ukarofi

12736 Posts
Yobe: Shugaban ƙaramar Hukumar Bade ya yaba wa Gwamna Buni kan cigaba

Yobe: Shugaban ƙaramar Hukumar Bade ya yaba wa Gwamna Buni kan cigaba

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe, Hon. Ibrahim Babagana, ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni na jihar ta Yobe bisa manyan nasarorin da ya samu a fannin bunƙasa ɗan Adam, samar da ababen more rayuwa, noma, ilimi, da kiwon lafiya a faɗin jihar. A wata sanarwa da Babagana ya raba wa jaridar Blueprint a Abuja, ya yi ƙarin haske game da gyaran babbar sakatariyar ƙaramar hukumar Bade, samar da fitilun titi mai amfani da hasken rana, gina cibiyar gudanar da taro, da hanyoyi a matsayin wasu muhimman ayyukan da gwamnan ya yi waɗanda…
Read More
Kotu a Landan ta fallasa tsohon Ministan Abuja kan amfani da bayanan ƙaraya wajen sayen kadara

Kotu a Landan ta fallasa tsohon Ministan Abuja kan amfani da bayanan ƙaraya wajen sayen kadara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An fallasa wani tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Jeremiah Useni, bisa zargin sayan wata kadara a Burtaniya a shekarar 1993 ta hanyar amfani da bayanan ƙarya. Kotun ɗaukaka ƙara ta Landan ta bayyana yadda Useni ya ƙirƙiri bayanan ƙarya shekaru da dama da suka gabata don ɓoye sayan gida mai lamba 79 Randall Avenue, Neasden, Arewacin Landan. Hukuncin kotun, wanda Adam Wren, darektan Open Justice UK, ya raba wa ɗ, ya kuma daƙile yunƙurin mallakar gidan ga Mike Ozekhome, babban lauyan Nijeriya (SAN). A makon da ya gabata ne Kotun ƙoli ta Farko…
Read More
Ta kashe ‘yar uwarta akan bashin N800 A Ondo

Ta kashe ‘yar uwarta akan bashin N800 A Ondo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata ‘yar kasuwa a Akure, babban birnin jihar Ondo, Bosede Iluyemi, ta kashe ƙanwarta mai suna Omowumi Tewogboye kan bashin Naira 800. Manhaja ta ruwaito cewa Bosede ta buƙaci a biya ta kuɗin tumatur da barkono Omowumi da ta saya a kan bashi. Lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali lokacin da ake zargin Bosede ta riƙe kayan Omowumi, wanda hakan ya sa ta faɗi ta kuma samu munanan raunuka. Nan take aka garzaya da Omowumi asibitin da ke kusa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarta da isar ta. Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo…
Read More
DSS ta maka Sowore da Meta a kotu kan cin zarafin Tinubu

DSS ta maka Sowore da Meta a kotu kan cin zarafin Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Tsaron Farin Kaya a Nijeriya DSS, ta gurfanar da fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore a kotu. A ƙunshin ƙarar da DSS ta gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta haɗa da shafukan sada zumunta na ɗ da kuma Facebook, inda take zarginsu da ba da ƙofar aibata Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Daraktan shigar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, M.B Abubakar da wasu lauyoyi huɗu —M.E. Ernest da U.B. Bulla da C.S. Eze da kuma E.G. Orubor, ne suka shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya da kuma…
Read More
Sojoji sun hallaka mayaƙan ISWAP takwas a Borno

Sojoji sun hallaka mayaƙan ISWAP takwas a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sojojin Nijeriya sun kashe aƙalla mayaƙan ƙungiyar ISWAP 8, ciki har da manyan kwamandojinta biyu a Jihar Borno. Wata majiyar leƙen asiri daga rundunar haɗin kai ta OPHK ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’addan ne a wata arangama da suka yi da sojojin a kan hanyar Maiduguri zuwa Baga a safiyar ranar Litinin. A cewar majiyoyin, an yi arangamar ce a kusa da Garin Giwa da ke gab da ƙauyen Kauwa, lokacin da ’yan ta’addan suka yi wa dakarun da ke sintiri kwanton ɓauna. “A yayin wannan artabu, an kashe ’yan ta’adda takwas,…
Read More
Neja: ‘Dole ne malamai su miƙa takardun huɗuba domin samun amincewar gwamnati’

