ukarofi

12663 Posts
Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon Shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-ɓaci a kowace jiha

Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon Shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-ɓaci a kowace jiha

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kotun ƙoli ta Nijeriya ta tabbatar da ikon Shugaban ƙasa a ƙarƙashin kundin tsarin mulki na ayyana dokar ta-ɓaci a kowace jiha da ke fuskantar taɓarɓarewar tsaro ko barazanar faɗawa cikin rikice-rikice. Hukuncin, wanda aka yanke da rinjayen Alƙalai 6–1, ya biyo bayan ƙarar da Jihar Adamawa da wasu jihohi 10 da PDP ke mulki suka shigar. Masu ƙarar sun ƙalubalanci ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas, wadda ta haɗa da dakatar da zaɓaɓɓun jami’an jihar na tsawon watanni shida. A hukuncinta, kotun koli ta yi watsi da…
Read More
Ganduje ya janye shirin kafa ‘sabuwar Hisbah’ a Kano

Ganduje ya janye shirin kafa ‘sabuwar Hisbah’ a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya dakatar da shirinsa na kafa rundunar Hisbah mai zaman kanta a jihar. Ganduje ya dakatar da shirin nasa ne bayan ce-ce-ku-ce da hakan ya haifar da kuma haramcin da gwamnatin jihar ta sanya kan lamarin. A cikin wata sanarwa da jigo a Jam’iyyar APC, Baffa Babba Dan-Agundi, ya fitar a madadin Gandujen, ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawa da Gwamnatin Kano, da hukumar tsaro ta DSS, domin tabbatar da zaman lafiya a jihar. A kwanakin baya, Ganduje, wanda shi ne tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, ya…
Read More
CDD ta horar da ‘yan jarida kan sanin makamar aiki a Katsina

CDD ta horar da ‘yan jarida kan sanin makamar aiki a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan jarida fiye da 40 suka halarci taron ƙara wa juna sani kan inganta samo tare da aikawa da labarai wanda cibiyar raya dimokuraɗiyya ta ƙasashen Afrika ta Yamma ta shirya a Katsina. 'Yan jaridun da suka halarci horas wa sun haɗa da na kafofin yaɗa labarai na gida Najeriya da ƙasashen waje da gidajen rediyo da talabijin da kuma masu aikawa da labarai ta yanar gizo. Horan yafi mai da hankali wajan tace da tabbatar da sahihancin labari kafin amfani da shi. Haka kuma an tabo illar rubuta labarai na bogi da abinda ka…
Read More
Vendors a Katsina sunyi kira ga gwamna Raɗɗa ya kawo masu ɗauki daga durƙushewa

Vendors a Katsina sunyi kira ga gwamna Raɗɗa ya kawo masu ɗauki daga durƙushewa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Malam Muhammad Rabi'u shugaban masu sana'ar sayar da jaridu ta ƙasa (Vendors )reshen jihar Katsina ya yi wannan kira a wata takardar sanarwa da ya fitar. Ya ce ƙungiyar ta fi shekara 30 da kafuwa amma basu taɓa samun tallafi daga gwamnatin jihar ba. Malam Rabi'u ya bayyana cewa da kafuwar ƙungiyar,ta na da mambobi fiye da arba'in "Amma yanzu mutum shida suka rage,"Inji shi. "Mai da gidajen jaridu da sauran kafafen yaɗa labarai a yanar gizo da matakin gwamnati na tsayar da sayen jaridu ya taimaka wajen durƙushewar sana'ar mu,"Inji Malam Rabi'u. Shugaban ƙungiyar…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 21 domin biyan giratuti na ma’aikata

Gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan 21 domin biyan giratuti na ma’aikata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya amince da sakin sama da Naira biliyan 21 domin biyan giratutu na ritaya da waɗanda suka rasu na Jihar, ƙananan hukumomi da hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi (LEA) a jihar. A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai da al'adu Dr Salisu Bala Zango ya ce shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Falalu Bawale ya sanar da haka a ofishinsa yayin taron farko na kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin tsara da shirya yadda za a raba kuɗaɗen. A cewar shugaban ma’aikatan jihar, kuɗaɗen an…
Read More
Sanata Wadada ya ƙaddamar da masallacin Masjid Zaidan a Keffi

