ukarofi

12687 Posts
‘Yan bindiga sun kashe wata mata tare da sace mutane uku a Kano

‘Yan bindiga sun kashe wata mata tare da sace mutane uku a Kano

' Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Yankamaye da ke cikin ƙaramar hukumar Tsanyawa a Jihar Kano, inda suka kashe wata mata tare da sace wasu mutane uku. Daily Nigerian ta rawaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Asabar, lokacin da mazauna ƙauyen suka riga suka kwanta. Majiyoyi a yankin sun shaida wa jaridar nan cewa ’yan bindigar sun ajiye babur-babur ɗinsu a wajen garin sannan suka shigo a kafa domin guje wa a gano su. A cewar majiyoyin, ’yan bindigar sun harbe…
Read More
Rukunonin makarantun Gidauniyar Isyaka Rabi’u ta yaye ɗalibai 250 

Rukunonin makarantun Gidauniyar Isyaka Rabi’u ta yaye ɗalibai 250 

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano  Makarantar firamare da sakandare da ke ƙarƙashin Gidauniyar Khalifa Isyaka Rabi’u Khadimul ƙur’an ta yaye ɗalibai sama da 250, kamar yadda Babban Jami’in kula da rukunonin makarantun kuma Mataimakin Darakta na mamallakin Jami’ar Khairun ADPO, Malam Rabi’u Shamma, ya bayyana yayin bikin raba kyaututtuka da jawabai da aka gudanar a harabar jami’ar da ke Kano a ƙarshen makon nan. Malam Rabi’u Shamma ya yaba wa ma’aikatan gidauniyar da masu kula da makarantun kan yadda suke aiki da himma. Haka kuma ya jinjinawa ɗaliban da iyayensu da sauran baki da suka halarci taron muhimmanci. A nasa…
Read More
Bajekolin abinci da al’adu na matan Arewa zai bunƙasa tattalin arziki – Magajiyar Zangon Daura

Bajekolin abinci da al’adu na matan Arewa zai bunƙasa tattalin arziki – Magajiyar Zangon Daura

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano  An bayyana cewa shirya taron baje kolin abincin gargajiya da na zamani, tare da nune-nunen al’adun jihohin Arewa 19, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Shahuda Muhammad — Shugabar ƙungiyar ta ƙasa — da Dakta Zubaida Ahmad Nagi — Shugabar ƙungiyar ta Jihar Kano — zai kawo sauyi mai fa’ida a tsakanin matan Arewa da na Nijeriya baki ɗaya. Magajiyar Zangon Daura, Hajiya Jamila Buhari Sani, ta bayyana hakan a taron da ya gudana a Kano a makon da ya gabata. Ta yaba wa dukkan mahalarta taron kan fasahar da suka nuna wajen kawo abinci iri-iri na zamani…
Read More
’Yan siyasa ke ɗaukar nauyin sace-sacen mutane don gurgunta gwamnatin Tinubu – Kalu

’Yan siyasa ke ɗaukar nauyin sace-sacen mutane don gurgunta gwamnatin Tinubu – Kalu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Gwamnan Jihar Abiya kuma sanata yanzu, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa hare-haren kisa, garkuwa da mutane da tashe-tashen hankula da ake fama da su a sassa daban-daban na Nijeriya ba haka nan kawai suke faruwa ba, sai dai tsarin siyasa da wasu ke amfani da shi domin tarwatsa mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A tattaunawarsa a shirin Sunday Politics na gidan talbijin na Channels, Kalu ya ce akwai ’yan siyasa da ke ɗaukar nauyin ’yan ta’adda da ’yan bindiga domin lalata zaman lafiya da kuma gurgunta gwamnatin Tinubu — abin da ya ce ya…
Read More
Tinubu ya amince da ɗaukar sababbin ’yan sanda 30,000

Tinubu ya amince da ɗaukar sababbin ’yan sanda 30,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarni ga Hukumar ’Yan Sanda ta ƙasa da ta fara ɗaukar sababbin jami’ai kimanin 30,000, a wani babban mataki na ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da garkuwa da mutane da suka ƙaru a makonnin baya-bayan nan. Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da al’umma ke ci gaba da fuskantar matsanancin tashin hankali sakamakon hare-haren ’yan bindiga musamman a jihohin Neja, Katsina, Kebbi, Kaduna da Filato — wuraren da rikicin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare. Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa sabon tsarin zai bai wa…
Read More
’Yan sanda sun haramta amfani da ‘knockout’ yayin bikin shigowar sabuwar shekara

