ukarofi

12687 Posts
Abin da tawagar Nijeriya ta shaida wa Amurka kan zargin kisan Kiritoci

Abin da tawagar Nijeriya ta shaida wa Amurka kan zargin kisan Kiritoci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wakilan Nijeriya da Amurka sun gana domin tattauna yadda ƙasashen biyu za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tabbatar da tsaron 'yan Nijeriya. Gwamnatin Nijeriya ta tura wakilai zuwa Amurka ne domin ganawa da hukumomin Amurka domin lalubo hanyoyin da za a bi domin magance matsalar, wadda ta daɗe tana addabar 'yan ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar aika sojojin zuwa Nijeriya bayan ya bayyana ƙasar a "matsayin ƙasar da yake sa ido' sannan kuma ya yi barazanar 'shiga domin fatattakar' 'yan ta'adda. Haka kuma Trump ya…
Read More
Kotu ta kori ƙarar da ICPC ta shigar kan shugaban hukumar KANSIEC ta Kano 

Kotu ta kori ƙarar da ICPC ta shigar kan shugaban hukumar KANSIEC ta Kano 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta kori shari’ar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar kan wasu manyan jami’an Hukumar Zaɓen ƙananan Hukumomi ta Jihar Kano (KANSIEC). Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi; Sakataren Hukumar, Anas Muhammed Mustapha; da Daraktan Kuɗi na Hukumar, Ado Garba. An tsara shari’ar mai lamba FHC/ABJ/210/2025 domin gurfanar da su a gaban kotu ranar Litinin, amma zaman bai ci gaba ba saboda waɗanda ake tuhuma ba su bayyana a kotu ba.…
Read More
Tsaron makarantu: An ƙaddamar da sabbin matakai a Gombe

Tsaron makarantu: An ƙaddamar da sabbin matakai a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wata tattaunawa tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar. An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Shugaban ’Yan Sanda na ƙasa, Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙara tsaurara tsaro a makarantu a faɗin ƙasar nan. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan duba tsarin tsaro na yanzu a makarantu, musamman waɗanda ke yankunan da ke da ƙalubale,…
Read More
Kogi: An ruwaito cewa ‘yan bindiga na shaƙa wa mutane wani sinadari mai guba kafin garkuwa da su

Kogi: An ruwaito cewa ‘yan bindiga na shaƙa wa mutane wani sinadari mai guba kafin garkuwa da su

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Akwai fargaba a tsakanin mazauna garin Egbe da ke ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma ta jihar Kogi, bayan labarin da ke tayar da hankali cewa yanzu haka 'yan fashi suna amfani da sinadarai masu guba a gidaje don kawar da hankalin mutane kafin yin garkuwa da su. An tattaro cewa an kai hare-hare aƙalla sau biyu a kan al'umma a safiyar Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025, inda aka yi garkuwa da mazauna biyu yayin da wani kuma ya tsere bayan ya aika da saƙon damuwa. 'Yan fashin, waɗanda aka bayyana a matsayin masu hazaƙa…
Read More
Iyalan Marigayi Audu Baƙo sun nemi ɗaukin Gwamnan Kano kan a sakar musu kayan mahaifinsu

Iyalan Marigayi Audu Baƙo sun nemi ɗaukin Gwamnan Kano kan a sakar musu kayan mahaifinsu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An ƙaddamar da littafin tarihin Gwamnan mulkin soja na farko na jihar Kano, Alhaji Audu Baƙo  mai suna "Governor Audu Bako Man of Wisdom and Foresight, wanda Kwamishinan 'yan sanda mai ritaya Dogo Manya ya rubuta. Taron an gudanar da shi ne a Kano da ya samu halartar manyan baƙi daga sassa daban-daban na jihar Kano da Jigawa wato tsohuwar jihar Kano da suka haɗa da mataimakin Gwamnan jihar Jigawa Ahmad Usman Gumel da Kwamishinan ma'aikatar kasuwanci na jihar Kano Gwani Wada Sagagi wanda ya wakilci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a yayin taron. Babban…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta ɗauki matakan tallafawa ‘yan kasuwa a jihar – Hon. AbdulRahman Tunbido

