ukarofi

12736 Posts
Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya ce Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba shi da burin da ya wuce na tara haraji tun yana Gwamna a Legas. Adebayo ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. A cewarsa, “Kowa ya san cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sananne ne wajen karbar haraji. Amma wannan tsarin karɓar haraji ya fi tsarin da ya tarar da shi wanda ba shi da tsari. “Ya yi hakan a Legas,…
Read More
Gwamnan Katsina ya taya Maryam Idris murnar zama wakiliyar Nijeriya a OPEC

Gwamnan Katsina ya taya Maryam Idris murnar zama wakiliyar Nijeriya a OPEC

ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya taya Maryamu Idris murnar nada ta a matsayin Wakiliyar Najeriya a OPEC. Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Muhammad kaula ya fitar. Maryamu, ‘yar asalin Jihar Katsina ce, kuma ita ce daraktar janar na NNPC Trading Limited. Gwamna Raɗɗa ya bayyana wannan muƙami a matsayin shaida ta ingancin ƙwararrun da Katsina ke samarwa domin hidima ga ƙasa da ma duniya baki ɗaya. “Muna alfahari da ganin ‘yar Katsina ta samu damar wakiltar Najeriya a…
Read More
Gwamnatin Norway da UNFPA tare da CERSDOV sun faɗaɗa yaƙi da cin zarafi a Akko da Billiri

Gwamnatin Norway da UNFPA tare da CERSDOV sun faɗaɗa yaƙi da cin zarafi a Akko da Billiri

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Cibiyar nazari da magance matsalolin cin zarafi a gida (CERSDOV), tare da goyon bayan Gwamnatin Norway da asusun raya jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA), ta faɗaɗa yaƙin wayar da kai kan ’yancin lafiyar haihuwa (SRHR) da kuma yaƙi da cin zarafin mata (GBV) zuwa ƙananan hukumomin Akko da Billiri a Jihar Gombe. A yayin taro da kungiyoyin mata a Kumo, babban mai bincike na CERSDOV, Dokta Hussaini Momoh Lawal, ya bayyana cewa wannan ziyartar ta ƙunshi duba tasirin shirye-shiryen da aka aiwatar a matakin al’umma, bayan jerin horo da aka gudanar tare da…
Read More
Sanata Marafa ya bar APC ne saboda gazawar Shugaba Tinubu – Maikatako

Sanata Marafa ya bar APC ne saboda gazawar Shugaba Tinubu – Maikatako

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau An bayyana ficewar Sanata Kabiru Garba Marafa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara a baya-bayan nan, ya biyo bayan gazawar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen sa, musamman alƙawarin da ya yi na kawo ƙarshen rashin tsaro da ya addabi jihar. Alhaji Surajo Garba Maikatako, Shugaban Majalisar ƙoli ta ƙungiyar Sanata Marafa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Juma’a. Ya ci gaba da cewa, ficewar Sanata Kabiru Garba Marafa daga jam’iyyar APC a…
Read More
CERSDOV ta faɗaɗa yaƙi da cin zarafin mata a Akko da Billiri

CERSDOV ta faɗaɗa yaƙi da cin zarafin mata a Akko da Billiri

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Cibiyar nazari da magance matsalolin cin zarafi a gida (CERSDOV) ta faɗaɗa wayar da kai kan ’yancin lafiyar haihuwa da yaƙi da cin zarafin mata zuwa ƙananan hukumomin Akko da Billiri a Jihar Gombe, tare da tallafin gwamnatin Norway. A yayin taro da ƙungiyoyin mata a Kumo, babban mai bincike na CERSDOV, Dokta Hussaini Momoh Lawal, ya ce ziyartar na nufin duba tasirin horon da aka gudanar a matakin al’umma, tare da ƙarfafa mata su karya shingayen al’ada domin kare kansu da ’yan mata masu tasowa. Jakadiyar CERSDOV wacce kuma lauya ce a ma’aikatar…
Read More
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara na tallafa wa iyayen ‘yan uku

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara na tallafa wa iyayen ‘yan uku

