ukarofi

12736 Posts
Taron FAO: Ministan kasafi ya nemi ‘yan ɓasashen waje da su zuba jari a fannin noma

Taron FAO: Ministan kasafi ya nemi ‘yan ɓasashen waje da su zuba jari a fannin noma

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yi kira da a zuba jari mai ɓarfi na ɓasa da ɓasa a fannin noma da bunɓasa ban-ruwa a Nijeriya, inda ya bayyana ɓasar a matsayin wuri mafi cancanta a duniya wajen saka hannun jari a harkar noma a wannan zamani. Ya bayyana haka ne a wajen Bikin Buɗe FAO National & Sub-Regional Hand-in-Hand Inɓestment Forum to Enhance Agricultural Inɓestment in West Africa and the Sahel, inda Mataimakin Shugaban ɓasa, Maigirma Sanata Kashim Shettima, ya kasance baɓo na musamman na girmamawa. Sanata Bagudu…
Read More
 2027: Hana wasu yin takara da Tinubu a Jam’iyyar APC ba daidai ba ne — ACF

 2027: Hana wasu yin takara da Tinubu a Jam’iyyar APC ba daidai ba ne — ACF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Nijeriya, ACF ta yi watsi da kalaman da ke cewa babu wanda zai fito ya yi takara da Shugaba Tinubu a jam'iyyar APC a zaɓen 2027. ƙungiyar ta ce 'yan arewacin ƙasar na da damar fitowa takara duk da cewa wasu shugabannin APC a yankin sun goyi bayan takarar shugaban ƙasar. ACF, ta ce waɗannan kalamai sun saɓawa kundin tsarin mulkin Nijeriya, kuma irin waɗannan kalamai bai kamata su riƙa fitowa daga bakin waɗanda ake yi wa kallon yi wa shugabanni ba. Farfesa Tukur Muhammad Baba, shi ne mai magana…
Read More
Saudiyya ta saki ‘yan Nijeriya da aka zarga da safarar miyagun ƙwayoyi

Saudiyya ta saki ‘yan Nijeriya da aka zarga da safarar miyagun ƙwayoyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumomin Saudi Arabia sun saki wasu 'yan Nijeriya uku da aka tsare a Jidda, bayan an zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi. Mutanen da aka saka su ne Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abdulhamid Saddieƙ. Wasu gungun mutane da ke aiki a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Mallam Aminu da ke Kano (MAKIA) ake zargi da manna sunayen mutanen uku a wasu akwatuna da ke ƙunshe da miyagun ƙwayoyin. Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA ce ta sanar wa manema labarai batun sakin mutanen uku. Unda…
Read More
Gwamnatin Sakkwato ta ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa na zamani a jihar

Gwamnatin Sakkwato ta ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa na zamani a jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin jihar Sakkwato ta ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa masu ɗaukar mutum 20 da rigunan kariya 2,000 a yankunan jihar da ke kusa da koguna. Yayin ƙaddamar da aikin a garin Dundaye da ke yankin ƙaramar hukumar Wamako, gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa da ɗauki matakin ne da nufin kare lafiya da dukiyoyin al'ummomin jihar da ke rayuwa a kusa da koguna. Gwamnan ya ce matakin zai taimaka wajen inganta lafiyar sufurin ruwa da nufin rage yawan hatsuran da ake yawan samu a kwale-kwale a gokuna da tafkunan jihar. Ya ƙara da…
Read More
Yadda gwamnatin tarayya ta raba mata sama da 1600 da larurar yoyon fitsari – NHIA

Yadda gwamnatin tarayya ta raba mata sama da 1600 da larurar yoyon fitsari – NHIA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Akwai mata sama da 1600 da aka yi wa aiki da ke fama da larurar yoyon fitsari a ƙarƙashin hukumar inshoran lafiya ta ƙasa na shirin aikin yoyon fitsari kyauta (FFP) da gwamnatin tarayya ke yi. Dr Saka Agboola, shugaban sashen tabbatar da ingancin aiki na hukumar inshoran lafiya ta duniya (NHIA) ne ya tabbatar da hakan a cikin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Ilorin a ranar Litinin. Agboola ya ce, manufar shirin gwamnatin tarayya ita ce yin tiyata kyauta da shigar da mata cikin tsarin inshorar lafiya. “Gwamnatin Nijeriya…
Read More
Yaƙi da cutar mantuwa a Nijeriya

