Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamna Umar Bago na Jihar Neja ya bayyana cewa wajibi ne a kan masu wa’azi su riƙa miƙa takardun huɗubarsu domin samun amincewar gwamnati kafin su yi wa’azi a jihar.
Gwanan ya faɗi hakan ne a cikin wani shiri na gidan talabijin TɓC inda ya fayyace wasu abubuwa na dokar da ke kokarin tsara yadda ake wa’azi a jihar.
Gwamnan ya ce, “Ban haramta wa’azi ba, Duk wanda zai yi huɗuba a ranar Juma’a, ya kamata ya kawo takardar da zai yi amfani da shi domin a duba abun da ke ciki, ko a Saudiya ma ana yin hakan.”
“Ba za mu ce saboda an ba ka dama ka zama malami, za ka fita ka yi wa’azi wanda zai saɓawa mutane ko gwamnati ba.” gwamnan ya ƙara da cewa.
“Saboda haka ne muke son mu ga abin da takardar wa’azin ya ƙunsa, abin da za a faɗi kuma muna aiki tare da hukumomin tsaro na DSS da ‘yan sanda da NSCDC da sojoji.” inji gwamnan.
Wannan mataki da aka fara bayyanata ga bainar jama’a a farkon watan nan ya janyo ce-ce-ku-ce.
