04
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Arewacin Nijeriya ne zai fi amfana da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta kawo, musamman ta fuskar manyan ayyukan more rayuwa da bunƙasa damar kasuwanci da ƙasashen maƙwabta. Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnati damar karkatar da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tallafin zuwa wasu muhimman fannoni na ci gaban ƙasa. Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a wani taron tattaunawa kan manufofin gwamnati da APC Professionals Forum ta shirya a Abuja. Gwamnatin ta…
