Rashin aiki tsakanin matasa na barazana ga tsaron Nijeriya — Janar Musa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Christopher Musa, ya yi gargaɗin cewa ƙarancin damar tattalin arziki ga matasan Nijeriya na zama babbar barazana ga tsaron ƙasa da ma duniya baki ɗaya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da jawabin babban baƙo a taron ƙasa da ƙasa karo na 19, babban taro da karrama mambobi na ƙungiyar Nazarin Zaman Lafiya da Aikace-aikacen Zaman Lafiya, wato Society for Peace Studies and Practice, wanda aka gudanar a Cibiyar Albarkatun Abiola Ajimobi da ke Jami’ar Ibadan.

Janar Musa ya jaddada cewa akwai matuƙar buƙatar gwamnatocin tarayya da jihohi su ɗauki matsalar rashin aikin yi da ƙarancin damar dogaro da kai a tsakanin matasa a matsayin babbar barazana ga tsaron ƙasa da ma zaman lafiyar duniya.

A cewarsa, sakaci wajen warware wannan matsala na iya jefa ƙasa cikin rikice-rikice da tashin hankali mai ɗorewa.

Ya ce zuba jari a fannin kasuwanci na zamani, koyon sana’o’in hannu da fasahohin zamani, tare da bunƙasa tattalin arzikin fasahar zamani, ba kawai ci gaba ba ne, illa ma “mafi araha kuma mafi ingancin aikin kiyaye zaman lafiya” da Nijeriya za ta taɓa aiwatarwa.

A fahimtarsa, duk wata ƙasa da ke neman tabbataccen tsaro dole ta fara daga tushen tattalin arziki na matasa.

A ɓangaren yaƙi da cin hanci da rashawa, tsohon Hafsan Tsaron ya nanata cewa Nijeriya dole ta zama ƙasa mai tsananin tsayawa kan gaskiya da shugabanci nagari.

Ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin laifi da ke rushe tubalan zaman lafiya a hankali, yana lalata amincewar jama’a ga hukumomi, yana gurgunta adalci, tare da haifar da tsarin da fifiko ke rinjayar cancanta. A cewarsa, hukumomi masu bin doka da oda da kuma gaskiya a harkokin mulki su ne tushen kwanciyar hankali na tattalin arziki da zaman lafiya a kowace al’umma.

Janar Musa ya ƙara da cewa, rashin magance waɗannan matsaloli na tattalin arziki da na shugabanci na iya ƙara yawan matasan da ke faɗawa cikin laifuka, ta’addanci da sauran nau’o’in tashin hankali, lamarin da ke barazana ga ci gaban Nijeriya baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Gudanarwa kuma Shugaban Kwamitin Kula da Jami’ar Ibadan, Bisi Akande, ya ce akwai tsananin buƙatar shugabannin ƙasa su gaggauta ɗaukar matakai masu ma’ana domin kauce wa fushin matasan da ba su samu horo da ayyukan yi ba. Ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da yin watsi da matsalolin matasa, abin na iya gurguntar da tsaron ƙasa da tsarin zaman lafiya.

Masu sharhi kan harkokin tsaro da ci gaban matasa na ganin cewa wannan kira na Janar Musa ya zo a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban, tare da yawan matasan da ke fama da rashin aikin yi da talauci. A cewarsu, warware matsalar tattalin arziki na matasa na daga cikin ginshiƙan da za su iya rage shiga laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

By ukarofi