ukarofi

12687 Posts
Da ɗumi-ɗumi: Ministan tsaron Nijeriya ya yi murabus

Da ɗumi-ɗumi: Ministan tsaron Nijeriya ya yi murabus

Daga USMAN KAROFI Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa a daren Litinin. Bayanai daga mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, sun tabbatar da cewa Badaru ya aike da takardar murabus ɗinsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 1 ga Disamba. A cewar takardar, Badaru ya ce dalilin barinsa aiki shi ne “saboda matsalolin lafiyya” da suka fara shafar aikinsa. Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin tare da gode masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa tun daga lokacin da aka naɗa shi a ranar 21…
Read More
Farfesa Barnabas Barde ya gabatar da laccar jami’ar Nasarawa karo na 56

Farfesa Barnabas Barde ya gabatar da laccar jami’ar Nasarawa karo na 56

Daga JOHN D. WADA a Lafia An shawarce masu harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan baki ɗaya su zuba jari sosai a fannin fasahohi domin su taimaka musu wajen ɗorewar harkokinsu na kasuwanci da kuma inganta ayyuka da nasarori. Shawarar ta fito ne daga wani malami a sashen gudanar da kasuwanci na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Farfesa Barnabas Embugus Barde. Farfesan ya kuma shawarce su da su riƙa koyar da ma’aikatansu yadda za su yi amfani da sabbin fasahohin zamani yadda ya kamata, domin taimaka wa kasuwancinsu kawar da tsofaffin dabaru da kuma samun karin yawan aiki cikin…
Read More
SAPZ ta gudanar da ranar nuna fasahar noman shinkafa a Kano

SAPZ ta gudanar da ranar nuna fasahar noman shinkafa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Tarayya ta Najeriya, ta hannun Shirin Kano state Special Agro-Processing Zone (SAPZ) na Jihar Kano tare da haɗin gwiwa da IFAD, ta gudanar da taron ranar nuna fasahar noman shinkafa a Tungar Chiromawa Garin Babba, da ke ƙaramar hukumar Garin Malam, Kano domin tantance ci gaban aikin gona a cikin zagayen bincike na biyu na FGN/SAPZ/IFAD. Babban jami'in SAPZ na jihar Kano, Malam Aminu Iliyasu, ya ce an shirya taron ne domin bai wa manoma damar koyo da ganin sabbin fasahohin noma da za su inganta amfanin gona, tare da rage asarar bayan girbi…
Read More
Ɗaliban Sautus Sunnah 85 sun haddace Alqur’ani a Katsina

Ɗaliban Sautus Sunnah 85 sun haddace Alqur’ani a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Makarantar Sautus Sunnah dake cikin birnin Katsina, sun shirya walimar haddar Alqur'ani Maigirma ga ɗalibai 85, don ƙarfafa ma ɗaliban da kuma ci gaba da yaɗa addinin Allah. Taron wanda ya gudana acikin harabar makarantar dake bayan Water Boad Kofar Ƙaura, ya tara jama'a daban-daban don taya murna. Ɗaliban Maza da Mata su 85 ne suka haddace Alqur'ani Maigirma a makarantar. Da yake jawabi lokacin walimar, shugaban makarantar Malam Aminu Yakubu Musa PhD, ya bayyana jin daɗin sa kan wannan rana da kuma halartar taron wanda shi ne na farko da makarantar ta taɓa shirya…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya shaida haɗarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu

Gwamna Raɗɗa ya shaida haɗarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya shaida munanan haɗuran mota biyu yayin da yake dawowa daga zagayen farko na ziyarar aiki a yankin Funtua. Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan ya kammala tarurruka a ƙaramar hukumar Matazu. Haɗarin farko ya faru ne a cikin garin Matazu, inda ayarin gwamnan ya tarar da wata motar Golf ta kasuwanci da ta yi mummunan haɗari. Motar, wadda ke ɗauke da fasinjoji da dama, mutane huɗu sun rasa rayukansu, yayin da mutane goma suka sami raunuka daban-daban. Gwamna Raɗɗa ya hanzarta bada umarnin a tsaya, ya…
Read More
Ma’aikatan gwamnatin Katsina 1,800 za su koyi kwanfuta na kwanaki uku

