ukarofi

12736 Posts
Dakta Daudu ya nemi samar da maganin cizon maciji a gida

Dakta Daudu ya nemi samar da maganin cizon maciji a gida

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar masana ilimin guba ta Najeriya (TSN), Dakta Ibrahim Jalo Daudu, ya buƙaci gwamnati ta ƙara himma wajen samar da maganin cizon maciji a cikin gida domin rage tsada da dogaro da ƙasashen waje. Dakta Jalo Daudu ya yi wannan kira ne a taron zauren kimiyya karo na biyu na TSN da aka gudanar a Gombe, mai taken: “Binciken Hanyoyin Samar da Maganin Cizon Maciji na Gargajiya da Na Zamani a Najeriya: Manufofi, Ƙalubale da Dama.” Ya ce zaɓen Gombe a matsayin wurin taron ya dace ƙwarai, ganin yadda jihar…
Read More
JIBWIBS ta sanar da rasuwar daraktan agaji na Jihar Katsina

JIBWIBS ta sanar da rasuwar daraktan agaji na Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar Izalatul bidi'a wa Iƙamatul sunnah reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya sanar da rasuwar Alhaji Abdullahi Na Bakori wanda shine Daraktan Agaji na ƙungiyar a jihar Katsina. Sheikh Yakubu Musa ya ce marigayi Abdullahi Bakori ya rasu ne bayan yayi fama da jinya. Ya bayyana marigayi a matsayin jajirtacce da sadaukar da kai wajen aikin sa. "Marigayi Abdullahi Bakori mutum ne mai natsuwa da sanin yakamata ya kuma sadaukar da kai wajen aikin Allah,"Inji Sauttus sunnah. Sheikh Yakubu Musa Sauttus sunnah ya roƙi Allah SWT ya jiƙan shi, ya gafarta ma…
Read More
Kwamitin ganin an ƙirƙiro Jihar Karaɗua zai fara taron gangamin wayar da kan jama’a

Kwamitin ganin an ƙirƙiro Jihar Karaɗua zai fara taron gangamin wayar da kan jama’a

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamitin yunƙurin ganin a ƙirƙiro karaɗua a Jihar Katsina ta shirya fara taron gangamin wayar da kan jama'a a cigaba da fafutukar ganin an ƙirƙiro jihar. Shugaban kwamitin Alhaji Kabir Aliyu Maskan ya sanar da haka a wani taro da yayi da ya'yan kwamitin a Katsina Ya nuna cewa akwai buƙatar kwamitin ya fito da wasu sabbin tsare-tsare na ilmantar da al'ummar yankin karaɗua game da wannan buƙata na ganin a ƙirƙiro jihar daga cikin Jihar Katsina. Kabir Aliyu ya bayyana cewa wannan yunkuri na neman ƙirkiro Jihar karaɗua an fara shi ne shekaru da…
Read More
Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da fararen hula sama da 10 a Zamfara

Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da fararen hula sama da 10 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu ‘yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a garin Maru ƙaramar hukumar Maru a Zamfara, inda suka kashe wani matashi da akafi sani da Attahiru Abubakar. Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa wakilinmu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 2:00 na daren yau. Ya ce, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da iyalan marigayi Attahiru tare da wasu mutane tara a yayin harin. Jaridar Blueprint Manhaja ta rawaito cewa ƙaramar hukumar Maru na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga suka…
Read More
Sharhin littafin ‘Duhun Damina’

Sharhin littafin ‘Duhun Damina’

Daga BAMAI ALHAJI DABUWA Sunan Marubuciya: Maryam Abdul. Shekarar Bugu: Babu. ISBN: 978-978-982-968-4. Mai Sharhi: Bamai Dabuwa. Lambar Waya: 07037852514. Gabatarwa/Abubuwan Burgewa: Littafin 'Duhun Damina' littafi ne da aka yi amfani da wani irin salo mai kama da tafiyar kura. Shi ne littafin da ya kawo zunzurutun kuɗi sama da miliyan guda a ranar da aka ƙaddamar da shi. Littafin ya taɓo wata matsala da kusan kowa ke tsoron taɓawa saboda gudun tambayar kai ta ya aka yi ka sani? Wasu kuma hankalinsu bai kai wajen ba, musamman iyaye, amma kuma rayuwar 'ya'yansu ce dumu-dumu a ciki. Littafi ne da…
Read More
Zan fi zaɓar in kasance da gaskiya fiye da in birge mutane – Shakespeare

