ukarofi

12688 Posts
Bichi: An bayyana Kansilan Fagolo a matsayin jajirtacce

Bichi: An bayyana Kansilan Fagolo a matsayin jajirtacce

An bayyana kansilan mazaɓar Fagolo dake ƙaramar hukumar Bichi, Hon. Habibu Musa Habibu kuma sakataren ƙungiyar Kansiloli ta Jihar Kano, a matsayin jajirtacce bisa tsayin daka da yake yi wajen cigaban al'umar yankinsa. Ɗaya daga cikin matasan yankin Mazabar Fagolo, Aliyu Abdullahi Ibrahim, ya bayyana ayyukan kansilan da suka ƙunshi gyaran makarantu; Fagolo firamare, Kungu firamare da suka haɗa da samar da ajujuwa, zuba kujeru, saka silin, fenti, kofofi da kuma ofishin malamai. Haka a garin Kadage da Tukwibi ya samar da kyakkyawan yanayi irin wannan a makarantunsu na firamare domin inganta ilimin al'ummar yankinsa. "Idan ka gyara gini dole…
Read More
Ƙaramar Hukumar Bichi za ta gina wa dagatanta 44 sabuwar fada

Ƙaramar Hukumar Bichi za ta gina wa dagatanta 44 sabuwar fada

Majalisar ƙaramar hukumar Bichi ta saka ɗambar gina wa dagatan yankin 44 zaunanniyar fada ƙarƙashin sahalewar Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf. Shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, a yayin hirarsu da jami'ar yaɗa labaran yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo a ofishinsa, jim kaɗan bayan ganawarsa da dagatai goma da aikin zai fara ta kansu. Da yake jawabi shugaban ƙaramar hukumar, ya ce, alƙawari ne da suka ɗauka za su cika na gina wa dukkan dagatan ƙaramar hukumar Bichi sabuwar fada, sakamakon rashin gyara na tsawon lokaci. Kazalika da sanin cewa dagatai iyayen ƙasa ne…
Read More
Wasu marubutan da suka samu ɗaukaka suna da girman kai –  Fatima Sunusi Rabi’u 

Wasu marubutan da suka samu ɗaukaka suna da girman kai –  Fatima Sunusi Rabi’u 

"Sanadin kyautar da aka min a dalilin rubutu na samu jarin sana'ata" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Fatima Sunusi Rabi'u, ba marubuciyar onlayin ba ce kawai, tana daga cikin marubutan da suka wallafa littattafansu a tsarin ɗab'i, har ma suka shiga kasuwa. Bayan kasancewarta ƴar kasuwa, tana matuƙar sha'awar aikin jarida na gidan rediyo. Ta rubuta littattafai da gajerun labarai fiye da goma, kuma har yanzu tana kan cigaba da rubutu. A ganawarta da wakilinmu Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar da ake yi wa laƙabi da Ummu Affan ta bayyana masa burinta na ganin an samu canji a harkar rubutun adabi da…
Read More
Ƙananan ‘yan kasuwa na Arewa sun bajekolin sana’o’in mata a Jos

Ƙananan ‘yan kasuwa na Arewa sun bajekolin sana’o’in mata a Jos

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos A yayin da ake kukan taɓarɓarewar tsaro a yankin Arewacin ƙasar nan, musamman a jihohin tsakiyar Nijeriya kamar Jihar Filato, wasu matasa mata da ke harkar tallata kayan da suke sana'antawa a zaurukan sada zumunta, sun bayyana kansu ƙarƙashin shirin kasuwar bajekoli ta Arewa, da suka yi wa laƙabi da Arewa Festival, inda masu ƙananan sana'o'i fiye da ɗari da ashirin suka samu fitar da kayan da suke sayarwa ga jama'a a babban filin Polo na Jos. Wani abin burgewa da ƙayatarwa a taron shi ne yadda ƴan kasuwar suka fito daga ɓangarori na addini…
Read More
An naɗa Farfesa Sallau sarautar Sarkin Askar Maganin Ƙasar Hausa

