28
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani shaida a shari'ar da ake ci gaba da yi wa Olu Agunloye, tsohon ministan wutar lantarki da ƙarafa, ya shaida wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa takardar kwangilar da aka yi amfani da ita wajen bayar da aikin wutar lantarki na Mambilla ta dala biliyan 6 ta jabu ce. Umar Babangida, wanda shi ne shaida na uku a gaban kotu (PW3), ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da ake yi masa tambayoyi a gaban Alƙali Jude Onwuegbuzie. Ana shari'ar Agunloye kan tuhumar da aka yi masa na cin hanci da…
