ukarofi

12663 Posts
Zakka da waƙafi na taimakawa wajen rage kyashi, hassada da talauci – Dikko Radda

Zakka da waƙafi na taimakawa wajen rage kyashi, hassada da talauci – Dikko Radda

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar tawagar gamayyar ƙungiyoyin Zakka da Waƙafi na Najeriya (AZAWON), wadda ta kawo masa ziyarar aiki a fadar gwamnatin jihar. Ya jaddada cewa Zakka da Waƙafi ba wai kawai ibada ba ce, illa wata muhimmiyar hanya ta rage raɗaɗin talauci, ƙarfafa jin ƙai, tsaftace zuciya, da samar da adalci a cikin al’umma. A cewarsa, yadda ake tara da rarraba zakka cikin tsari yana taimakawa wajen inganta tsaro, domin yana rage yawan matasa marasa aikin yi, tare da samar da damar dogaro da…
Read More
Tsakanin tausayi da kundin tsarin mulki: Dalilin da ya sa Kotun Koli ta ƙi yafiyar Tinubu ga Maryam Sanda

Tsakanin tausayi da kundin tsarin mulki: Dalilin da ya sa Kotun Koli ta ƙi yafiyar Tinubu ga Maryam Sanda

Daga AISHA ASAS  Doka mai tsauri ce ke hana aikata laifi, ba tausayi ba - Amina Sidi Aƙibu  Shekaru da dama, shari’ar Maryam Sanda ta kasance a tsakiyar muhawara mai zafi tsakanin laifi, iko, tausayi da adalci a zuciyar al’ummar Najeriya. A ranar Juma’a, wannan doguwar muhawara ta ɗauki sabon salo bayan Kotun Koli ta Najeriya ta yanke hukuncin da ake ganin shi ne na ƙarshe a ɗaya daga cikin shari’un kisan kai mafi ɗaukar hankali a tarihin ƙasar nan. Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa Maryam Sanda…
Read More
Hukumar NFC a shirye take ta bada goyon baya ga masu harkar fim – Ali Nuhu 

Hukumar NFC a shirye take ta bada goyon baya ga masu harkar fim – Ali Nuhu 

Daga MUKHTAR YAKUBU  Shugaban Hukumar kula da bunƙasa harkokin fim ta Nigerian Film Corporation' Ali Nuhu, ya bayyana ƙudirin hukumar na bada goyon bayanta ga dukan ayyukan da suka shafi harkar fim a ƙasar nan. Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron horar da marubutan labarin fim da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata a ɗakin taro na Kannywood TV dake titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano. Tun da farko ya bayyana muhimmancin rubutun labari wanda ya kasance kashin bayan duk wani fim da za a shirya. Inda…
Read More
A bikin Ranar Jammaje na wannan shekarar za a  kalli sabon fim ɗin mu – Kabiru Jammaje 

A bikin Ranar Jammaje na wannan shekarar za a  kalli sabon fim ɗin mu – Kabiru Jammaje 

Daga MUKHTAR YAKUBU  A yanzu haka dai shirye-shirye suna fara kankama na bikin ranar Jammaje ta wannan shekarar ta 2025 wanda za a gudanar a ranar 30 ga Disamba a cikin sabuwar Jami'ar Bayero dake Kano. A wata sanarwa da kwamitin shirya taron ya fitar ta bayyana cewa taron na bana zai kasance na daban ne domin baya ga jawabai da za a saurara daga bakin manyan malamai, to kuma a ranar ne za a haska sabon fim ɗin kamfanin Jammaje Production mai suna 'Jamila Jammaje'. Haka nan a wani ɓangare na gudanar da taron za a yi bajekolin litattafai…
Read More
Turanci da boko ne ke hana ‘yan Kannywood shiga KILAF AWARD – Ahmad Sarari

Turanci da boko ne ke hana ‘yan Kannywood shiga KILAF AWARD – Ahmad Sarari

Daga MUKHTAR YAKUBU An bayyana tsarin boko da kuma Turanci da yake cikin gudanar da bikin' 'Kano Indigenous Languages Afrka Film Market and Festival' (KILAF AWARD) da cewar shi ne yake hana shigar 'yan Kannywood tsarin wanda mutane suke ganin 'yan fim ɗin Kannywood ba sa shiga ana damawa da su.Tsohon shugaban ƙungiyar kwararru ta masu shirya fim ta ƙasa MOPPAN Dakta Ahmad Muhammad Sarari ne ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu dangane da taron KILAF AWARD na wannan shekarar da ya gudana a watan  Nuwambar da ya gabata. Dakta Ahmad Sarari ya fara ne da…
Read More
’Yan sanda sun kama magidanci bisa zargin dukan matarsa har lahira