Ma’aikatan gwamnatin Katsina 1,800 za su koyi kwanfuta na kwanaki uku

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya ƙaddamar da shirin horas da ma’aikata kimanin 1,800 a kan fasahar kwamfuta, wanda zai gudana na tsawon kwana uku. Hukumar makarantar KSITM wanda suka ɗauki nauyi gudanar da shirin sun sha alwashin bayar da ingantanccen horo ga ma’aikatan domin zamanan tar da aikin gwamnati a faɗin jihar. Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da shirin Alhaji Falalu Bawale ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin ƙarfafa amfani da fasahar zamani, wanda zai taimaka wajen hanzarta aiki, inganta adana bayanai, da kuma rage dogaro…
Read More
Abin takaici ne yadda iyaye ba sa koyawa ‘ya’yansu iya magana – Safiyya Jibril Abubakar 

Abin takaici ne yadda iyaye ba sa koyawa ‘ya’yansu iya magana – Safiyya Jibril Abubakar 

"A da iyaye ba su fiye jan ƴaƴa a jiki ba, yanzu kuwa ya zama wajibi" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A wannan makon muna ɗauke ne da wata tattaunawa da abokin aikinmu Abba Abubakar Yakubu ya yi da wata fitacciyar malamar makaranta, marubuciya, mai aikin faɗakarwa kan tarbiyya da zamantakewar iyali, ƴar gwagwarmayar kula da haƙƙoƙin marayu da raunana. Safiyyah Jibril Abubakar ƴar Jihar Kaduna, wacce ta kasance jajirtacciyar mace ce mai son ganin an samu sauyin halayya tsakanin manya da yara masu tasowa. Burinta a lokacin tana ƙarama bai wuce ta zama likita ba, sai ga shi a maimakon…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin hanya mai tsawon kilomita 27.6 a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin hanya mai tsawon kilomita 27.6 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan ayyuka, Injiniya Sani Magaji Ingawa, ya bayyana cewa titin mai tsawon kilomita 27.6 zai fara ne daga cikin garin Sabuwa ya bi ta Mazare har zuwa Tashar Bawa a ƙaramar hukumar Sabuwa. Injiniya Magaji yayi wannan magana ne lokacin da gwamna Dikko Raɗɗa ke shirin ƙaddamar da aikin hanyar. Ya ce, idan an kammala aikin zai taimaka wajen bunƙasa tsaro, sauƙaƙa jigilar amfanin gona da harkokin sufuri, tare da farfado da tattalin arzikin yankin. Wakilin Sabuwa a Majalisar Dokoki, Hon. Ibrahim Danjuma Macika, ya jinjina wa gwamna bisa wannan aikin, haka ma Shugaban ƙaramar…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta gina hanya a kan Naira biliyan 18.5 a Sabuwa

Gwamnatin Katsina za ta gina hanya a kan Naira biliyan 18.5 a Sabuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da aikin gina hanya mai tsawon kilomita 27.5 daga sabuwa zuwa Rafin Iwa a ƙaramar hukumar Sabuwa. Aikin hanyar da zai ci kuɗi Naira biliyan 18.5 za a kammala shi a nan da watanni 18 kuma da idan an kammala zai haɗa ƙauyuka 50 waɗanda al'ummar su duk manoma ne da zai taimaka masu wajan safarar kayan abinci. Da yake jawabi bayan ƙaddamar da aikin hanya gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewar fara aikin daga cikin alkawarin da yayi a lokacin yana yaƙin neman zaɓe musamman gina hanyoyi a karkara…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya tallafa wa marasa galihu a Funtua

Gwamna Raɗɗa ya tallafa wa marasa galihu a Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na zurfafa shigar al’umma cikin tattalin arziki, ƙarfafa gudanar da mulki a matakin ƙananan hukumomi, tare da tallafa wa gidaje marasa galihu a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar. Da yake jawabi yayin ziyarar haɗe kan Jihar da aka gudanar a Ofishin ƙaramar hukumar Funtua, Gwamna Raɗɗa ya ce sabon zagayen tallafin "ya nuna jajircewarmu na ganin kowace al’umma ta amfana da muhimmin tallafi da zai inganta rayuwa da gina makoma mafi kyau." A cikin shirin tallafin an raba injinan nika 55, injinan ban ruwa 55,…
Read More