ukarofi

12663 Posts
2027: El-Rufai ya ƙaryata zargin mara wa shugabancin Nijeriya ya cigaba da zama a Kudu

2027: El-Rufai ya ƙaryata zargin mara wa shugabancin Nijeriya ya cigaba da zama a Kudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ƙaryata wani rahoto da ke iƙirarin cewa ya ce lokaci ya yi da yankin Kudu zai fitar da Shugaban ƙasa a shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, yana mai cewa bai taɓa yin irin wannan furuci ba a cikin jawaban da ya gabatar, hirarraki ko kuma rubuce-rubucensa a kafafen sada zumunta. Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da editoci da su cika nauyin da ya rataya a wuyansu, tare da gujewa yaɗa labaran bogi. El-Rufai,…
Read More
Yaƙi da cin hanci ba lamari ne na siyasa ba — Fadar Shugaban ƙasa

Yaƙi da cin hanci ba lamari ne na siyasa ba — Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Fadar Shugaban ƙasa ta yi watsi da zargin da wasu ‘yan adawa suka yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a matsayin makamin siyasa, tana mai cewa hukumar mai zaman kanta ce da ke aiki bisa tanadin doka. A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara ta Musamman kan labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Lahadi, fadar ta ce shugaba ƙasa ba ya bayar da umarni ga kowace hukumar yaƙi da cin hanci kan wanda za a bincika ko a gurfanar.…
Read More
Gwamnatin Filato ta ba masu Keke Napep tallafin Naira miliyan huɗu

Gwamnatin Filato ta ba masu Keke Napep tallafin Naira miliyan huɗu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Gwamnatin Jihar Filato ta bai wa masu gudanar da sana'ar tuƙin babur mai ƙafa uku, da aka fi sani da Keke Napep, tallafin Naira Miliyan huɗu, ƙarƙashin wata ƙungiyar masu taimakawa matuƙa babura ta United People Association of Keke Napep Riders, domin ƙara taimaka musu su samu sauƙin gudanar da sana'arsu. Jagoran ƙungiyar mai kula da harkokin tallafawa masu baburan, Malam Anas Abubakar Maihali shi ne ya sanar da haka a yayin wani taro da ƙungiyar ta kira, don raba wa wasu masu Keken da suka samu nasara da bashin Naira dubu ɗari, wanda…
Read More
Shirin FG, IFAD da VCDP na cigaba da bunƙasa harkokin noma – Manoman Nasarawa

Shirin FG, IFAD da VCDP na cigaba da bunƙasa harkokin noma – Manoman Nasarawa

DAGA JOHN D. WADA a Lafiya Manoma a Jihar Nasarawa sunce a yanzu haka suna sa ran samun girbi mai matuƙar amfani saboda gwamnatin Nasarawa ta ce za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen din din din na shirin nan na musamman da aka ƙirƙiro don bunƙasar ayyukan noma a jihar dama ƙasa baki ɗaya wato FG/IFAD-VCDP a turance har bayan shekarar badi ta 2026 ma don cigaba da bunƙasar harkokin noma a jihar baki ɗaya. Manoman sun bayyana haka ne a wajen wani taron kwana ɗaya na ƙara wa juna sani da aka shirya wa masu ruwa da…
Read More
Neja: Iyaye sun roƙi gwamnati ta ceto ’ya’yansu kafin Kirsimeti

Neja: Iyaye sun roƙi gwamnati ta ceto ’ya’yansu kafin Kirsimeti

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Iyaye da ‘yan uwan ɗaliban makarantar Katolika da aka sace a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar Neja da su gaggauta ceto sauran ‘ya’yansu da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane. Binciken da aka gudanar ya nuna cewa yaran sun shafe makonni a daji suna rayuwa cikin mawuyacin hali, inda ake ba su tuwon gero da miyan kuka sau ɗaya kacal a rana, tare da shan ruwa mai datti. Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Nuwamba 2025, lokacin da aka sace ɗalibai 303…
Read More
Yadda shugaban CAC ya mallaki gidajen miliyan N700 cikin shekara biyu — Rahoto

