30
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Tsaron Jihar Ondo, Amotekun Corps, ta ce ta fara sintiri a makarantun kwana a jihar. Adetunji Adeleye, Kwamandan Rundunar, ya sanar da hakan a ranar Talata a Akure yayin da yake gabatar da mutane 16 da ake zargi da laifuka daban-daban. Mista Adeleye, wanda ya ce an sanya cikakken sa ido kan makarantu masu kayan kwana, ya ce an sanya ido ne "bayan koke-koken da aka yi kwanan nan na keta ka'idojin tsaro da sace mutane. "A cikin makon da ya gabata, mun ziyarci makarantu da yawa, kuma mun sanya ido kan duk…
