ukarofi

12687 Posts
Legas: Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin mambobi

Legas: Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin mambobi

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban ƙungiyar ’Yan Arewa na ƙaramar Hukumar Epe a Jihar Legas, Alhaji Ummaru Gwamna Epe, ya shawarci shugabanni da mambobin kungiyar a faɗin jihar da su ƙara haɗa kai da zaman tafiya a tsari ɗaya domin ƙarfafa martabar al’ummar Arewa a Legas. Alhaji Gwamna Epe ya yi wannan kira ne a garin Epe yayin wani taron tattaunawa da ya gudanar tare da wasu jiga-jigan ƙungiyar, wanda yake kanana shugabanci ke gudanarwa a ƙarshen kowane mako domin nazari kan matsaloli da kuma ɗaukar matakan magance su. Ya bayyana cewa, hadin kai da kyakkyawar fahimta ita ce…
Read More
Cin Zarafi: Sarakunan Nafada da Funakaye sun goyi bayan dokar VAPP

Cin Zarafi: Sarakunan Nafada da Funakaye sun goyi bayan dokar VAPP

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe A ci gaba da ƙoƙarin daƙile cin zarafin mata da yara a Gombe, ma’aikatar mata da Walwalar Jama’a ƙarƙashin jagorancin Kwamishiniya Asma’u Muhammad Iganus ta kai ziyara masarautun Nafada da Funakaye, domin ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da cin zarafi a yankunan. A yayin ziyarar farko zuwa Masarautar Nafada, Kwamishiniyar ta bayyana damuwarta kan alƙaluman da suka nuna cewa Gombe na fama da matsalar cin zarafi da kashi 87.46%, abin da ta bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya da ci gaban al’umma. Ta ce hakan ne ya sa ake kai ziyara domin jan hankalin…
Read More
Yara miliyan 2.8 za a yiwa rigakafin Polio a Katsina

Yara miliyan 2.8 za a yiwa rigakafin Polio a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tuni dai Gwamnati ta tura ma’aikata 3,700, ciki har da ƙungiyoyin masu zagayen gida-gida su 961, an kuma tanadi fiye da allurai miliyan 2 domin gudanar da allurar rigafin. Haka kuma akwai ƙungiyoyi na musamman su 993 da za su riƙa aiki a kasuwanni, tashoshin mota, tituna da wuraren cunkoso. Wakilin UNICEF na yankin Kano, R. M. Farah, shi ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da manema labarai a Katsina. A cewar Malam Farah, UNICEF na ci gaba da haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin titin filin Polo

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin titin filin Polo

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Aikin titin wanda zai fashi daga Filin Polo- zuwa Ring Road da nisan kilomita huɗu a birnin Katsina. Wannan aikin na daga cikin shirin gyaran birni na gwamnatin jihar (Katsina Urban Renewal), wanda aka tsara domin inganta zirga-zirgar ababen hawa, bunƙasa haɗin kai tsakanin wurare da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci a cikin birnin. Kwamishinan ayyuka, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa titin zai zama muhimmiyar hanyar da za ta haɗa manyan tituna, wanda zai saukaka sufuri da kasuwanci cikin birnin. Dan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon Aliyu Albaba ya nuna godiya…
Read More
Mai Binciken Kuɗi na Nijeriya ya bankaɗo almundahana biliyan N2.69 a Rundunar ’Yan Sanda

Mai Binciken Kuɗi na Nijeriya ya bankaɗo almundahana biliyan N2.69 a Rundunar ’Yan Sanda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahoton shekara-shekara na Babban Mai Binciken Kuɗi na Nijeriya kan rashin bin ƙa’idojin kuɗi a hukumomin gwamnati na shekarar 2022 ya zargi Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da aikata manyan almundahana a harkokin kuɗi, bayar da kwangiloli ba bisa ƙa’ida ba, da kuma watsi da ayyuka da darajarsu ta kai kimanin Naira Biliyan 2.69. Wani rahoto da jaridar News Point ta wallafa, ya ce, rahoton Oditan ya bayyana cewa hedikwatar ‘yan sanda ta saɓa ƙa’idoji da suka haɗa da biyan kuɗaze ga ayyukan da ba a aiwatar ba, bayar da kwangiloli ba tare da sahalewar majalisa ba,…
Read More
Rashin aiki tsakanin matasa na barazana ga tsaron Nijeriya — Janar Musa