Yadda shugaban CAC ya mallaki gidajen miliyan N700 cikin shekara biyu — Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahoton bincike da kafar yaɗa labarai ta SaharaReporters ta wallafa ya tona zargin yadda Shugaban Hukumar Rajistar Kamfanoni ta ƙasa (CAC), Ishaƙ Hussaini Magaji (SAN), ya mallaki dukiya mai yawa da ta haɗa da gidajen alfarma guda biyu a birnin Abuja, duk kuwa da cewa albashinsa na wata bai wuce naira dubu 583 ba. Majiyoyi da dama sun bayyana cewa Magaji, cikin ƙasa da shekaru biyu da karɓar muƙamin sa a shekarar 2023, ya sayi gidaje guda biyu a unguwar Jahi, kowanne na kusan Naira miliyan 350. Rahoton ya ƙara da cewa, kayan ɗaki da na’urorin…
Read More
’Yan sanda na yunƙurin fara kama masu gilashin mota mai duhu

’Yan sanda na yunƙurin fara kama masu gilashin mota mai duhu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan sandan Nijeriya sun sanar da cewa za su ci gaba da tilasta bin dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu ko kuma su ci gaba da kame daga 2 ga Janairu 2026, abin da ya janyo suka daga ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), wadda ta bayyana matakin a matsayin saɓa wa hukuncin kotu da kuma tauye doka. Wannan sanarwa ta fito ne daga CSP Benjamin Hundeyin, jami’in hulɗa da jama’a na hukumar 'yan Sanda, a ranar 15 ga Disamba 2025. NBA ta bayyana cewa matakin ’yan sandan ya saɓa wa hukuncin da kotu ta…
Read More
Mun ƙwato naira biliyan 37.44 da Dala miliyan 2.35 a 2025 – ICPC

Mun ƙwato naira biliyan 37.44 da Dala miliyan 2.35 a 2025 – ICPC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta sanar da cewa ta samu nasarar ƙwato kadarori da kuɗaɗe da suka kai naira biliyan 37.44 da kuma dalar Amurka miliyan 2.353 a cikin shekarar 2025, adadin da ake ganin yana daga cikin mafi girma da hukumar ta taɓa cimmawa a shekara guda. Shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron ƙarshen shekara na ICPC, wanda ya haɗa da bankwana ga ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma bikin karrama ma’aikatan da suka nuna kwazo a aiki.…
Read More
NNPC ya ƙaddamar da bincike bayan fashewar bututun gas na Escravos–Legas

NNPC ya ƙaddamar da bincike bayan fashewar bututun gas na Escravos–Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An shiga fargaba a sassan ƙasar nan bayan wata mummunar fashewa da ta afku a kan bututun iskar gas na Escravos–Legas, wanda ke daga cikin muhimman ginshiƙan tsarin samar da lantarki a Nijeriya. Kamfanin NNPC ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a daren Juma’a, inda ya bayyana cewa fashewar ta janyo katsewar iskar gas tare da tayar da gagarumin matakin gaggawa domin daƙile illar da ka iya biyo baya. A cewar kamfanin, fashewar ta faru ne a kusa da yankin Tebijor, Okpele da Ikpopo da ke yankin Kudu maso Yammacin Warri a Jihar…
Read More
Amurka da Nijeriya na dab da cimma yarjejeniyar tsaro don yaƙar Boko Haram da ISIS 

Amurka da Nijeriya na dab da cimma yarjejeniyar tsaro don yaƙar Boko Haram da ISIS 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya ce Amurka da Nijeriya na dab da cimma matsaya kan wani tsarin tsaro na dabaru da nufin yaƙar Boko Haram da ISIS a Nijeriya. Moore, wanda ya kai ziyara Nijeriya tare da wasu ’yan majalisar Amurka, ya bayyana cewa sun yi tattaunawa masu kyau da gwamnatin Nijeriya kan batutuwan tsaro. Ya ce ziyarar ta ba shi damar ganawa da wasu daga cikin waɗanda ta’addanci ya shafa, inda ya ce abin da ya gani ya girgiza zuciya. Dan majalisar ya kuma ce zai miƙa rahoto ga Shugaban Amurka,…
Read More