Gwamnatin Zamfara ta ɗauki matakan tallafawa ‘yan kasuwa a jihar – Hon. AbdulRahman Tunbido

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana cewa ƙananan hukumomin jihar Zamfara  14 za su bajekolin albarkatun da Allah ya hore musu a bikin bajekoli na duniya karo na 46 da aka buɗe a jihar Kano. Kwamishinan kasuwanci da masana'antu da yawon buɗe ido na jihar Zamfara Hon. AbdulRahman Tunbido Kogunan Maru ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a yayin buɗe bajekolin a Kano. Ya ƙara da cewa za su nuna kayan albarkatun su ne domin duniya ta ga irin albarkatun da suke da su musamman a rana ta musamman da za a yi na jihar…
Read More
Zan kashe ku idan kuka kuskura kuka shigo Fatakwal, Dokubo Asari ya gargaɗi ‘yan bindiga

Zan kashe ku idan kuka kuskura kuka shigo Fatakwal, Dokubo Asari ya gargaɗi ‘yan bindiga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon shugaban 'yan-aware kuma mai fafutukar kare haƙƙin 'yan Neja Delta, Mujahid Asari-Dokubo, ya gargaɗi Boko Haram da sauran ƙungiyoyin 'yan ta'adda da kada su shiga Fatakwal, yana mai cewa ba zai yi jinkirin fuskantar duk wani ɗan ta'adda da ya yi yunƙurin yin ta'addanci a birnin ba. Tsohon shugaban 'yan-awaren a wani bidiyo da ya yaɗu a ranar Talata ya ce imaninsa a matsayinsa na Musulmi ba zai hana shi fada ba idan aka kai masa hari. Ya ce, "Idan Boko Haram ta zo Port Harcourt, ka san cewa kasuwancina shine in kashe…
Read More
’Yan bindiga sun sake yin garkuwa da mutum 11 a Kwara

’Yan bindiga sun sake yin garkuwa da mutum 11 a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara. Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci. A cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira. Sabon…
Read More
Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirin tallafa wa hanyoyin yaɗa labarai a taron SNB 

Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirin tallafa wa hanyoyin yaɗa labarai a taron SNB 

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ci gaba da inganta ɗabi’a da ƙwarewar aikin jarida a Nijeriya, yayin da ƙungiyar Society of Nigerian Broadcasters (SNB) ta kammala taron ƙasa na biyu da bikin shigar da sababbin mambobi a Kano. Taron, wanda ya ɗauki taken “ƙa’idojin Aikin Jarida da ƙwararru a Zamanin Fasahar Artificial Intelligence (AI),” ya tattaro manyan ƙwararru a harkar watsa labarai, jami’an gwamnati, masana, da shugabannin masana’antu domin tattauna ƙalubalen da sabuwar fasaha ke haifarwa ga aikin watsa labarai. A jawabin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Darakta Janar na Yada…
Read More
Abin da Tinubu ya kamata ya yi don magance matsalar tsaro –Kwararre a harkar tsaro

Abin da Tinubu ya kamata ya yi don magance matsalar tsaro –Kwararre a harkar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani ƙwararre a fannin tsaro, Seyi Babaeko, ya yi gargaɗin cewa Nijeriya na iya fuskantar wani mummunan yanayi, yayin da hare-haren ta'addanci, sace-sacen mutane, da kuma mamaye al'umma ke ci gaba da ƙaruwa a faɗin ƙasar. Mista Babaeko, Manajan Darakta kuma Babban Jami'in Gudanarwa na Absolute Security and Adɓance Protocol Ltd, ya yi gargaɗin yayin da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ranar Talata a Legas. A cewarsa, ƙasar na karkata zuwa ga wani yanayi mai cike da ruɗani kuma tana buƙatar gaggawar shiga tsakani daga Shugaba Bola Tinubu don hana taɓarɓarewar…
Read More