ukarofi

12687 Posts
Yadda matasan Hausawa na Kuje Amuwo Odofin a Legas suka nuna wasannin gargajiya

Yadda matasan Hausawa na Kuje Amuwo Odofin a Legas suka nuna wasannin gargajiya

Daga DAUDA USMAN a Legas A Legas, kwamitin majalisar matasan Hausawa na unguwar F-Shor da ke ƙaramar hukumar Kuje Amuwo Odofin, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Samari Alhaji Tijjani Abdulrahman, ya gudanar da gagarumin taron nuna wasannin gargajiya, domin farfaɗo da al’adun Bahaushe tare da wayar da kan matasa mazauna yankin. Taron, wanda aka gudanar a makon da ya gabata, ya haɗa matasa daga sassa daban-daban na unguwar F-Shor, tare da halartar ’yan kabilu iri-iri. An gudanar da fitattun wasannin gargajiya irinsu damben gargajiya, kokowa, wasan kwai-kwayo, langa da sauran su — duk a matsayin nuni ga al’adun Hausawa na Arewa. Da…
Read More
Yadda ‘yan kasuwar Mile-12 a Legas suka gudanar da addu’o’in nema wa Nijeriya zaman lafiya 

Yadda ‘yan kasuwar Mile-12 a Legas suka gudanar da addu’o’in nema wa Nijeriya zaman lafiya 

Daga DAUDA USMAN a Legas A Legas, an gudanar da taron addu’o’i na musamman a kasuwar Mile 12 International Market ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban kasuwar, Alhaji Isa Muhammad Mai Shinkafa, tare da babban sakataren kasuwar, Alhaji Balarabe Idris. Taron ya mayar da hankali ne kan neman zaman lafiya da bunƙasar Nijeriya. Taron, wanda ya samu halartar manyan malamai magada Annabaw daga sassa daban-daban na Legas, ya gudana cikin natsuwa da tsari. A farkon taron an raba malaman gida uku, inda kashi na farko suka karanta ayoyi masu tsarki na Al-Kur’ani, kashi na biyu suka gudanar da addu’o’i na musamman, yayin…
Read More
Rikicin IPOB ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30,000, ya lalata tattalin arzikinmu – Kalu

Rikicin IPOB ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30,000, ya lalata tattalin arzikinmu – Kalu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ke wakiltar Abia ta Arewa, ya bayyana cewa zanga-zangar 'yan aware ƙarƙashin jagorancin shugaban 'yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ta haifar da mutuwar mutane sama da 30,000 da kuma rugujewar kasuwanci a faɗin Kudu maso Gabas. Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, kwanaki bayan da aka yanke wa Kanu hukuncin aikata laifukan ta'addanci a babban kotun tarayya da ke Abuja. Kalu ya buƙaci shugabannin siyasa na Kudu maso Gabas da magoya bayan Kanu da su kawo ƙarshen "hayaniya" su mai da hankali…
Read More
Shehu Sani ya caccaki El-Rufai kan iƙirarin biyan ‘yan bindiga Naira biliyan ɗaya

Shehu Sani ya caccaki El-Rufai kan iƙirarin biyan ‘yan bindiga Naira biliyan ɗaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon ɗan majalisar dokokin ƙasa a majalisar dattawa ta 8, Shehu Sani, ya soki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin da ake yi masa na biyan 'yan fashi Naira biliyan 1. A cewarsa, El-Rufai, wanda aka san shekaru takwas a matsayin gwamna a jihar Kaduna yana tallata al'adar kwantar da hankalin 'yan ta'adda da 'yan fashi, ba shi da ikon zargi da kuma yi wa gwamnatin Uba Sani zagon ƙasa kan biyan 'yan fashi. Sanata Sani, wanda kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam ne, ya ce a cikin wata sanarwa a…
Read More
Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000. Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida. Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu. Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya, don tunatar da ku cewa gwamnatin…
Read More
Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna

Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADɓS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta. Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara. Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da…
Read More
Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunan mutum uku zuwa Majalisar Dattawa, domin tantance su a matsayin sabbin jakadun Nijeriya. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya sanar da haka a zaman majalisar na ranar Laraba. Waɗanda aka zaɓa sun haɗa da Kayode Are daga Jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga Jihar Jigawa da kuma Ayodele Oke. Bayan karanta takardar Tinubu, Akpabio ya ce, “Sunaye uku ne zuwa yanzu, tabbas sauran za su biyo baya.” Tun bayan ɗarewarsa kan mulki a 2023, Tinubu bai naɗa jakadu ba har yanzu. Mutane da dama sun daɗe suna…
Read More
Tukur Mamu ya karɓi miliyan N50 daga kuɗin fansar harin jirgin ƙasan Kaduna – DSS

Tukur Mamu ya karɓi miliyan N50 daga kuɗin fansar harin jirgin ƙasan Kaduna – DSS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar tsaro ta DSS ta zargi ɗan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin ƙasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karɓar Naira miliyan 50 daga kuɗin fansar fasinjojin. Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana aikin kwamitin babban hafsan tsaron ƙasa da aka kafa domin tattaunawa da masu garkuwa da mutanen, musayar saƙonnin murya da mai magana…
Read More
Kano ta ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziki da ƙasar Sin

Kano ta ƙara ƙarfafa dangantakar tattalin arziki da ƙasar Sin

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi bakuncin Mataimakin Shugaban Jakadancin Jamhuriyar Jama’ar Sin a Nijeriya, Hon. Zhou Hongyou, wanda ya jagoranci wata tawaga zuwa Fadar Gwamnati ta Kano domin ziyarar ban-girma. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba. Hon. Zhou Hongyou ya ce ziyarar tasa na nuna irin girmamawar da kasar Sin ke yi wa Kano a matsayin daya daga cikin muhimman cibiyoyin kasuwanci a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya. Ya yaba wa gwamnan…
Read More
Yadda mayaƙan Boko Haram suka fille kan mata biyu a Borno

Yadda mayaƙan Boko Haram suka fille kan mata biyu a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa mayaƙan sunyi wa matan kisan gilla ne bisa zargim yin shirka.   ƙungiyar ta kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayaƙan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya. An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar. Rahotanni sun…
Read More