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Uwargidan gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta tallafawa iyalan da suka haifi ‘ya’ya uku da aka haifa kwanan nan a garin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau. A cewar sanarwar da sakatariyar yaɗa labaran uwargidan gwamnan, Rabi Yusuf ta fitar, ta ce an tallafawa iyayen da tallafin magunguna, kayan abinci, diapers, tallafin kuɗi da sauran muhimman abubuwa domin sauƙaƙa nauyin kula da jariran. Suma a nasu ɓangaren, Iyayen ‘yan ukun Iliyasu Nuhu Mada da Aina’u Musa sun yabawa uwargidan gwamnan bisa kulawa dasu, inda suka bayyana hakan a matsayin wani babban ƙwarin gwiwa…
Read More
NCDC ta fitar da sanarwa kan zargin cutar Ebola a Abuja

NCDC ta fitar da sanarwa kan zargin cutar Ebola a Abuja

Daga USMAN KAROFI a Abuja Hukumar NCDC ta ƙasa ta bayyana cewa an yi gwaji kan mutum biyu da ake zargin suna ɗauke da cutar Ebola da Marburg a Abuja, amma sakamakon ya nuna cewa babu wanda ya kamu da cututtukan. Hukumar ta ce, duk da haka, ana ci gaba da gudanar da bincike kan wasu cututtukan zazzaɓin j Lassa da dengue. Shugaban NCDC, Dakta Jide Idris, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a domin kwantar da hankulan jama’a bisa raɗe-raɗin ɓullar cutar Ebola a babban birnin tarayya. Daga cikin waɗanda aka yi wa gwaji akwai…
Read More
Jaridar yanar gizo: Aikin jarida a yanar gizo da ɗan soshal midiya, tarihi, asali da bambancinsu

Jaridar yanar gizo: Aikin jarida a yanar gizo da ɗan soshal midiya, tarihi, asali da bambancinsu

Daga ƊANJUMA KATSINA Masana tarihi sun ce aikin jarida ya faro ne daga halittar ɗan'adam wato neman sani, neman ilmi a kan wani abu faɗakarwa da nishaɗantarwa. Aikin jarida bisa tsari na farko an fara shi ne da hawa bisa wani tudu a ba da labari, inda wani mutum kan hau, jama'a su kewaye shi yana ba da labari ko na faruwar wani lamari, ko na nishaɗi, ko na an kararwa a kasuwanni ko wajen taruwar jama'a. Matakin aikin jarida na biyu shi ne wanda aka fara a takarda, wanda ake ce wa jarida. Mataki na uku shi ne na…
Read More
Rasha ta ƙara haddasa fargaba yayin da ta shigar da jiragen yaƙi Turai

Rasha ta ƙara haddasa fargaba yayin da ta shigar da jiragen yaƙi Turai

Gwamnatin Burtaniya ta sanar da aika jiragen yaƙi zuwa Poland domin shiga sabon shirin NATO mai suna “Eastern Sentry.” Wannan shiri na zuwa ne bayan rahotannin da ke nuna cewa jiragen drone daga Rasha na ta shiga sararin sama na Poland da Romania. Rahotanni daga The Guardian sun nuna cewa wannan mataki na NATO ya zama gargaɗi ga Rasha cewa ba za a lamunci keta doka ba. Ministan tsaron Burtaniya, Grant Shapps, ya ce jiragen nasu ba don tada hankali ba ne, sai don tabbatar da kariya ga ƙasashen mambobi. Sai dai wasu masana sun yi gargaɗin cewa wannan na…
Read More
Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu, inji wasu ‘yan APC a Jihar Nasarawa

Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu, inji wasu ‘yan APC a Jihar Nasarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a mazaɓar Agyaga da ke jihar Nassarawa sun mara wa Shugaban ɓasa Tinubu baya kan neman wa’adin mulki na biyu da neman gwamna Abdullahi Sule ya tsaya takarar Sanata 2027. Sannan sun goya wa takarar Dr Jeremiah Umaru, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Akwanga/Nassarawa Eggon/Wamba da Larry ɓen-Bawa mai wakiltar Akwanga ta Arewa a neman wa’adi na biyu saboda irin abubuwan da suka cimma. Mista Monday Magaji, kansilar mazaɓar Akwanga kuma shugaban kungiyar kansiloli ne ya bayyana haka a ranar Litinin a yayin taro na masu…
Read More