ukarofi

12736 Posts
Yadda Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓacin Jihar Ribas

Yadda Tinubu ya kawo ƙarshen dokar ta-ɓacin Jihar Ribas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A watan Maris ɗin 2025 ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas bayan ya bayyana cewa rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da majalisar dokoki ya jawo “durƙushewar mulki gaba ɗaya.” Tinubu ya ce, rikicin ya taɓa manyan kadarorin tattalin arzikin jihar, musamman bututun mai da ake lalatawa, abin da ya sanya dole ya dakatar da gwamnati da majalisar dokoki na tsawon watanni shida. A lokacin, ya naɗa tsohon shugaban sojojin ruwa, ɓice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), a matsayin shugaban riƙon ƙwarya domin tafiyar da jihar mai arzikin mai. Shugaba Bola Tinubu ya ce,…
Read More
Yadda taƙaddamar Ɗangote da NUPENG ta ke ƙazancewa

Yadda taƙaddamar Ɗangote da NUPENG ta ke ƙazancewa

*Rikicin zai iya tsorata masu son zuba jari a Nijeriya, a cewar masana *Kotu ta yi allawadai da umarnin rufe Matatar ɗangote Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin rukunin kamfanonin ɗangote da ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Iskar Gas ta Nijeriya, NUPENG a taƙaice. Wannan sabon rikici ya ɓarke ne kwanaki bayan hukumar DSS ta jagoranci sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu, kan ƙungiyanci a matatar Dangote. Rikicin ya kunno kai ne bayan an umarci direbobin motocin mai na MRS da su cire tambarin ƙungiyar NUPENG da aka manna a motocinsu. Wannan mataki ya fusata shugabannin ƙungiyar NUPENG, inda…
Read More
Mai Tajul’izzi ya halarci gayyatar da Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta yi masa

Mai Tajul’izzi ya halarci gayyatar da Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta yi masa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Biyo bayan gayyatar Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'ia ta Jihar Kano ta yiwa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi da lauyansa Abba Hikima kan muhawarar da suka gudanar ba tare da sanin ta ba, Shehi Mai tajul'izzi ya amsa gayyatar Hukumar tare da rakiyar lauya Abba Hikima. Ta cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar Sani Abdullahi ya aikewa Blueprint Manhaja da yammacin Alhamis, ya ce, zaman da ya gudana a harabar hukumar, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi dokokin hukumar wanda ya haɗa da alaƙar aikin hukumar da su sha'irai,…
Read More
Gwamna Dikko Raɗɗa ya raba tallafin Naira Miliyan 102 ga matasa don inganta noma

Gwamna Dikko Raɗɗa ya raba tallafin Naira Miliyan 102 ga matasa don inganta noma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya raba tallafin naira miliyan 102 ga matasa 102 da suka kammala samun horo a cibiyar noma ta Songhai da ke ƙaramar hukumar Dutsinma a Jihar Katsina. Kowanne ɗalibi daga cikin ƙananan hukumomin 34 ya samu naira miliyan ɗaya a matsayin jari, bayan sun kammala samun horo na watanni shida. Sun sami horo a ɓangaren kiwon kaji, kifi, noma, sarrafa ƙasa, kiwon dabbobi, lambu da fasahar samar da iskar gas daga shara. A jawabin sa wajen taron, Gwamna Raɗɗa ya bayyana shirin a matsayin “juyin juya hali a tarihin…
Read More
Jihar Kano ta zama zakara a jarrabawar NECO ta bana

Jihar Kano ta zama zakara a jarrabawar NECO ta bana

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi ne ya bayyana haka a garin Minna babban birnin jihar Neja yayin da yake sanar da sakamakon jarrabawar ta wannan shekara ta 2025. Farfesa Wushishi ya ce ɗalibai 68,159 ne suka samu kiredit biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi daga Jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya. Sai Jihar Legas da ke biye mata da ɗalibai 67,007, a inda Jihar Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 48,742. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar,…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya umarci hukumar jin daɗin alhazai ta wayar da kan jama’a