Rashin aiki tsakanin matasa na barazana ga tsaron Nijeriya — Janar Musa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Christopher Musa, ya yi gargaɗin cewa ƙarancin damar tattalin arziki ga matasan Nijeriya na zama babbar barazana ga tsaron ƙasa da ma duniya baki ɗaya. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da jawabin babban baƙo a taron ƙasa da ƙasa karo na 19, babban taro da karrama mambobi na ƙungiyar Nazarin Zaman Lafiya da Aikace-aikacen Zaman Lafiya, wato Society for Peace Studies and Practice, wanda aka gudanar a Cibiyar Albarkatun Abiola Ajimobi da ke Jami'ar Ibadan. Janar Musa ya jaddada cewa akwai matuƙar buƙatar gwamnatocin…
Read More
Majalisar Dattawa ta yi ƙudirin zartar da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane

Majalisar Dattawa ta yi ƙudirin zartar da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dattawa ta zartar da wani ƙudiri da ya sanya garkuwa da mutane a matsayin aikin ta'addanci, inda ta tsara cewa a yi wa Dokar Ta'addanci kwaskwarima don sanya hukuncin kisa mafi girma. Manhaja ta ruwaito cewa an yanke wannan ƙudiri ne a zaman majalisar ranar Laraba. A ƙarƙashin sabuwar dokar, a cewar babban ɓangaren majalisar dokoki, da zarar an tabbatar da hukuncin kisa, dole ne a yi amfani da hukuncin kisa. Nijeriya na fama da matsalar tsaro da ta ci gaba da haifar da hare-hare da tashin hankali daga ƙungiyoyin "'yan fashi" da…
Read More
TETFund ya kashe biliyan N30 wajen samar da tsaro a manyan makarantu

TETFund ya kashe biliyan N30 wajen samar da tsaro a manyan makarantu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Asusun tallafawa manyan makarantu na Nijeriya (TETFund) ta ce, ta kashe Naira biliyan 30 a manyan makarantu a faɗin Nijeriya domin ƙarfafa tsaro a Nijeriya daga watan Janairu zuwa yau. Shugaban asusun, Aminu Masari, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a Katsina a ranar Talata. Masari, wanda ya taɓa zama gwamnan Katsina, ya ce, wannan mataki da suka ɗauka ya taimaka wajen tabbatar da tsaron ɗalibai da lakcarori da sauran mazauna manyan makarantu. A cewarsa, tallafin samar da tsaron ya yi daidai da manufar Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, na…
Read More
Kano da Faransa sun ƙara dangantaka kan shirin gyaran sashen ruwa

Kano da Faransa sun ƙara dangantaka kan shirin gyaran sashen ruwa

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Faransa sun kara zurfafa hulɗarsu a ƙarƙashin Shirin Gyaran Sashen Ruwa na ƙasa, shirin da ke mai da hankali kan inganta walwalar jama’a, ƙarfafa tsarin gudanarwa da kuma tabbatar da ɗorewar samar da ruwan sha. Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba. A yayin tarbar tawagar jakadancin Faransa mai mutum takwas a Gidan Gwamnati, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tattauna da Jakadan Faransa a Nijeriya, Mista Marc Fonbaustier, kan ci gaban muhimman ayyukan ruwa da ake aiwatarwa…
Read More
Wurin Mauludi waje ne da ake ƙara son Manzon Allah, inji Sa’idu Ahmad

Wurin Mauludi waje ne da ake ƙara son Manzon Allah, inji Sa’idu Ahmad

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano An bayyana wajen da ake gudanar da Mauludi da cewa wuri ne mai matuƙar muhimmanci da ake ƙara nuna soyayya da kauna ga Manzon Allah (SAW), tare da koyon kyawawan halayensa domin samun rahamar Allah (SWA). Wannan furuci ya fito ne daga bakin fitaccen malamin addinin Musulunci na garin Dawakin Kudu, Malam Sa’idu Ahmad Gidan Nagunda, yayin Mauludin Zawiyyar Gidan Nagunda da aka gudanar a makon da ya gabata. Malam Sa’idu ya ce Mauludi wata babbar makaranta ce da ke ƙara kusantar da al’umma ga Annabi (SAW), musamman matasa da yara. Ya bayyana cewa…
Read More