19
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya musanta zargin iƙirarin da Bello Turji ya yi cewa manufofin gwamnatinsa ne suka rura wutar ayyukan ‘yan bindiga a Sakkwato da Zamfara. Bafarawa ya ce ayyukan ‘yan bindiga bai zama ruwan dare a lokacin da ya sauka daga gwamnan Sakkwato ba a jiharsa ko a Zamfara a 2007 ba. Kuma ya ƙara da cewa bai san dalilin da ya sa Turji ya alaƙanta shi da abubuwan da ke faruwa bayan shekaru da sauka daga mulki ba. Turji, a wani faifan bidiyo da ya fitar a ranar Lahadi, ya…
