16
Sep
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ranar Asabar 13 ga watan Satumban 2025 makusantan tsohon shugaban jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma ta Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi sun gudanar da gagarumin taron murna da farin cikin kammala aiki lafiya tare da karrama shugaban rukunin jami’oin Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da lambar yabo. Gagarumin bikin wanda aka gudanar da shi a babban ɗakin taro na kwalejin ilimi na Tarayya (FCE) Bichi ya samu halartar ɗimbin masoya daga ko’ina a faɗin Nijeriya. Farfesa Abubakar Adamu Rasheed tsohon shugaban Hukumar dake kula da jami’oin ƙasa (NUC), a yayin…