Zan fi zaɓar in kasance da gaskiya fiye da in birge mutane – Shakespeare

“Komai yana da lokacinsa, kuma duk abin da ke faruwa yana faruwa bisa dalili” Daga AISHA ASAS  A cikin tarihin adabin duniya, babu wani suna da ya fi girma da ƙayatarwa fiye da William Shakespeare. An san shi da ƙwarewa mai zurfi a fagen rubuce-rubuce, wasan kwaikwayo, da waƙa, inda ya haifar da wani gagarumin sauyi a harshen Ingilishi da kuma yadda ake fahimtar ɗabi'ar ɗan adam. Shakespeare ba kawai marubuci ba ne, domin ya kasance wani ginshiƙi ne da ya sauya fasalin adabi gabaɗaya. Rubuce-rubucensa sun ci gaba da rayuwa fiye da shekaru ɗari huɗu, kuma kalmominsa sun ratsa…
Read More
Matsalar tsaron Katsina ta ragu da kaso 70 – Gwamnatin Katsina

Matsalar tsaron Katsina ta ragu da kaso 70 – Gwamnatin Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce an samu raguwar ayyukan ta’addanci da kaso 70 a faɗin jihar, biyo bayan ɗaukar muhimman matakai wajen kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar sassan ta. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr. Nasir Mu’azu ne ya bayyana haka yayin wani muhimmin taron bayar da rahoton halin da ake ciki kan tsaro, wanda gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya shirya. Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar, ta bayyana cewa irin matakan da gwamnatin ke ɗauka ya sanya da yawa daga cikin jagororin ‘yan bindiga ajiye makamansu tare da neman a yi…
Read More
Gwamnatin Katsina ta amince da kashe Naira miliyan 372 na kuɗin tallafin karatu

Gwamnatin Katsina ta amince da kashe Naira miliyan 372 na kuɗin tallafin karatu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar bayar da tallafin Karatu ta Jihar Katsina (Scholarship Board) ta sake kafa wani tarihi ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Dikko Raɗɗa inda ya amince da naira ₦372,051,176.00 a matsayin tallafin karatu ga ɗalibai 24,452 masu karatu a makarantun gaba da sakandire ƴan asalin jihar Katsina. Sanarwar hakan na ƙunshe a cikin wata takarda da babban sakataren hukumar Dakta Aminu Salisu Tsauri, ya sanya ma hannu. Sanarwar ta cigaba da cewa; gwamnatin Dikko Raɗɗa ta biya kuɗin tallafin karatu fiye da Naira biliyan biyu ga dalibai 174,471. Hukumar ta ce nan ba da jimawa ba za a…
Read More
Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da muƙabalar mawaƙan addini

Hukumar tace finafinai ta Kano ta dakatar da muƙabalar mawaƙan addini

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muhawara a tsakanin mawaƙan addini, tare da gayyatar Usman Maidubun Isa, Shehi Mai Tajul’izzi da sauran wanda suka jagoranci muhawarar tasu dasu bayyana a gabanta a ƙasa da awa 24. A wani yunƙuri na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da bin doka tsakanin mawaƙa ɓangaren nishadi da na addini, shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta Jihar Kano, Alh. Abba El-Mustapha, ya sanar da haramta duk wani nau'in muhawara daga mawaƙan addini a Jihar Kano, ba tare da izinin hukumar ba. Ta…
Read More
Tallafawa matasa ne zai kawo ƙarshen ta’addanci a Katsina – Sardaunan Funtua

Tallafawa matasa ne zai kawo ƙarshen ta’addanci a Katsina – Sardaunan Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sardaunan Funtua Alhaji Aƙilu Hassan Muhammad ya ce tallafawa matasa ne kawai zai kawo ƙarshen ta'addanci da sauran miyagun ɗabi'u a Katsina. Alhaji Aƙilu wanda shine shugaban kamfanin sarrafa ƙarafa na NAK yayi wannan magana a garin Funtua a yayin da yake ganawa da manema labarai. Ya bayyana cewa ganin yadda a ke samun yawaitar matasa a jihar,ya zama wajibi gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su ɓullo da hanyoyin tallafawa matasa domin a sami raguwar aikata ta'addanci da sauran miyagun ɗabi'u da ke addabar musamman kudancin jihar. Aƙilu wanda ya aiwatar da shirye…
Read More