Neja: ‘Dole ne malamai su miƙa takardun huɗuba domin samun amincewar gwamnati’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamna Umar Bago na Jihar Neja ya bayyana cewa wajibi ne a kan masu wa’azi su riƙa miƙa takardun huɗubarsu domin samun amincewar gwamnati kafin su yi wa’azi a jihar. Gwanan ya faɗi hakan ne a cikin wani shiri na gidan talabijin TɓC inda ya fayyace wasu abubuwa na dokar da ke kokarin tsara yadda ake wa’azi a jihar. Gwamnan ya ce, “Ban haramta wa’azi ba, Duk wanda zai yi huɗuba a ranar Juma’a, ya kamata ya kawo takardar da zai yi amfani da shi domin a duba abun da ke ciki, ko a…
Read More
An tsinci gawar wani barasaken gargajiya a Filato

An tsinci gawar wani barasaken gargajiya a Filato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata ƙungiyar Cigaban Kanam (KADA) ta fitar da sanarwar alhini da fushi kan kisan gillar da aka yi wa shugaban unguwar Shuwaka, Malam Hudu Hassan Barau, wanda aka fi sani da Sarkin Shuwaka daga yankin Kyaram, al’ummar Garga a ƙaramar Hukumar Kanam ta Jihar Filato. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Litinin. Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da shi kusan kwanaki shida da suka wuce, inda daga bisani aka kashe shi, kuma aka gano gawarsa a Dajin Wanka a safiyar Litinin 15 ga…
Read More
Fiye da rabin ƙananan yaran Afirka na rayuwa cikin ƙangin talauci – Rahoto

Fiye da rabin ƙananan yaran Afirka na rayuwa cikin ƙangin talauci – Rahoto

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani sabon rahoton bankin duniya da asusun tallafa wa ƙananan yara na Unicef ya nuna cewa a yankin Afirka, kudu da hamadar sahar ƙangin talauci tsakanin ƙananan na ci gaba da ƙaruwa. Rahoton ya ce fiye da rabin ƙananan yaran Afirka na rayuwa cikin ƙangin talauci, inda ya ce yaro guda cikin kowane biyar na rayuwa cikin ƙangin talauci a duniya. To sai dai rahoton - wanda aka fitar a cikin wannan wata na Satumba - ya nuna cewa adadin yaran da ke rayuwa cikin ƙangin talauci ya ragu daga miliyan 507 zuwa 412…
Read More
Wasu makirai na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina — Dangote

Wasu makirai na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina — Dangote

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dangote ya yi zargin cewa wasu miyagun ’yan kasuwan suna shirya maƙarƙashiya domin kashe matatar mansa kamar yadda aka kashe masana’antun tufafin ƙasar nan. Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta ɗangote, Alhaji Aliko ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa. Dangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar. Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur…
Read More
Tallafin ayyuka: Kungiya ta roƙi Tinubu ya shiga tsakaninta da EFCC a Kaduna

Tallafin ayyuka: Kungiya ta roƙi Tinubu ya shiga tsakaninta da EFCC a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata ƙungiyar bayar da tallafi mai suna United Charity Foundation (UCF) tare da haɗin gwiwar Formal Act Legacy Ltd ta roƙi Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani a tsakaninta da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC da kuma wasu jami’an jihar Kaduna. A cewar ƙungiyar, shiga tsakani na shugaban ƙasar zai taimaka wajen magance rikicin da kuma haifar da ci gaba da "aiwatar da shirin ci gaban al'umma da aka ba da tallafi a faɗin ƙananan hukumomi 774 na ƙasar." A wata buɗaɗɗiyar wasiƙa…
Read More