’Yan sanda sun kama magidanci bisa zargin dukan matarsa har lahira

Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta tabbatar da cafke wani mutum mai shekaru 58, ɓitalis Nwoko, ɗan asalin Umuagba da ke ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise, bisa zargin dukan matarsa, Uloma, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta. Mai magana da yawun rundunar, DSP Henry Okoye, ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga sashen Ahiazu Mbaise ne suka kama wanda ake zargin, bayan ’yar uwar mamaciyar ta kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda. A cewar rahoton, ana zargin Nwoko da yi wa matarsa duka yayin wata saɓani na cikin gida. Okoye ya ce binciken farko ya nuna cewa rikicin da ya faru…
Read More
Matashi ya halaka mutum uku yayin Sallar Asuba a Abuja

Matashi ya halaka mutum uku yayin Sallar Asuba a Abuja

Wani matashi ya kashe mutum uku a masallaci a yayin da suke jiran Sallar Asuba a yankin Gwarimpa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Matashin ya daɓa wa mai kula da masallacin da wasu mutum biyu wuƙa har lahira a yayin da suke jiran sallar ne a masallacin da ke Kado Bimko a shiyyar First Aɓenue da ke shararriyar unguwar. Wani ganau, Muhammad Auwal, mai shago a kusa da masallacin, ya ce wanda aka fara kashewa, Alhaji Wanzam, dattijo ne da ke sana’ar wanzanci a kusa da masallacin. “Alhaji Wanzam ya kan zo masallaci tun ƙarfe 4 na Asuba daga…
Read More
Yarjejeniya da Faransa ba za ta raunana tsarin harajin Nijeriya ba – FIRS

Yarjejeniya da Faransa ba za ta raunana tsarin harajin Nijeriya ba – FIRS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya (FIRS) ta yi watsi da rahotannin da ke tada ruɗani game da yarjejeniyar haɗin gwiwa (MoU) da ta rattaba hannu da Hukumar Kula da Kuɗin Jama’a ta Faransa (DGFiP), tana mai tabbatar da cewa yarjejeniyar ba za ta yi barazana ga ikon tattalin arziki ko tsaron ƙasa na Nijeriya ba. A wara wasiƙa da suka aike zuwa Gwamnatin Tarayya, Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, ƙungiyar Dattawa Arewa (NEF) ta bayyana yarjejeniyar a matsayin haɗari ga tsarin bayanan haraji na ƙasa, tana mai nuna damuwa cewa za a iya fallasa muhimman…
Read More
Babu mai zuba jari da zai sayi matatun man Nijeriya, inji Dangote

Babu mai zuba jari da zai sayi matatun man Nijeriya, inji Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa yanayin kasuwanci da tsarin doka a Nijeriya ba su dace ba ta yadda ba wani mai zuba jari da zai nuna sha’awar sayen matatun man fetur da Kamfanin NNPC ke da su, ko da gwamnati ta fito da su kasuwa. Dangote ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya yi a Legas ranar Lahadi, inda ya ce ko a yau NNPC ta yanke shawarar sayar da matatun man, babu wanda zai zo ya saya, saboda yanayin aiki da tsare-tsaren da ke gudana a…
Read More
NYSC ta faɗaɗa shirin koyon sana’o’i ga matasa

NYSC ta faɗaɗa shirin koyon sana’o’i ga matasa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Masu Yi Wa ƙasa Hidima ta Nijeriya (NYSC) ta sanar da wani gagarumin sauyi a shirin ta na Koyon Sana’o’i da Harkokin Kasuwanci (SAED), inda ta fito da sabuwar manhaja guda ɗaya da aka daidaita, wadda yanzu ta ƙunshi sabbin dabaru na zamani kamar ilimin ƙirƙirarriyar basira ta AI da ƙirƙirar manhajojin waya, domin ƙarfafa damar aikin yi da kasuwanci ga matasan Nijeriya. Babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki na SAED karo na biyu na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja.…
Read More