Sanata Wadada ya ƙaddamar da masallacin Masjid Zaidan a Keffi

DAGA JOHN WADA a Keffi A ci gaba da gagaruman gudumawa da yake bayarwa don ɗaukaka harkokin addini, Sanata da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa ta yamma a majalisar dattijai ta tarayya, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya ƙaddamar da wani babban masallaci mai sunar Masjid Zaidan wadda ya gina a gab da titin babban hanyar nan na Keffi zuwa Abuja a garin Keffi. A jawabinsa a lokacin taron ƙaddamar da masallacin, wani babban malamin addinin musulunci mai suna Sheikh Dalhatu Abubakar Abdullahi Kantana wanda shi ne kuma mataimakin shugaban ƙungiyar JIBWIS na ƙasa da ke Jos jihar Filato ya buƙaci masu…
Read More
Farfesa Barde ya gabatar da laccar jami’ar Nasarawa karo na 56

Farfesa Barde ya gabatar da laccar jami’ar Nasarawa karo na 56

Daga JOHN D. WADA a Lafia An shawarce masu harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan baki ɗaya su riƙa zuba jari sosai a fannin fasahohi domin taimaka musu wajen ɗorewar harkokinsu na kasuwanci da kuma inganta ayyuka da nasarori. Shawarar ta fito ne daga wani malami a sashen gudanar da kasuwanci na jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Barnabas Embugus Barde. Farfesan ya kuma shawarce su da su riƙa koyar da ma’aikatansu yadda za su yi amfani da sabbin fasahohin zamani yadda ya kamata, domin taimaka wa kasuwancinsu kawar da tsofaffin dabaru da kuma samun ƙarin yawan aiki cikin…
Read More
Dattawan Arewa sun buƙaci soke yarjejeniyar bayanan tara haraji tsakanin Nijeriya da Faransa

Dattawan Arewa sun buƙaci soke yarjejeniyar bayanan tara haraji tsakanin Nijeriya da Faransa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Zauren Dattawan Arewacin Nijeriya da suka ƙunshi jihohi 19 na ɗaukacin jihohi talatin da shida jimlatan na ƙasar nan sun buƙaci Shugabsn ƙasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu daya gaggauta soke takardar yarjejjeniyar fahimtar juna da hukumomin tara kuɗaɗen haraji na ƙasashen biyu, "Federal Inland Revenue Service (FIRS) da  France’s Direction Générale des Finances (DGFiP) suka rattaba hannayen su, da gargaɗin cewa yarjejeniyar wata mummunar katoɓara ce ga 'yancin tattalin Nijeriya, har ma da lamuran tsaronta. A wata takardar jawabi da mai magana da yawun zauren dattawar, Abubakar Jika Jiddere ya fitar a birnin tarayya na…
Read More
Mai Kaltungo ya halarci bikin cikar Sarkin Keffi shekaru 10 kan karagar mulki

Mai Kaltungo ya halarci bikin cikar Sarkin Keffi shekaru 10 kan karagar mulki

Daga RABIU SANUSI a Kano Uban ƙasa, Mai martaba HRH Engr. Saleh Muhammad Umar, OON (Mai Kaltungo), ya halarci bikin cikar Mai Martaba Sarkin Keffi, HRH Dr. Shehu Chindo Yamusa III, shekaru goma a kan karagar mulki. Engr. Saleh Muhammad Umar, wanda shi ne North East Coordinator na NTRC da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Gombe ya wakilci masarautar Kaltungo tare da tawagarsa a wannan gagarumin biki. Bikin ya gudana ne a harabar Kwalejin Gwamnati da ke birnin Keffi, inda ya samu halartar manyan sarakuna daga Jihar Nasarawa da ma sauran sassan kasar nan, tare da ‘ya’yan masarautar Keffi,…
Read More
A dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji – ADC

A dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji – ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jam’iyyar haɗakar 'yan adawa ta ADC ta nuna damuwa kan abin da ta kira gazawa iri-iri da ’yan Nijeriya ke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji nan take. Jam’iyyar ta ce aiwatar da sabuwar dokar haraji zai ƙara tsananta matsin rayuwa ne kawai ga talakawa ba. A cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, ta jaddada buƙatar tattaunawa a faɗin ƙasa da ƙungiyoyin ƙwadago da na fararen hula da ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa da ƙwararru, da kuma gwamnatocin jihohi. Jam’iyyar…
Read More