ukarofi

12736 Posts
Kwastom ta cire harajin shigo da kayan da ba su wuce Dala 300 ba

Kwastom ta cire harajin shigo da kayan da ba su wuce Dala 300 ba

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCSB), ta amince cire harajin kayan da su kai dalar Amurka 300. Matakin wanda zai fara aiki a ranar Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025, an cimma shi ne a taron hukumar na yau da kullum na karo na 63 da aka gudanar a ranar Talata 2 ga watan Satumba, 2025, wanda ministan Kuɗu kuma mai Kula da Harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun ya jagoranta. Hukumar ta ce, amincewar ta yi daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya waɗanda ke da nufin sauƙaƙe hanyoyin shigo da kayayyaki masu ƙarancin aima don habaka…
Read More
Za mu tabbatar ana amfani da bashin da gwamnati ke ci wajen gina ƙasa – Abbas

Za mu tabbatar ana amfani da bashin da gwamnati ke ci wajen gina ƙasa – Abbas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kakakin majalisar wakilan Najeriya Hon. Tajudeen Abbas ya ce idan aka yi amfani da basukan da gwamnati ke shi yadda ya kamata za su taimaka wajen bunƙasa ci gaban ƙasar. Cikin wata sanarwa da kakakin ya fitar bayan taron kwamitocin kuɗi na ƙungiyar Majalisun Dokokin Yammacin Afirka, Hon Tajudeen ya ce idan ba a yi amfani da basukan ta hanyar da ba ta dace ba za su iya jefa ƙasashen cikin matsin tattalin arziki. “Ya zuwa tsakiyar shekarar 2025, jimillar bashin da ake bin Nijeriya ya kai tiriliyan 149.39 (kimanin dalar Amurka biliyan 97) abin da…
Read More
Ba mu da shirin rufe sashen fetur – Matatar Dangote

Ba mu da shirin rufe sashen fetur – Matatar Dangote

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar man Dangote ta ƙaryata labarin shirin rufe sahen matatar man fetur na tsawon watanni biyu zuwa uku. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, za a iya rufe sashin mai a matatar Dangote na tsawon watanni biyu zuwa uku domin gyara. Kamfanin dillancin labaran na ƙasa da ƙasa ya nakalto daga shafin sa ido na kamfanin IIR Energy cewa zai yiwu a rufe sashen mai da ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowacce rana tun a ranar 29 ga watan Agusta bayan da aka samu tsaiko. Rahoton ya ƙara da cewa, matatar ta…
Read More
Dan sanda ya harbe faston da ya je wa’azi gidan gwamna

Dan sanda ya harbe faston da ya je wa’azi gidan gwamna

Wata uwa ta zargi jami’an ‘yan sanda da kashe ɗanta, Moses, bayan ya nemi ya yi wa gwamnan Kuros Ribas wa’azi. Ana zargin ɗan sanda ya hallaka matashin da ya je gidan gwamnan domin yi masa wa'azi da kira zuwa ga Ubangiji. Mahaifiyar matashin mai suna Moses Mba Onyekachi mai shekaru 23 ta buƙaci adalci game da lamarin. Ta ce, abin ya faru ne a Kalaba ranar 1 ga Agusta 2025, sun je jana’iza, sai suka samu kira da safe cewa a gaggauta zuwa asibitin sojojin ruwa saboda wata matsala. Bayan mijinta ya isa wurin, sai ya gano ɗansu aka…
Read More
Yadda ’yan bindiga ke karɓar haraji har N500,000 kafin a binne mamaci

Yadda ’yan bindiga ke karɓar haraji har N500,000 kafin a binne mamaci

Lamarin ’yan bindiga ya fara wuce gona da iri yayin da ake ƙorafin suna karɓar haraji kafin a birne mamaci. Wasu shugabannin al’umma a Lilu da Agwa da ke jihohin Anambra da Imo ne suka yi wannan ƙorafi. Shugabannin sun bayyana haka ne a yayin gabatar da rahoton 'Amnesty International' a kan kisan gilla a Kudu maso Gabas a Ikeja, Legas. Al'ummomin sun koka cewa ana tilasta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu biyan kuɗin harajin birne mamata ga yan bindiga. Sakataren fada na Lilu, Dr. Dominic Okoli, ya bayyana cewa tsakanin 2020 zuwa 2025, an kashe mutum 25…
Read More
Komawa makaranta: Mai girma gwamna ana cin amanarka…

