ukarofi

12687 Posts
Yadda farashi a Nijeriya ya sake faɗuwa

Yadda farashi a Nijeriya ya sake faɗuwa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Farashin kayan masarufi na cikin gida ya ci gaba da sauka a cikin shekara guda, abin da ya nuna tasirin raguwa a hauhawar farashi wadda ke saukowa a hankali a watannin baya-bayan nan. Wannan ci gaba na faruwa ne yayin da farashin ɗanyen man fetur na brent crude ya koma Dala 62.09 a ƙarshen makon da ya gabata. Bisa bayanan da Bismarck Rewane, shugaban kamfanin Financial Derivatives Company (fdc), ya fitar a rahoton kasuwanci na ƙarshen mako, farashin abinci da dama sun kai mafi ƙasa tun farkon shekarar nan. Ya ce shinkafa na kai N70,000, wake…
Read More
EU ta zuba Yuro biliyan 15.5 don samar da tsayayyen lantarki a Afrika

EU ta zuba Yuro biliyan 15.5 don samar da tsayayyen lantarki a Afrika

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta amince da wani gagarumin tallafi na yuro biliyan 15.5 domin tallafa wa yaƙin neman zartar da sabbin ayyukan makamashi mai ɗorewa a nahiyar Afrika, wani yunƙuri da ake sa ran zai inganta samar da wutar lantarki ga miliyoyin jama’a tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa. Wannan shiri, wanda Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula ɓon der Leyen, da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, suke jagoranta, na da nufin ƙara samar da makamashi tsaf, faɗaɗa hanyoyin samun wuta ga al’umma, da kuma haɓaka jarin da zai taimaka wa…
Read More
’Yan Yahoo sun fi ’yan siyasa lalata tattalin arzikin Nijeriya — EFCC

’Yan Yahoo sun fi ’yan siyasa lalata tattalin arzikin Nijeriya — EFCC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC), ta ce ayyukan masu damfarar intanet da aka fi sani da Yahoo na janyo wa tattalin arzikin Nijeriya asara mai girma fiye da kowace ƙungiya a halin yanzu. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya jaddada cewa yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa ba na gwamnati kaɗai ba ne, illa lamari ne da ke buƙatar haɗin kan kowa da kowa. A cewarsa, “Gaskiyar da muke fuskanta a yau a ƙasar…
Read More
Kano: Kwankwaso, Shekarau da Ganduje sun ci moriyar dimukraɗiyya amma sun hana ta rawar gaban hantsi, inji Salisu Maje

Kano: Kwankwaso, Shekarau da Ganduje sun ci moriyar dimukraɗiyya amma sun hana ta rawar gaban hantsi, inji Salisu Maje

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kungiyar  Maitaimako Organisation da ke ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kano, tsohon ɗan majalisar jiha na ƙaramar hukumar, wanda kuma yanzu hadimi ne a ofishin ƙaramin Ministan Gidaje da raya  birane , Hon. Salisu Maje Ahmad Gwangwazo da aka fi sani da Alhajin Bana ta ƙaddamar da tsohon ɗan takarar Gwamnan Kano, Malam Salihu Sagir Takai a matsayin daraktan yaƙin neman zaɓe na Sanata Barau Jibrin na Gwamnan Kano ƙungiyar ta Maitaimako ta ƙaddamar da Malam Salihu Takai ne a yayin taron cika shekara 23 da kafa ta da aka gudanar a babban…
Read More
Shugabannin PDP na yunƙurin sulhu da Sule Lamiɗo

Shugabannin PDP na yunƙurin sulhu da Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabannin jam'iyyar adawa a Nijeriya, PDP, sun yi kira ga tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamiɗo da ya maida wuƙarsa cikin kube, ya kuma goyi bayan ƙoƙarin da ake yi na daidaita jam'iyyar. Kiran ya biyo bayan hirar da Lamido ya yi kwanan nan da sashen Hausa na BBC, inda ya soki yadda jam'iyyar ke tafiyar da rikicin shugabanci tare da yin nuni ga wata shari'a da ya gabatar kan lamarin. Da yake magana kan lamarin, Umar Sani, wani makusancin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya ce da'awar da…
Read More
Uba Sani da Yerima Shettima ƙungiyar Capacity Movement ta ɗauka zuwa yanzu – Sani Sado

Uba Sani da Yerima Shettima ƙungiyar Capacity Movement ta ɗauka zuwa yanzu – Sani Sado

