20
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Kuɗi Wale Edun, ya bayyana a ranar Talata cewa Gwamnatin Tarayya ta yi asarar kuɗaɗen shiga mai yawa a shekarar kuɗi ta 2025. Ya ce duk da cewa gwamnati ta yi hasashen samun Naira tiriliyan 40.8 a wannan shekara, abin da ta samu gaba ɗaya bai wuce Naira tiriliyan 10.7 ba. Edun ya yi wannan bayani ne a gaban kwamitocin Majalisar Wakilai kan Kuɗi da Tsare-tsaren ƙasa yayin zaman tattaunawa kan Matsakaicin Tsarin Kasafin Kuɗi (2026–2028). Ya tuna cewa gwamnati ta yi hasashen samun Naira tiriliyan 40.8 a 2025 domin tallafawa kasafin kuɗin…