Komawa makaranta: Mai girma gwamna ana cin amanarka…

Daga DR. MUSA TANKO HARUNA (MUSA MAZANKWARAI) Makarantu masu zaman kansu suna cin karensu babu Babbaka! La haula lana wala ƙuwwata illa billah! Muna roƙon Allah ya horewa iyaye abin hidimar iyali. Amma maganar gaskiya ba'a yiwa iyaye adalci. Akwai wani bincike dana gudanar akan abinda ya shafi yadda aka bar makarantu masu zaman kansu (Private schools) suke cin karensu babu babbaka. Tabbas a waccan shekarar data gabata mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tsawatar musu da duk iyayen da suka buƙaci a basu list din littattafai a basu, wanda yaga zai iya siya a makarantar kuma tom…
Read More
Dalili da kuma yadda aka kafa Izala

Dalili da kuma yadda aka kafa Izala

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Allah ya jiƙan Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi, saboda irin kyakkyawar niyyarsa wajen kafa Izala, domin farfaɗo da ilimin addinin Musulunci tsakanin al'ummar Musulmin Nijeriya. Kamar yadda marigayin a wata hira da ya yi, wacce ya nuna, tunanin kafa wata ƙungiya a Nijeriya wadda za ta yi wannan aiki ya samo asali a shekarar 1962 lokacin aikin hajji na wannan shekarar. Sheikh Gumi da Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, an ba su masauki a gidan saukar baƙi na Abdallah Khalid da ke Mina kusa da Jamra (wajen jifan shaiɗan). A wajen jifan shaiɗan ɗin, sai Gumi ya…
Read More
Ƙurajen fuska (pimples) da hanyoyin magance su

Ƙurajen fuska (pimples) da hanyoyin magance su

Tare da BILKISU YUSUF ALI  08054137080, [email protected] Gabatarwa: Kurajen fuskar da ake kira da ‘pimples’ a turance na ɗaya daga cikin matsalolin fata da suka fi addabar mutane a duniya, musamman matasa da matan da ke fuskantar sauyin jiki ko ‘hormones’. Wannan cuta tana faruwa ne sakamakon toshewar ‘pores’ na fata da mai da ƙwayoyin fata da suka mutu da kuma wasu ƙwayoyin cuta. Duk da cewa, ba cuta ce mai hatsari ba, amma tana iya haddasa raɗaɗi, kunya da damuwa, musamman idan ta yawaita ko ta bar tabo a fuska. A cewar Mayo Clinic, ƙurajen fuska na iya tasiri…
Read More
An yi zaman sulhu tsakanin ‘yan bindiga da al’ummar Faskari

An yi zaman sulhu tsakanin ‘yan bindiga da al’ummar Faskari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina sun tabbatar da cewa an ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin al’ummar yankin da wasu daga cikin ƴan bindiga da ke addabar yankin tsawon lokaci. Wannan yarjejeniya ta samu ne a yayin wani zama na musamman da ya gudanar, inda aka cimma matsaya cewa ƴan bindigar za su daina kai hare-hare ko cutar da al’umma, amma za su riƙa shigowa gari don gudanar da rayuwar yau da kullum cikin lumana. Wannan mataki ya zo ne bayan dogon lokaci na tashin hankali da kashe-kashe da garkuwa da mutane da aka…
Read More
AGILE ta wayar da kan wakilan kafafen yaɗa labarai kan ilimin mata a Zamfara

AGILE ta wayar da kan wakilan kafafen yaɗa labarai kan ilimin mata a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ma'aikatar ilimi ta jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar hukumar AGILE a yau Lahadi sun gudanar da taron wayar da kai ga kafafen yaɗa labarai da nufin inganta tsarin ilimin yara mata a jihar. A jawabin maraba shugabar shirin AGILE ta jihar Sa'adatu Abdu Gusau ta bayyana cewa taken shirin shine "ci gaban sadarwa ga matasa" Ta jaddada buƙatar ’yan jarida dake aiki a Jihar su ba da muhimmanci sosai kan ilimin yara mata a rahotonsu a jihar. Ta ci gaba da cewa, maƙasudin taron shine don ƙarfafa aikin yaɗa labarai kan hanyoyin sadarwa na…
Read More