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna  ƙungiyar Capacity Movement, ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na ƙasa Alhaji Shehu Sani Sado, ta yi ƙarin haske kan jita-jita, tambayoyin jama’a da kafafen yaɗa labarai ke yi dangane da matsayar ta a siyasa yayin da harkokin siyasar Jihar Kaduna ke ƙara ɗumama. A matsayin ta na ƙungiyar da ta ginu a kan gaskiya, jama’a da tsari mai nagarta, hakan ya sa, ya zama wajibi ta jaddada matsayar ta a fili. Sanarwar mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar a ƙasa, Dakta Bashir Umar Mohammed ta ce, “A halin yanzu, bayan Ambasada Yerima Usman Shettima da…
Read More
Tsofaffin kansilolin Filato sun yi watsi da yunƙurin Gwamna Mutfwang na shiga APC

Tsofaffin kansilolin Filato sun yi watsi da yunƙurin Gwamna Mutfwang na shiga APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Zauren Tsofaffin Kansiloli na Nijeriya, reshen jihar Filato, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa Nentawe Yilwatda, Sanata Simon Lalong, da shugaban jam'iyyar APC na jihar Rufus Bature, da su yi watsi da duk wani yunƙurin Gwamna Caleb Mutfwang na shiga jam'iyyar. Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Jos, Shugaban ƙungiyar, Dabit John Dashe, ya yi watsi da amincewar da wata kungiya mai suna "Coalition of Concerned Tsoffin Kansilolin APC da Grassroots Mobilisation (CFACGM)" ta yi kwanan nan a matsayin "yunƙurin da Gwamna da wakilansa…
Read More
’Yan Arewa mazauna Kudu maso Yammacin Nijeriya sun yi taron haɗin kai a Legas

’Yan Arewa mazauna Kudu maso Yammacin Nijeriya sun yi taron haɗin kai a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas Kungiyar 'Yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya ta gudanar da wani babban taron haɗin kai a birnin Legas, domin ƙarfafa zumunci da haɗa kan al’umma wajen tafiyar siyasar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, gabanin zaɓen shekarar 2027. An gudanar da taron ne ranar Alhamis da ta gabata a harabar babban ɗakin taro da ke Ikeja, inda daraktan janar na tafiyar Tinubu a jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Jibirin Sampam, ya jagoranci taron a matsayin sabon jagoran tafiyar a yankin. Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa maza da mata daga…
Read More
Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta nemi a riƙa mutunta shari’a a Nijeriya

Kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta nemi a riƙa mutunta shari’a a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Kare Haƙƙin Bil'adama ta Duniya (IHRC-RFT) a Nijeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun ƙaruwar amfani da umarnin kotu wajen ƙauce wa shari’a bayan aikata laifuka ko tauye haƙƙin mutane inda take neman a riƙa mutunta shari'a a ƙasar. ƙungiyar ta lura cewa amfani da umarnin kotu a Nijeriya wajen ba bisa ƙa'ida ba na neman ya zama ruwan dare wanda ke hana jami’an tsaro daga kama ko binciken masu aikata laifi. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktan ƙasa ta ƙungiyar Amb. Abdullahi Bakoji Adamu ya fitar. Sanarwar ta ce,…
Read More
Zan ba da gudunmawa mai tsoka wajen bunƙasa NURTW a Legas – Kwamaret Ahmed Isah

Zan ba da gudunmawa mai tsoka wajen bunƙasa NURTW a Legas – Kwamaret Ahmed Isah

Daga DAUDA USMAN a Legas Sabon Shugaban ƙungiyar Direbobin J5 ta ƙasa, ƙarƙashin NURTW reshan Jihar Legas da ke shiyar unguwar mile12 a Legas, Kwamaret Umar Ahmed Isah ya yi alƙawarin cewa zai bayar da ɗimbim gudunmawa wajan kawo cigaban ƙungiyar a jihar da kewayenta gabaɗaya. Kwamaret Umar Ahmed Isah ya yi wannan tsokacin ne a ofishin ƙungiyar da ke kasuwar mile12 a lokacin da suke karɓar baƙuncin waɗansu daga cikin 'yan ƙungiyar ta J5 na unguwanni daban-daban a cikin garin Legas da suka zo taya shi murna tare da fatan alheri dangane da samun wannan matsayi. Sabon shugaban ƙungiyar…
Read More