An naɗa Farfesa Sallau sarautar Sarkin Askar Maganin Ƙasar Hausa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Farfesa sallau wanda Malami a jami'ar FUDMA da ke Dutsinma yana riƙe da sarautar Sarkin Askan Yarima Katsina Hakimin Safana . Ya kuma taɓa riƙe muƙamin darakta a hukumar raya al'adu na jihar Katsina kafin ya koma jami'ar FUDMA. A kwanakin baya ya taɓa faɗawa manema labarai cewa a matsayin sa na Farfesa bai hana shi sana'ar wanzaci ba. Ni nakewa ɗalibai da malaman jami'ar aski su biyani,"Inji Farfesa. Haka ma ya ce idan iyalan malaman jami'ar suka sami ƙaruwa "ni nake yi wa jaririn aski in cire belu a biya ni"Inji sallau Sarkin askan…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da cibiyar sauƙaƙe kasuwanci ta Katsina

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da cibiyar sauƙaƙe kasuwanci ta Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Haka kuma za a Ƙirƙiri irin wannan ƙananan cibiyoyi a ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina. Cibiya ita ce ta biyu irinta a Najeriya kuma ta farko a matakin jiha da aka kafa domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a ƙasa da waje. Da yake jawabi bayan ƙaddamar da cibiyar, Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan nasara a matsayin mataki nagari da ya daidaita a Katsina da ƙa’idojin kasuwanci na duniya, tare da buɗe sabbin damar bunƙasar tattalin arziƙi da faɗaɗa kasuwanni. Ya ce ƙirƙiro cibiyar ya nuna himmar gwamnati wajen samar da yanayi mai kyau da ya…
Read More
Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Haƙƙin Iyali: Ciyarwa

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako, sannunku da jimirin bibiyar jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan makon, za mu tattauna kan darasin da a wannan zamani ya fi ci wa mata tuwo a ƙwarya tsayin lokaci, musamman ma a ƙasar Hausa. kafin mukai ga tattauna ƙorafin mata kan rashin ciyar da su da mazansu ke yi, bari mu fara kan mazan wanda wataƙila mu samo wata mafita ko fahimta a cikin lamarin. Akwai wani lokaci can bayan a kafar sadarwa ta ɗ wanda a baya aka fi sani da…
Read More
Rawar da kwalliya ke takawa a rayuwar matan Arewa

Rawar da kwalliya ke takawa a rayuwar matan Arewa

Daga AISHA ASAS  Kwalliya ba wai kawai man shafawa ba ce ko fentin leɓe da gashi, a'a, wata hanya ce da mata ke bayyana kansu, suna ƙarfafa gwiwarsu, suna jan hankali da kuma neman girmamawa a cikin al'umma. A Arewacin Najeriya, inda al'adu da addini ke taka muhimmiyar rawa, kwalliya ta samu wani matsayi na musamman. Amma shin me ya sa kwalliya ta zama abin alfahari ga wasu, yayin da wasu ke kallonta a matsayin kwaikwayo ko tsinuwa? A al’adance, mata a Arewa suna amfani da lalle, turare, dilka da man shafawa don ƙawata kansu. Amma zuwan zamani ya kawo…
Read More
Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na 2026

Gwamnan Katsina Dikko Raɗɗa ya sanya hannu a kasafin kuɗi na 2026

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A jawabinsa bayan da ya sanya hannu a kasafin kuɗin ya bayyana cewa kaso 80 bisa ɗari na kasafin kudin zai tafi a wajen manyan ayyuka,sai kuma 18 bisa ɗari zai tafi wajen harkokin yau da kullum. Ya ce wannan kaso shine karo na farko tun kirkiro da jihar Katsina da aka ware kaso na 18 bisa ɗari kan harkokin yau da kullum "tun lokacin gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar'adua yana gwamnan Katsina. Dikko Raɗɗa ya yabawa Yan majalisar dokokin jihar kan yadda suka sadaukar da lokacin wajen tabbatar da komai ya tafi daidai kan…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin madatsar ruwa a Faskari

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin madatsar ruwa a Faskari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan aikin madatsar ruwa da za a fara a garin Sabon Layi da ke ƙaramar hukumar Faskari ya biyo bayan fara samun zaman lafiya a yankin da su kai ta fama da ta'addanci. Aikin, wanda shirin ACReSAL zata ɗauki nauyi, zai samar da ruwa ga dubban mutane dake yankunan tare da haɓaka tattalin arziki ga al'ummar yankin musamman bayan fara samun sauƙi daga iftila'i na rashin tsaro. Da yake ƙaddamar da fara aikin,Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana aikin a matsayin hanyoyin da gwamnati ke bi na dawo da harkokin yau da kullum a yankunan da…
Read More