03
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda a Katsina sun kama ƙarin mutum biyu a bincike da suke gudanarwa kan yadda ake karkatar da abincin RUTF da aka fi sani da 'yar ƙwamaso. 'Yar ƙwamaso abincin ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara biyar masu fama da rashin abincin gina jiki wanda gwamnnatin tarayya da hukumar UNICEF da sauraren ƙungiyoyin sa kai suka samar. A baya dai 'yan sanda sun kama Muhamud Aliyu ɗauke da buhu uku na 'yar ƙwamaso wanda bincike na farko wanda ake zargi ya ambaci sunan Zaharaddin Musa wani jami'in kiwon lafiya da 'yan sanda suke…
