28
Nov
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Umarnin da Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya bayar na rage yawan ’yan sandan da ke gadin manyan mutane ya fara aiki, bayan da Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa, an janye jami’ai 11,566 daga ayyukan gadin manyan mutane tare da mayar da su manyan ayyukan tsaro a faɗin ƙasa. Egbetokun ya bayyana hakan ne a yayin taro da manyan kwamandojin ’yan sanda a Abuja a ranar Alhamis, inda ya ce matakin wani shiri ne na musamman da aka ƙaddamar domin ƙarfafa aikin tsaro a sahun gaba da dawo da ganin ’yan sanda…