Gwamna Raɗɗa ya umarci hukumar jin daɗin alhazai ta wayar da kan jama’a

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan ya jaddada cewa dole ne a yi amfani da duk hanyoyin sadarwa da ake da su—rediyo, talabijin, kafafen sada zumunta, da tarukan al’umma—don isar da saƙon ga maniyyata a faɗin jihar domin su fara rajistar aikin hajji da wuri. Haka kuma ya roƙi malamai su yi amfani da huɗubobinsu da karatuttukansu wajen tunatar da al’umma a masallatai kan buƙatar yin rajista da wuri. Gwamna Raɗɗa ya bayar da wannan umarni ne lokacin da ya karɓi shugaban hukumar hajji na ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman Saleh Pakistan, wanda ya jagoranci tawagar manyan jami’an hukumar a…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da wutar sola a Asibitin Aminu Kano

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da wutar sola a Asibitin Aminu Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO), gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da megawatt bakwai (7MW) na wutar sola a asibitin. Yayin bikin ƙaddamar da aikin a Kano a jiya Laraba, shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Wakilai, kuma ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi, Abubakar Bichi, ya bayyana cewa an ware fiye da naira biliyan 12 domin aikin, wanda ake sa ran zai baiwa asibitin wutar lantarki ba tare da dogaro da tsarin wutar lantarki ta ƙasa ba.…
Read More
Magidanci da matarsa da ɗiyarsa sun kuɓuta bayan biyan Naira miliyan 50

Magidanci da matarsa da ɗiyarsa sun kuɓuta bayan biyan Naira miliyan 50

Daga UMAR GARBA a Katsina Matashin ɗan kasuwa a Katsina, Anas Ahmadu da matarsa Halimatu mai ɗauke da juna biyu wata bakwai da ɗiyarsu mai shekaru biyu da aka yi garkuwa da su, sun shaƙi iskar ‘yanci. An sako mutanen ne a daren ranar Laraba bayan sun shafe kwanaki 21 a tsare a hannun 'yan bindiga, kamar yadda wani ɗan uwan iyalan ya tabbatar wa manema labarai. Ɗan uwan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an biya kuɗin fansa naira miliyan 50 domin a sako su. “Alhamdulillah! A daren nan masu garkuwa da su sun sako Anas,…
Read More
Laifin Ɗanfodiyo ga ’yan kwangila, wargaza gungun mushurkai

Laifin Ɗanfodiyo ga ’yan kwangila, wargaza gungun mushurkai

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Duk wanda ya tsaya kai da fata don kafa wani abun alheri don amfanin bani-adama za ka taras ya taka kafar miyagun iri da ke amfana da abubuwan da a ka kawar na kazanta da son zuciya. Ga ma misalai a nan cikin Afurka in mun duba Nelson Mandela a Afurka ta kudu da ya taso da yunƙurin yakar nuna bambancin launin fata daga turawa an yi wuf a ka jefa shi gidan yari a Robins Island na tsawon shekaru 27 amma ya fito daga ƙarshe ya samu nasarar zama shugaban ƙasar bayan rugujewar mulkin wariya.…
Read More
Wane ne miji nagari?

Wane ne miji nagari?

Daga AISHA ASAS  (Ci gaba daga makon jiya) Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.  Idan ba a manta ba, a satin da ya gabata, mun kawo wa masu karatu alamomin miji nagari har guda shida, inda muka yi alƙawarin ƙaro wasu a wannan makon. 7. Shi ne wanda yake son sanin ababen da yake yi wa matarsa da ba ta so: Ya ba ta dama ta zayyana mishi ababen da ke ɓata ranta da yake yi. Sannan ya ba ta hankalinshi yayin sauraron ta. Ka da ya katse ta har…
Read More