ukarofi

12663 Posts
Gwamnan Kano ya biya biliyan N15.7 na haƙƙoƙin tsofaffin kansiloli

Gwamnan Kano ya biya biliyan N15.7 na haƙƙoƙin tsofaffin kansiloli

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da kammala biyan wani tsohon bashi da ya daɗe yana jiran warwarewa, inda gwamnatin jihar ta raba sama da Naira biliyan 8.2 a matsayin ragowar alawus-alawus ga tsofaffin kansiloli 1,371. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba. Biyan kuɗaɗen ya nuna nasarar kammala wani shiri mai matakai uku da gwamnatin ta kirkiro domin biyan dukkan hakkokin sallama da suka hada da garatuti, alawus na kayan ɗaki, masauki, da hutun aiki, ga kansilolin da suka…
Read More
Tsakanin gargajiya da zamani: Tarihin ɗinki da canjin salon kaya a Arewa

Tsakanin gargajiya da zamani: Tarihin ɗinki da canjin salon kaya a Arewa

Daga MARYAM BATOOL A Arewa, kaya ba kawai rufe jiki kawai suke ba, suna bayyana al’ada, martaba da kwaliyya. Daga rigar zane ta gargajiya irin su saki, tsamiya, bunu, fatari da sauransu, har zuwa kayan zamani masu salo, ɗinki da salon kaya sun kasance wani muhimmin ɓangare na rayuwa a  Arewa. Wannan rubutun zai duba yadda tarihin ɗinki da salon kaya ya sauya daga ƙarni zuwa ƙarni, da kuma yadda matasa ke ɗaukar wannan sana’a da kuma sabunta ta a yau. Asalin ɗinki a Arewa: Shigowar Musulunci ya kawo sauye-sauye a tsarin kaya, inda aka fi karkata zuwa sutura masu…
Read More
Kotu ta hana belin Malami

Kotu ta hana belin Malami

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun Babban Birnin Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya gabatar domin a sake shi daga tsarewar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC. Alƙalin kotun, Mai shari’a Babangida Hassan, ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ba shi da hurumin bayar da beli, kasancewar wata kotu mai matsayi iri ɗaya ta riga ta bai wa EFCC umarnin tsare Malami domin ci gaba da bincike. Rahotanni sun nuna cewa Malami, wanda ke daga…
Read More
Majalisar Dattawa ta amince da naɗin jakadun Nijeriya 64

Majalisar Dattawa ta amince da naɗin jakadun Nijeriya 64

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da sunayen mutane 64 da aka naɗa a matsayin jakadu, bayan ta yi la’akari da rahoton Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar. A zaman da aka gudanar, Shugaban Kwamitin Harkokin Waje, Sanata Sani Bello, ne ya gabatar da rahoton tantancewar, inda majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin baki ɗaya. Sai dai a yayin zaman, Sanata Sahabi Yau ya yi tsokaci kan rashin sunan kowanne ɗan jihar Zamfara a cikin jerin sunayen da aka gabatar. Ya buƙaci majalisar ta sanar da Shugaban ƙasa game da wannan giɓi, domin a gyara. Shugaban Majalisar Dattawa…
Read More
Gwamna Yusuf ya yaba wa Tinubu da Abba Bichi kan aikin titin Wuju-wuju a Kano

Gwamna Yusuf ya yaba wa Tinubu da Abba Bichi kan aikin titin Wuju-wuju a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar da ya bayar na sa hannun GwamnatinTarayya domin kammala shahararren aikin titin Wuju-Wuju, wanda kuɗinsa ya kai Naira biliyan 47. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis. Gwamnan ya yi wannan yabo ne yayin da yake jawabi a taron Majalisar Zartarwa ta Jiha karo na 35, inda ya bayyana cewa an fara aikin titin ne tun a shekarar 2013 a zamanin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa…
Read More
Gwamnatin Nasarawa da ƙasar Angola za su haɗa hannu don bunƙasa tattalin arzikinsu

Gwamnatin Nasarawa da ƙasar Angola za su haɗa hannu don bunƙasa tattalin arzikinsu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da takwararsa ta Jihar Bengo a ƙasar Angola wato Dokta Maria Antonia sun rattaɓa hannu a wata yarjejeniya na musamman a tsakaninsu don bunƙasa fannonin aikin noma da ilimi da ma'adanai da sauran su don cigaban jihohin biyu da ma ƙasashen nasu baki ɗaya. Da yake jawabi a yayin zaman sanya hannun wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ta Nasarawa dake Lafiya babban birnin jihar, Gwamna Abdullah Sule ya bayyana cewa tabbas ba shakka yarjejeniyar da zarar aka fara aiwatar da su za su kawo cigaba masu…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sake buɗe makarantun ‘Unity’ 47

Gwamnatin Tarayya ta sake buɗe makarantun ‘Unity’ 47

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada alƙawarinta na kare ɗalibai da kuma tabbatar da ci gaba da iliminsu a faɗin Nijeriya, bayan da ta sake buɗe makarantun haɗin gwiwa da jihohi, waɗanda ake kira sa ‘Unity Schools’ a turance guda 47. A cewar wata sanarwa gwamnatin a jiya Alhamis, wacce Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya sanya wa hannu, bayan ƙarfafa tsarin tsaro a ciki da kewayen makarantun da abin ya shafa, ayyukan ilimi sun ci gaba da gudana gabaɗaya. Sanarwar ta ce: "ɗalibai sun dawo…
Read More
Rikici da Ɗangote ya ci kujerar shugaban NMDPRA

Rikici da Ɗangote ya ci kujerar shugaban NMDPRA

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Abu kamar wasa, amma sai rikici tsakanin Shugaban rukunin kamfanonin ɗangote, Alhaji Aliko ɗangote, da Shugaban Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Malam Farouk Ahmed, ya kai ga cin kujerar shugaban na hukumar ta NMDPRA. Tun da fari dai ɗangote ya yi kira ga hukumomin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da su gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa Shugaban Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), Malam Farouk Ahmed, kan biyan kuɗin karatun ’ya’yansa a ƙasar Switzerland da ya kai kimanin dala miliyan biyar. Dangote…
Read More
Ɗan Majalisar Jihar Zamfara ya sha kashi a hannun al’ummar sa

Ɗan Majalisar Jihar Zamfara ya sha kashi a hannun al’ummar sa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan Majalisar Jihar Zamfara mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru ta Kudu, Hon. Kabiru Mika'ilu Dangulbi yasha dukan tsiya a hannun al'ummar sa a Garin Dansadau da ke ƙaramar hukumar Maru. Rahotanni sun bayyana cewar lamarin ya faru ne a jiya Laraba yayin da ɗan majalisar ya bi tawagar gwamnan jihar a yayin da gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar aiki a yankin na Dansadau. Ɗan Majalisar ya fuskanci fushin al'ummar sa ne a yayin da ya fito wajen jim kaɗan bayan Gwamna Dauda Lawal ya shiga fadar sarkin na Dansadau don ganawa da shi. Fusatattun…
Read More
Motsa jiki ma kwalliya ne

Motsa jiki ma kwalliya ne

Daga AISHA ASAS Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne. Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaƙulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan…
Read More