tawagar, ita ce buɗe sabon babi na tattaunawa da fahimtar juna, domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka daɗe suna addabar…
Read More
RAI ta maka tsohon shugaban NMDPRA a kotu tana neman a gudanar da bincike a kansa

RAI ta maka tsohon shugaban NMDPRA a kotu tana neman a gudanar da bincike a kansa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ƙungiya mai zaman kanta suna 'Rights for All International' RAI ta shigar da ƙara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman a yi bincike game da rikicin Aliko Dangote da Farouk Ahmed. A ƙarar da RAI ta shigar, lauyan ƙungiyar Okere Nnamdi ya buƙaci kotu ta ayyana cewa Farouk Ahmed ya aikata laifin karɓar kuɗi daga hannun wasu ba bisa ƙa'ida ba. Idan dai ba a manta ba, Alhaji Aliko Dangote na zargin Farouk Ahmed, tsohon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Tsakiya da ƙasa (NMDPRA), bisa zargin rashin gaskiya da…
Read More
Dalilan da ya sa manyan ‘yan siyasa a jam’iyyun adawa ke dawowa APC – Fadar Shugaban ƙasa

Dalilan da ya sa manyan ‘yan siyasa a jam’iyyun adawa ke dawowa APC – Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da iƙirarin da wasu shugabannin jam’iyyar adawa a Nijeriya ke yi cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na yi wa wanzuwar jam’iyyun siyasa barazana da amfani da yaƙi da cin hancinta wajen cimma burinta na siyasa. ‘Yan jam’iyyar adawar da suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, da shugaban jam’iyyar ADC, David Mark; su ne suka yi wannan iƙirari a ranar Lahadi. Sun yi zargin cewa yawan sauyin sheƙa zuwa APC na zuwa sakamakon matsin lamba da…
Read More