’Yan sanda sun haramta amfani da ‘knockout’ yayin bikin shigowar sabuwar shekara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da ake tunkarar lokutan bukukuwan ƙarshen shekara, Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja ta fitar da sabuwar gargaɗi ga mazauna birnin cewa su guji saye ko sayarwa, balle amfani da bangar knockout, da sauran abubuwan fashewa masu ƙara. Wannan gargaɗin na zuwa ne bisa tsoron da rundunar ke nunawa kan yadda irin waɗannan abubuwan ke ƙaruwa a kasuwanni da unguwanni a babban birnin tarayya. A cikin wata takardar manema labarai da Kakakin Rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a Abuja, rundunar ta ce akwai ƙarin damuwa game da yaɗuwar abubuwan fashewa, musamman ganin yadda ake shiga…
Read More
Yadda Tinubu ya sa ido da kansa wajen kuɓutar da ’yan cocin Eruku 38

Yadda Tinubu ya sa ido da kansa wajen kuɓutar da ’yan cocin Eruku 38

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An samu cikakkiyar hujja cewa Shugaba Bola Ahmad Tinubu ne da kansa ya sa ido kan dabarun da hukumomin tsaro suka gabatar, lamarin da ya kai ga nasarar kuɓutar da mambobin cocin Christ Apostolic Church na Eruku 38 da aka yi garkuwa da su a Ifelodun, jihar Kwara. Jami’an DSS suka aiwatar da ceton cikin nasara da misalin ƙarfe 3:20 na ranar Lahadi. Wasu ’yan bindiga da ke ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kai mummunan farmaki a cocin ranar Laraba, inda suka buɗe wuta kan mutane, lamarin da aka yaɗa kai tsaye ta kafafen sada…
Read More
Kotu ta sake ɗage shari’ar Sanata Natasha kan zargin laifin intanet

Kotu ta sake ɗage shari’ar Sanata Natasha kan zargin laifin intanet

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake ɗage ci gaba da shari’ar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan zargin aikata laifin yaɗa bayanan ƙarya ta hanyar intanet, inda ta sanya sabon ranar sauraron shari’ar zuwa 4 ga Fabrairu, 2026. Wannan jinkirin ya faru ne sakamakon rashin halartar alƙalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Mohammed Umar, a zaman da aka shirya gudanarwa ranar Litinin. Tun da farko an ayyana ranar 4 ga Fabrairu, 2025 ne a matsayin ranar fara sauraron shari’ar, bayan jinkirin da aka sha yi a watannin baya, ciki har da ranar 21 ga Oktoba…
Read More
Limamin cocin Birtaniya ya buƙaci a kama Sheikh Gumi bisa zargin tallafa wa ’yan bindiga

Limamin cocin Birtaniya ya buƙaci a kama Sheikh Gumi bisa zargin tallafa wa ’yan bindiga

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani limamin cocin Katolika da ke ƙasar Birtaniya, Nick Donnelly, ya buƙaci Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) da ta fitar da sammacin kama malamin addinin Musulunci na Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi, bisa zargin nuna ra'ayin tausayawa ga ’yan bindiga. Donnelly ya yi wannan kira ne a shafinsa na ɗ a ranar Litinin, yana mai mayar da martani ga sabbin kalaman da Sheikh Gumi ya yi, inda ya musanta zargin cewa ana gudanar da kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ya bazu, Gumi ya ce “Makiyaya ba su kama da…
Read More
NNPC ya samu ribar Naira Tiriliyan 5.4 a 2024

NNPC ya samu ribar Naira Tiriliyan 5.4 a 2024

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya bayyana cewa, ya kammala shekarar 2024 da ribar ta kai tsabar kuɗi har Naira Tiriliyan 5.4, a wani babban ci gaban da ya nuna yadda sauye-sauyen da ake yi a kamfanin ke ƙara tasiri. Shugaban Kamfanin, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya sanar da hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa kamfanin ya samu kuɗaɗen shiga na naira tiriliyan 45.1, wanda ya nuna hauhawar kaso 88 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cewarsa, kuɗin rabo ga masu hannun jarin kamfanin…
Read More