Yaƙi da cutar mantuwa a Nijeriya

Wani bincike na masana ya nuna cewa ’yan Nijeriya na cikin waɗanda suka fi fama da ciwon mantuwa a duniya. Ciwon mantuwa da ake kira ‘dementia’ na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil’adama. Kungiyar da ta gudanar da binciken mai suna Alzheimer’s Disease International ta ce, sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba. Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma waɗannan alƙaluma sun fi yawa a ƙasashen Nijeriya da Indiya da kashi 90 cikin…
Read More
Tinubu ya gaji ruɓaɓɓen tattalin arziki ne daga Buhari, inji Yakubu Dogara

Tinubu ya gaji ruɓaɓɓen tattalin arziki ne daga Buhari, inji Yakubu Dogara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban hukumar tallafa wa masu neman bashi ta ƙasa (NCGC), Yakubu Dogara, ya ce, Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya gaji matsalar tattalin arziƙi ne a lokacin da ya kama mulki a watan Mayun 2023 wanda shi ne dalilin da ya tilasta masa ƙaddamar da sauye-sauye domin guje rugujewar ƙasar nan. Dogara ya bayyana haka ne a ranar Talata a Abuja a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron ƙaddamar da lakca kan ‘yan majalisa da aka yi wa take da: “Fahimtar sauye-sauyen haraji a Nijeriya: ƙarin haske game da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu.”…
Read More
Tallafin kayan haihuwa ya kai ga mata masu ciki 400 a Gombe

Tallafin kayan haihuwa ya kai ga mata masu ciki 400 a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙaramar hukumar Gombe ta raba kayayyakin haihuwa kyauta ga mata masu juna biyu 400, a wani shiri na musamman da aka ƙaddamar domin inganta lafiyar uwa da jariri tare da rage mace-macen da ke faruwa a lokacin haihuwa. An gudanar da bikin rabon ne a cibiyar haihuwa ta Gombe, inda shugaban ƙaramar hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna (Wakilin Arewan Gombe), ya jagoranci ƙaddamarwar. A jawabin sa, Haruna ya bayyana cewa shirin ya yi daidai da umarnin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ƙarfafa kiwon lafiya a matakin farko, musamman wajen kula da mata masu juna…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta raba biliyan N330 ga magidanta 8.1 a Nijeriya – Ministan Kuɗi

Gwamnatin Tarayya ta raba biliyan N330 ga magidanta 8.1 a Nijeriya – Ministan Kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta raba jimillar Naira biliyan 330 ga magidanta miliyan 8.1 a faɗin Nijeriya a ƙarƙashin shirin tallafin kuɗi (National Social Safety Net Programme), wanda aka ƙirƙiro domin rage wa marasa galihu raɗaɗin sauye-sauyen tattalin arzikin ƙasar. Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, bayan wata ganawa da Kwamitin Musamman na Shugaban ƙasa kan ɗaukar nauyin Jinƙai, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa a watan Fabrairu. Edun ya bayyana cewa shirin, wanda ya fuskanci jinkiri a farkon…
Read More
Sanatan Kano ta tsakiya ya ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 300 a ƙaramar Hukumar Dala

Sanatan Kano ta tsakiya ya ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 300 a ƙaramar Hukumar Dala

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Sanatan Kano ta Tsakiya Hon. Rufa'i Sani Hanga ya ƙaddamar da aikin yin wata sabuwar hanya mai tsawon kilomita 300 a mazaɓar Gobirawa  a yankin ƙaramar Hukumar Dala. Sanatan ya yi kira ga al'ummar yankin kan su baiwa ma'aikata da za su yi aikin cikakken goyon baya da haɗin kai a yayin da suke gudanar da aikin. Sanata Rufa'i Sani Hanta ya ce alummar yankin ne suka zo masa da buƙatar a yi wannan aikin ba hanya ya gode wa Allah da ya bashi dama ya zo don ƙaddamar da aikin yana fatan Allah ya…
Read More