DAGA JOHN WADA a Keffi
A ci gaba da gagaruman gudumawa da yake bayarwa don ɗaukaka harkokin addini, Sanata da ke wakiltar mazaɓar Nasarawa ta yamma a majalisar dattijai ta tarayya, Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya ƙaddamar da wani babban masallaci mai sunar Masjid Zaidan wadda ya gina a gab da titin babban hanyar nan na Keffi zuwa Abuja a garin Keffi.
A jawabinsa a lokacin taron ƙaddamar da masallacin, wani babban malamin addinin musulunci mai suna Sheikh Dalhatu Abubakar Abdullahi Kantana wanda shi ne kuma mataimakin shugaban ƙungiyar JIBWIS na ƙasa da ke Jos jihar Filato ya buƙaci masu hannu da shuni su riƙa yin koyi da sanata Ahmed Aliyu Wadada wajen yin amfani da dukiyoyin su don bunƙasa harkokin addinin musulunci a jihar da ma ƙasa baki ɗaya a ko yaushe.
Sheikh Dalhatu ya ƙara da cewa sabon masallacin Masjid Zaidan ɗin idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata ba shakka zai kawo taimako da cigaba ga rayuwar musulmai a yankin da ƙasa baki ɗaya.
A nasa ɓangaren shima da yake jawabi, wadda ya gina masallacin wato sanata Ahmed Aliyu Wadada bayan ya gode wa duka waɗanda suka samu damar halartar taron ƙaddamar da masallacin, ya kuma bayyana godiyar sa ta musamman ga waɗanda suka taimaka a fannoni dabandaban don tabbatar an kammala aikin gina masallacin cikin lokaci ba tare da matsala ba inda ya ƙara da cewa, “Muna fatar za a yi amfani da masallacin yadda yakamata don samun rahamar Ubangiji a rayuwar mu sa’anan ina kira ga kowa musamman masu hannu da shuni cikin al’umma sun tabbatar suna yin duka mai yuwa wajen bunƙasar ayyukan addini a duk fannin rayuwa da suka tsinci kansu don samun ladar mahallici a jihar mu ta Nasarawa da ma ƙasa gaba ɗaya.”
Haka kuma a cikin bayaninsa, Dakta. Musa Ahmed Mohammed, wanda shi ne akanta janar na gwamnatin jihar wanda ya kuma wakilci gwamnatin jihar ya yaba wa hangen nesa da wannan gagarumar gudumawa da sanata Wadada yayi na gina masallacin kana shima ya buƙaci masallata suyi amfani da sabon masallacin yadda yadace don su daɗe suna cin moriyar sa a fannin ibada.
Shima a nasa jawabin, kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu na jihar wato honorabu Aminu Maifata da mai martaba Odyong Nyankpa da sauran manyan baƙi duk sun bayyana godiyar su ga sanata Wadada saboda gudanar da wannan babban aikin ibada inda suma suka buƙaci musulmai su yi amfani da masallacin yadda yadace wajen yin bautar Allah.
Shi dai wakilin mu a jihar ta Nasarawa, John Wada ya kuma rubuto cewa sabon masallacin Masjid Zaidan din, sanata Wadada ya gina shi ne irin na zamani da ke cike da kayayyakin ibadar suma duk irin na zamani, kuma an gina masallacin ne gab da babban titin Keffi zuwa Abuja da hakan zai kuma bai wa matafiya damar tsayawa su gudanar da ibada a duk lokaci da buƙatar hakan ta taso.
